Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta hana sayen kayan sadarwa na China saboda tsaro
Gwamnatin Amurka ta haramta sayar da sabbin na'urorin sadarwa daga wasu kamfanonin biyar na kasar Sin, sakamakon damuwa a kan harkokin tsaron kasar.
Wannan dai shi ne karon farko da mahukunta suka dauki irin wannan matakin kan dalilan tsaro.
Kuma ya biyo bayan takunkumin da aka sanya a baya ne wanda ya hana daya daga cikin kamfanonin da ake magana a kai - Huawei - samar da kayan aiki ga hukumomin tarayya a kan fargabar cewa za a iya amfani da su wajen leken asiri.
Wannan shi ne mataki na baya-bayan nan a cikin jerin matakan da aka tsara domin takaita damarmakin da kamfanonin sadarwa na kasar Sin ke samu a kasuwannin Amurka.
Wanda mataki ne da ya samo asali a karkashin gwamnatin Obama kuma ya kara habaka a lokacin shugabancin Donald Trump.
Bayan kamfanin Hauwaei matakin ya kuma shafi kamfanin ZTE daya daga cikin kamfanoni mafiya girma da ke samar da naurori na sadarwa.
Wannan mataki bai tsaya ga Amurka ba hatta mahukunta a Birtaniya da Tarayyar Turai da Kanada da kuma Australiya suma sun dauki matakin takaita sayen kayayyakin kamfanonin na China.
Sauran kuma kamfanonin da ke cikin jerin wadanda aka fitar na hada na'urar daukar hoto ta tsaro da kuma rediyon oba-oba.
Sai dai kasancewar matakin ba nan take zai fara aiki ba kamfanonin za su iya ci gaba da sayar da kayayakinsu da aka amince da su a baya a Amurka.
Ko-da-yake akwai yuwuwar cewa a soke wannan matakin nan gaba.
Kamfanin Huawei da sauran kamfanonin sun musanta zargin cewa suna samar wa gwamnatin China da bayanan sirri.