Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Amurka ke son ƙulla ƙawance da makwaftan China
Babu wani wuri da manufofin hulɗa da ƙasashen waje na shugaban China Xi Jinping suka fi tasiri kamar a ƙasashen kudu maso gabashin Asiya.
To amma yayin da manufofin China ke ƙara ƙarfi a ƙasashen duniya, lamarin na zamewa barazana ga Amurka, shi ya sa ma yanzu Amurka take sake yunƙurin janyo ƙasashen yankin a jiki.
Yayin da zai halarci taron ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asia na shekara-shekara a Cambodia, Biden zai zamo shugaban Amurka na farko da ya kai irin wannan ziyara tun daga shekarar 2017.
Daga nan sai ya tafi Indonesia, ɗaya daga cikin manyan ƙasashen yankin, inda ake sa ran zai gana da Shugaba Xi Jinping kafin su tafi taron manyan ƙasashe 20 na duniya.
To amma a wannan yanayi Biden na ƙoƙarin ƙetare iyaka ne ta diflomasiyya, fiye da yadda ya kasance a baya.
Kungiyar 'Asean', wadda ke da muhimmanci a harkar diflomasiyya a yankin Asia-Pacific, ta yi ta ƙoƙarin ganin ta nuna muhimmancinta a yanayin da duniya ta dare zuwa ɓangarori daban-daban.
Yankin na nuna kansa a matsayin wanda bai karkata ga kowane ɓangare ba kuma mai son zaman lafiya.
Ƙasashen yankin guda 10 kan zaɓi samun matsaya a ko da yaushe, da kauce wa sukar juna, kuma suna hulɗa da kowace ƙasa kai-tsaye.
Wannan ya taimaka, yayin da Amurka take mamaye harkoki na kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙin duniya.
Sai dai tasowar China a harkar kasuwanci na duniya a farkon shekarun 2000 ya yi daidai da lokacin da ƙasashe ke ƙoƙarin juya wa Amurka baya, yayin da take koƙarin mayar da hankali zuwa Gabas ta Tsakiya.
Daga nan sai China ta fara cusa kanta a ƙasashen yankin. Yayin da Mr Xi ke kwashe shekara 10 yana kan mulki, tasirin ƙarfin China a yankin ya fito ƙarara.
A cikin shekara 10 da suka gabata, matakin China na mamayewa da jibge dakarunta a wasu tsibirai da ke tekun kudancin Asia ya sanya an samu fito na fito tsakaninta da wasu ƙasashen da ke iƙirarin su ne ke da iko da tsibiran, musamman ƙasashen Vietnam da Philippines.
Duk wani yunƙuri da ƙasashen Asean suka yi na ganin an yi sulhu kan lamarin abin ya ci tura. China ta ƙi yarda a yi wata tattaunawa ta a-zo a-gani kan batun tsawon shekara 20.
Ta kuma yi watsi da wani hukuncin kotun duniya na shekara ta 2016 wanda ya haramta matakin na China.
To amma ƙasashen ƙungiyar Asean na cikin yanayi mai wahala, na farko dai China na da matuƙar ƙarfin tattalin arziƙi, da na soji, kuma ba kowace ƙasa ce za ta iya yin fito-na-fito da ita ba.
Ko a Vietnam, wadda ta taɓa gwabza yaƙi da China, shekaru 43 da suka gabata, wadda har yanzu ake da masu ƙin jinin China ɗin a cikinta, jam'iyyar da ke mulkin ƙasar na yin taka-tsan-tsan kan yadda take hulɗa da China.
Suna da kan iyaka mai tsawo da ta haɗa su, kuma China ce wadda Vietnam ta fi hulɗa da ita a fannin kasuwanci.
Na biyu, China ta raunana haɗin kan ƙasashen Asean ta hanyar ƙulla aminta da ƙananan ƙasashen yankin kamar Laos da Cambodia, waɗanda suke dogaro kacokan a kanta.
Duk da cewa ɗarɗar ɗin da ƙasashen ƙungiyar Asean ke yi da China tamkar abin farin ciki ne ga Amurka, to amma ƙasashen ba su kuma shiri da Amurkar.
Ba sa kallon ta a matsayin wadda za su iya bai wa amana. Suna mata kallon wadda ta fi lamurra suka yi wa yawa, kuma ta mayar da hankali kacokan a kan haƙƙin bil'adama da dimokraɗiyya.
Amurka ta tursasa wa yankin ya amince da wani tsarin tattalin arziƙi mai tsauri wanda mutane ba su yi maraba da shi ba, bayan matsalar tattalin arziƙi da yankin ya samu a shekarar 1997.
Ƙulla aminta da Amurka ta yi na ƙawancen ƙasashe huɗu tare da Japan, da Australia, da India shi ma ya ƙara raunana Asean, abinda ya sa ƙungiyar ta rasa tudun dafawa tsakanin manyan ɓangarori biyu.
Sannan kuma ƙudurin Amurka na ƙalubalantar China a yankin Asia na tsoratar da su, domin kuwa 'idan giwaye biyu na faɗa, ciyawa ce ke shan wahala.'
Amurka ba ta taɓa tunanin ƙulla alaƙar kasuwanci babu shinge da ƙasashen na Asean ba, waɗanda su ne suka fi kowane ɓangaren duniya dogaro da harkar cinikayya.
A ɓangare ɗaya kuma alaƙarsu da China ne ta ƙara ma yankin ƙarfi, inda ya zamo yankin kasuwanci mafi girma, wanda ya haɗe ƙasashen na Asean, da China, da Japan, da Koriya ta kudu, da kuma New Zealand.
Amurka za ta ji daɗin cewar ƙasashen Asean za su so ƙulla alaƙa da wasu ƙasashen, to amma dukkanin ƙasashen na Asean sun yi amannar cewa China ita ce za ta yi kaka-gida a yankin, kuma ba za ta lamunci duk wani abu da zai zamo barazana gare ta ba.
Babbar tambayar ga shugaba Biden ita ce: shin Amurka ta makara ne wajen sake salon halɗa da ƙasashen da ke maƙwaftaka da China?