Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ban taɓa jin zan bar Wolves ba - Cunha
Ɗan wasan Wolverhampton, Matheus Cunha ya ce bai taɓa tunanin barin ƙungiyar ba, koda a lokacin da aka yi cinikayyar ƴan wasa a watan Janairu.
Mai shekara 25 an yi ta alakanta shi da zai bar Molinuex a watan Janairun ya koma taka leda a Arsenal ko Tottenham ko kuma Manchester United.
To sai dai ya kwo karshen jita-jita, sakamakon da a watan nan ya sabunta ƙwantiraginsa a Wolves da cewar zai ci gaba da taka leda kaka huɗu da rabi.
Cunha ya ce Wolves ta buɗa masa hanya, bayan da ta ɗauke shi daga Atletico Madrid daga buga wasan aro, bayan da baya cikin ƴan wasan da Brazil ta gayyata gasar kofin duniya a 2022.
''Ba na tunanin barin Wolves gaskiya. Ina jin da wata rawar da ban taka ba. Koda yau she ina faɗa wannan ce ƙungiyar da ta bani damar da na yi fice.'' in ji Cunha.
Cunha ya kara da cewar ''Ban ji daɗi da Brazil ba ta gayyace ni ba gasar da aka yi a Qatar a 2022, na damu mataka, baka jin cewar bari kaje atisaye, baka jin son ka yi komai, sai tarin damuwa.''
Cunha shi ne kan gaba a yawan ci wa Wolves ƙwallaye a bana mai 11 a raga a wasa 23 a Premier League, wadda za ta fafata da Bournemouth ranar Asabar.