Messi ba zai buga wa Argentina wasa da Brazil ba

Asalin hoton, Reuters
Ɗanwasan gaba na Inter Miami Lionel Messi ba shi cikin tawagar Argentina da za ta buga wasan neman gurbi a gasar Kofin Duniya da Brazil da kuma Uruguay.
Ɗanƙwallon mai shekara 37 ya koma buga wa ƙungiyar wasa da Atlanta a gasar Major League Soccer amma kuma sai ya ji rauni yayin wasan na ranar Lahadi.
Daga baya Miami ta tabbatar cewa Messi ya ji ƙaramin rauni tsokarsa.
Messi ya zauna a benci tsawon wasa uku na Miami kafin ya shigo a matsayin canji kuma ya zira ƙwallo a raga a wasan gasar Concacaf Champions Cup da suka buga a gidan Cavalier ta Jamaica.
Messi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa "abin baƙin ciki ne ya rasa buga waɗannan wasanni biyu na musamman".
"Na so na buga wasan kamar koyaushe amma kuma a ƙarshe wani ƙaramin rauni ya sa na tafi hutu kafin na dawo taka leda," in ji shi.
"Amma zan yi sowa da tafi daga nan kamar sauran magoya baya."
Argentina za ta iya samun gurbi tun daga wannan zagayen idan ta yi nasara kan Brazil da Uruguay.
Ita ce a saman teburin rukunin Kudancin Amurka mai tawaga 10 da tazarar maki biyar, sai Uruguay mai shida, da kuma Brazil ta biyar.
Shidan farko za su samu gurbi kaitsaye zuwa gasar ta 2026 da ƙasashen Amurka, da Mexico, da Canada za su karɓi baƙunci, inda na bakwai kuma zai buga wasan neman cike gurbi.
Bayan zagaye 12, Messi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye da guda shida, ya ci wa Argentina 112 kenan jimilla cikin wasa 191 da ya buga mata.
Paulo Dybala na Roma da Gonzalo Montiel na River Plate ma ba za su buga wasannin ba saboda rauni.
Shi ma Neymar ba zai buga wa Brazil wasannin ba sakamakon rauni a cinyarsa.











