'Yanwasan Super Eagles sun fara cika sansani don karawa da Rwanda

Asalin hoton, X/Super Eagles
'Yanwasan tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya sun fara cika sansaninsu da ke birnin Kigali na Rwanda domin cigaba da fafatawa a wasannin neman gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026.
Tun a ranar Talata 11 ga watan Maris mai horarwa Eric Chelle ya fitar da sunayen 'yanwasa 23 da za su buga wa taawagar wasannin na wannan karon.
Wasa biyu Najeriya za ta kara a wannan karon. Na farko shi ne na ranar Juma'a mai zuwa da Rwanda a birnin Kigali, sai kuma wanda za ta karɓi baƙuncin Zimbabwe kwana huɗu bayan haka.
A ranar Lahadi ne 'yanwasan suka fara isa sansani, cikinsu har da tauraron ɗanwasan gaba Victor Osimhen, wanda ya faɗa wa BBC cewa "sun zaƙu su kai Najeriya gasar" da za a yi a Amurka, da Mexico, da Canada.
Shi ma kociya Eric Chelle da sauran jami'an tawagar suna cikin matafiyan da suka isa, inda za su fara atasaye ranar Talata.
'Yanwasan da suka isa sansani zuwa yammacin Litinin su ne:
- Amas Obasogie
- Tolu Arokodare
- Kayode Bankole
- Victor Osimhen
- Simon Moses
- Bruno Onyemaechi
- Papa Daniel
Najeriya tana mataki na biyar da tazarar maki huɗu tsakaninta da Rwanda ta ɗaya.
Sabon koci Eric Chelle zai buƙaci kyakkyawan sakamako da gaggawa a matsayinsa na koci na uku da ya jagoranci Eagles ɗin a wasannin neman gurbin tun daga watan Nuwamban 2023.
Jose Peseiro ne ya fara buga canjaras biyu a wasan Lesotho da Zimbabwe, sai Finidi George ya yi rashin nasara a hannun Benin da kuma canjaras da Afirka ta Kudu.
Tuni koci Eric Chelle ya maye gurbin ɗanwasan tsakiyar Bayer Leverkusen, Nathan Tella wanda ya ji rauni, da Joshua Torunarigha na kulob ɗin Gent a Belgium.

Asalin hoton, Super Eagles











