Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta gano iyayenta na asali ta hanyar facebook
- Marubuci, Fay Nurse
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Sai da Tamuna Museridze ta ja numfashi, sannan ta latsa wayarta domin yin kiran wayar da ta daɗe tana fatan yi tun daga lokacin da ta gano cewa ita ƴar riƙo ce.
Ta kira matar da ta yi tunanin ita ce mahaifiyarta. Tana shakkun samun bayanin da take so, amma kuma ba ta yi tunanin zai zama abin faɗa ba.
"Sai ta fara ihu tana cewa ita ba ta haifa wani ba. Ba ta da wata alaƙa da ni," in ji Tamuna, a lokacin da take bayyana halin da ta shiga.
"Na shirya jin kowace irin amsa, amma amsar da ta ba ni ta yi muni matuƙa."
Amma duk da haka Tamuna ba ta cire tsammani ba. Tana so lallai sai ta gane yadda aka yi ta zama ƴar riƙo, sannan tana so aƙalla ta san sunan mahaifinta, wanda mahaifiyarta ce kaɗai za ta iya faɗa mata.
Tun a shekara 2016 ce Tamuna ta fara neman iyayenta, bayan wadda ta riƙe ta ta rasu. Wani lokaci tana kwalemar gidanta, sai ta ga takardar haihuwa da sunanta, amma ranar haihuwa daban, sai ta fara tunanin wataƙila riƙonta aka yi. Bayan ta fara bincike, sai ta buɗe wani zaure a Facebook mai suna Vedzeb wanda ke nufin ina nema, inda take fata zai taimaka mata wajen gano iyayenta.
Maimakon haka, sai ta gano wata baɗaƙalar safarar yara a Georgia, wadda ta shafi dubban ƙananan yara, inda aka ɗauki gomman shekaru ana yi wa iyaye ƙaryar cewa yaran da suka haifa sun mutu - alhali sayar da jariran ake yi.
Tamuna ƴarjarida ce, kuma ta taimaka wajen haɗa iyaye da dama da yaransu amma - idan ba yanzu ba - ta kasa share wa kanta hawaye na gano asalin iyayenta, inda har ta fara fargabar ko dai ita ma sace ta aka yi, aka sayar da ita.
Ta samu labari mai daɗi ne a wata bazara, lokacin da ta samu saƙo ta Facebook, daga wani wanda ya taɓa zama a Georgia, wanda ya faɗa mata cewa ya san wata mata da ta ɗauki ciki a Gerogia, amma ta ɓoye cikin, daga baya ta tafi Tbilisi ta haihu a watan Satumban 1984. Kuma a ɗan wanan tsakankanin ne aka haifa Tamuna.
Wanda ya turo mata saƙon yana tunanin wannan matar ce mahaifiyar Tamuna.
Tamuna sai ta fara neman matar a intanet, amma ba ta samu wani bayani ba. Sai ta buɗe gangamin nemanta a Facebook.
Sai wata ta amsa mata, ta ce wannan matar da ake magana ƴaruwarta ce. Sai ta ce Tamuna ta cire rubutun a Facebook, amma ta je ta yi gwajin DNA.
A daidai lokacin da suke jiran sakamakon gwajin DNA ɗin ne Tamuna ta yi waya da mahaifiyarta.
Bayan mako guda kuma, sai sakamakon gwajin ya fito, wanda ya nuna cewa lallai Tamuna da matar ƴanuwa. Sai Tamuna ta buƙaci mahaifiyarta ta bayyana mata sunan mahaifinta. Sai ta faɗa masa sunansa Gurgen Khorava.
"Na ɗauki watanni ina ta mamaki, kasancewar na fara cire tsammani. Yau ni ce na gano iyayena."
Sai Tamuna ta fara neman Gurgen a Facebook. Kwatsam sai ta gano ashe ya daɗe yana bibiyar harkokinta a Facebook - musamman ayyukanta na haɗa iyaye da ƴaƴan da aka sace a Georgia.
Sai Tamuna ta yi mamakin, "kasancewarsa cikin abokanta na Facebook na kusan shekara uku." shi ma bai san yaya suke ba.
"Shi bai ma san mahaifiyata ta ɗauki ciki ba. Shi kansa ya yi mamaki."
Sai suka shirya haɗuwa a gidansa da ke Zugdidi a kudancin Georgia - kimanin tafiyar mil 160 (kilomita 260) daga Tbilisi da take zaune.
Lokacin da mahaifinta mai shekara 72 ya fito, sai suka rungume juna, suka daɗe suna kallon juna suna murmushi.
"Yana kallona yana gane cewa ni ƴarsa ce," in ji ta.
Tana da tambayoyi da dama, amma ba ta san ta ina za ta fara ba. "Sai kawai muka zauna muna kallon juna, muna ƙoƙarin gano abubuwan da muke da su masu kama da juna," in ji ta.
Da suka cigaba da hira ne sai suka gane ashe akwai abubuwa da dama da ra'ayinsu ya zo ɗaya - Gurgen ya kasance ɗan rawa a Georgia, ita ma Tamuwa tana son raye-raye.
Sai Gurgen ya gayyaci iyalansa su gana da Tamuna, inda ta gana da ƴanuwanta masu yawa. "Daga cikin ƴaƴansa baki ɗaya, ni ce na fi kama da shi," in ji ta.
Sai suka wuni suna tattaunawa tare, suna cin abinci tare da yin waƙoƙin Gergia.
Sai dai duk da cewa Tamuna ta gano mahaifinta, tambayar da ke cigaba da faɗo mata ita ce, shin ita ma sace ta aka yi kamar sauran dubban yaran da aka sace aka sayar? ga shi kuma waɗanda suka riƙe ta sun rasu, ballanta ta tambaye su.
Sai ta samu damar tambayar mahaifiyarta a watan Oktoba. Wata tashar talabijin na ƙasar Poland ta shirya wani shiri na musamman a kan Tamuna, sai suka je wajen mahaifiyarta.
A nan ne ta gano cewa ita ba kamar sauran waɗanda ta taimaka wajen haɗa su da iyayensu ba, ita ba sace ta aka yi ba. Mahaifiyarta ce ta bayar da ita, sannan ta ɓoye maganar tsawon kusan shekara 40.
Mahaifiyarta da mahaifinta ba wai soyayya suka yi ba, haɗuwa suka yi da ƙanƙanin lokaci. Saboda takaici da kunya, sai ta ɓoye cikin. A watan Satumban 1984, sai ta tafi Tbilishi, inda ta faɗa wa mutane cewa za ta je a mata tiyata, inda a can ne ta haifa ƴarta. A can ta cigaba da zama har ta cimma yarjejeniyar riƙon Tamuna.
Ta ce mahaifiyarta ta buƙaci ta riƙa faɗa wa mutane cewa sace ta aka yi. "Ta faɗa min cewa idan ba zan ce sace ni aka yi ba, babu ita babu ni, amma sai na fada mata cewa ni ba zan iya yin wannan ƙaryar ba."
Tamuna ta ce idan ta yi ƙarya, ba ta kyauta wa sauran iyayen da aka sace musu yara ba, "saboda babu wanda zai ƙara yarda da su."
Sai mahaifiyarta ta kore ta daga gidan, kuma tun lokacin ba su sake magana ba.