"Mun shiga tashin hankali a daren da aka ɗauke mana yara huɗu"

An ɗauke Fatima, yar shekara 11, daga gidansu da tsakiyar dare
Bayanan hoto, An ɗauke Fatima, yar shekara 11, daga gidansu da tsakiyar dare

Jim kaɗan bayan dare ya raba a ranar 6 ga watan Satumban 2022, Musah Mustafa ya fito daga cikin bukkarsa domin yin buƙata, inda daga nan ne ya hango wasu motoci guda huɗu sun tunkaro ƙauyensu.

Mogyigna karamin ƙauye ne da iyalai kaɗan da kuma mutum 24 ke rayuwa a cikinsa, ya zama tamkar ɗigo a tsakiyar babbar gona a arewacin Ghana.

Abin mamaki ne ganin motoci da rana a ƙauyen, ballantana a ce da daddare. Musah ya ɓoye a bayan wani itace inda yake kallon abin da ke faruwa.

Lokacin da ya ga ƴan bindigar da ke cikin motocin na shiga wasu gidaje guda biyu, sai ya kwarma ihu da nufin tayar da sauran ƴan ƙauyen da ke barci.

Sai dai kafin a kawo ɗauki, mutanen sun shiga cikin gidajen tare da fitar da yara huɗu da ƙarfin tuwo, ciki har da wata yarinya mai suna Fatima yar shekara 11 wadda suka ɗauka lokacin da take barci tare da kakanninta.

Kakar Fatima mai suna Sana, ta roki mutanen da su sake ta bayan da suka ɗora mata bindiga a kai. Ba ta san dalilin da ya sa aka ɗauki yaran ba. An kuma ɗauki ƴan uwan yaran guda biyu. Sana tana cikin fargabar cewa ba za ta sake ganin jikokinta ba.

Ga ƴan ƙauyen Mogyigna, sun ɗauka cewa garkuwa da mutane aka zo aka yi musu a garin, sai dai wannan ba garkuwa da mutane ba ce.

A hukumance, wani shiri ne na ceto mutane da ƴan sandan Ghana suka gudanar karkashin dokar yaki da masu safarar bil’adama.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An mayar da yaran zuwa wurin da za a ba su kyakkyawar kulawa.

Wata kungiyar bayar da agaji ce ta Amurka mai suna International Justice Mission ta shirya aikin ceton.

Kungiyar ta IJM wadda ke bayar da tallafin kuɗi da ya kai dala miliyan 100 a cikin shekaru biyu da suka wuce, ta kasance kungiya ta sahun gaba a duniya wajen yaki da masu safarar bil’adam.

A Amurka, IJM ta ce ta samu goyon bayan wasu coci-coci kusan 300, inda aka tara kuɗi da ya kai sama da dala 280,000 a shekarar da ta gabata domin tallafa wa ayyuka a Ghana.

Sai dai wani rahoto na sashen binciken kwa-kwaf na BBC Africa Eye ya gudanar, ya gano cewa IJM ta raba wasu yara da iyalansu a wurin da babu wani batu na safarar bil’adam.

Binciken ya gano cewa hanyar da aka bi wajen yin ceton, ya samo asali ne daga wata aƙida ta kungiyar ta IJM.

Africa Eye ya kuma gano batutuwa biyu na wani aikin ceto da aka yi, inda aka tursasa da firgita da kuma raba yara da ƴan uwansu waɗanda aka yi iƙirarin cewa safararsu aka yi. Ɗaya daga cikin irin wannan batutuwa shi ne na Fatima.

A Ghana, IJM ta mayar da hankali ne wajen ceto yaran da aka yi safararsu da mayar da su leburori a Tafkin Volta, ɗaya daga cikin tafkuna mafi girma da mutum ya haƙa a duniya.

Ana yawan ganin yara na aiki a bakin Tafkin Volta
Bayanan hoto, Ana yawan ganin yara na aiki a bakin Tafkin Volta

Akalla mutane 300,000 ne suka dogara da tafkin wajen samun abin yau da kullum, kuma yaransu na aikin kamun kifi a masana’antar kamun kifi a yankin.

Wasu mutane kuma na taimaka wa iyalansu da aikin da suke yi yayin da ake ɗaukar hayar wasu domin aiki da masu kwale-kwale inda ake biyan su ƙankanin kuɗi.

Babu wasu bayanai masu zaman kansu da yawa kan yadda matsalar safarar yara take a tafkin Volta. Wani bincike da kungiyar IJM ta yi a 2016, ya nuna cewa sama da rabin dukkan yara da ke aiki a tafkin, an taɓa safararsu.

A 2015, kungiyar ta fara ceto yaran da aka gano kan jiragen ruwa a tafkin, sai dai a 2018, ta koma kai samame da dare a teku a wuraren da aka yi hasashen ana ajiye yara idan dare ya yi.

Samamen da suka kai wancan dare a ƙauyen Mogyigna na cikin irin samame da suke kaiwa. An yi wa samamen laƙabi da Operation Hilltop.

Africa Eye ya fara binciken kungiyar IJM ne bayan da aka fara samun korafi kan ayyukansu a Ghana, inda suka gudanar da bincike ta karkashin ƙasa a kan wani jami’in kungiyar.

Bayan fara binciken, mun yi nasarar sa ido kan abin da ma’aikatan kungiyar ke faɗa wa juna a cikin wani dandalin sada zumunta na WhatsApp. Mun kuma samu wasu bayanai da suka shafi batun, inda muka gano yadda kungiyar ke tsarawa da aiwatarwa da kuma yin ayyukanta.

Shaidar ta nuna cewa yayin da IJM ke faɗa wa ƙawayenta da suka hada da ƴan sanda, wasu mutane na cewa yara guda huɗun da aka ceto garkuwa da su aka yi, can a cikin gida kuwa ta kammala wani shiri na daban.

Wani jami’in shari’a na IJM ya faɗa a cikin wani sako da ya aike wa mambobin kungiyar cewa sun kammala bincike cewa babu batun safara a yaran da suka kama waɗanda suka haɗa da Fatima da wasu yara biyu da aka ɗauka daga ƙauyen Mogyigna a cikin dare.

An ajiye Fatima tare da sauran yara uku a cikin wani sansani da kungiyar ta IJM ta samar waɗanda kuma aka raba da ƴan uwansu tsawon watanni huɗu da suka wuce, kafin binciken da Ghana ta gudanar ya karkare cewa ba safarar yaran aka yi ba kuma a mayar da su zuwa ga iyalansu.

.
Bayanan hoto, Ƙauyen Mogyigna na ɗauke da gidaje da kuma iyalai da ke rayuwa da ba su da yawa

A yanzu Fatima ta koma ƙauyensu, kuma tana karkashin kulawar kakanta Sana, yayin da mahaifin Mohammed ya yanke shawarar cewa yaron zai iya zama a wani wuri na daban, kamar yadda mahaifan sauran yara biyun suka yi.

Lokacin da Africa Eye ta ziyarci Mogyigna, watanni biyar bayan ceto su, mazauna ƙauyen sun faɗa mana cewa suna cikin farin ciki saboda komawar yaran, sai dai sun ce sun ce har yanzu tasirin samamen da aka kai na ci gaba da shafarsu.

Fatima ta ce tana jin tsoron cewa tawagar BBC ta zo ne ta sake tafiya da ita.

"Na shiga fargaba inda nan da nan kawai na fara kuka,” in ji Fatima yar shekara 11 lokacin da take magana kan samamen da kungiyar IJM ta kai. “ Na ɗauka sun tafi da mu domin kashe mu. Ba mu san inda za su tafi da mu ba.”

A lokacin da take cikin sansanin ta ɗauka cewa kakanninta da ƴan uwanta sun mutu”.

“A lokacin da ake tafi da ni, na yi kuka inda nake tuna ƴan uwana,” in ji Fatima.

An kama kawunta Nantogma Abukari da kuma Sayibu Alhassan lokacin samamen.

An zarge su da laifin safarar yara da kuma bautar da su, inda suka kashe dukkan abin da suke da shi domin zuwa kotu da kuma biyan beli. Kowace tafiya da suka yi zuwa kotu, suna kashe akalla cedi 1,500 na Ghana.

Da suke mayar da martani kan batun Fatima da BBC ta nemi ji daga gare su, kungiyar IJM ta bayyana karara cewa shirinta ya mayar da yaran guda huɗu da iyayensu zuwa tudun mun tsira.

.
Bayanan hoto, An ɗaure Mawusi Amlade bisa kuskure kan laifin safarar yara

Yayin binciken BBC Africa Eye kan samamen da kungiyar IJM ta kai, ta kuma gano wani shirin ceto da aka yi. Wani samame a 2019, ya tilastawa wani yaro rabuwa da ƴan uwansa, abin da ya janyo aka yanke wa mahaifiyar yarinyar Mawusi Amlade, ɗaurin shekara biyar a gidan yari da laifin safarar yara.

Ta ce abu mafi ciwo na zaman gidan yarin shi ne raba ta da ‘ya’yanta, inda ta ce ba ta san me ya faru da su ba bayan nan.

"Ban san inda aka kai ‘ya’yana ba, na yi ta tunani a kansu,” in ji Amlade a tattaunawarta da Africa Eye.

Shekaru biyu bayan nan, a wani sauyawar al’amura, kwatsam sai aka soke hukuncin da ya ɗaure Ms Amlade bayan shiga tsakani na wata kungiyar agaji ta Amurka mai suna Sudreau Global Justice Institute – da ke da alaƙa da IJM.

Kungiyar ta yi wani kamfe na tara kuɗi kafin a saki Ms Amlade da kuma kwatanta ta a matsayin uwa wadda aka ɗaure da ba ta aikata wani laifi ba.

Shekara huɗu bayan nan, har yanzu ba a haɗa Ms Amlade da yaranta ba.

A wata tattaunawa ta daban, wakilin BBC ya tambayi wani mai bincike na IJM kan me zai faru idan ma'aikata da aka tura suka kasa ɗaukar yaran. "Ba za mu ce ba mu samu yaro ko guda ɗaya ba, muna son samun ƙarin wasu," in ji wani ma'aikacin kungiyar ta IJM yayin mayar da martani ga BBC.

Dakta Sam Okyere, wani babban malami a Jami'ar Bristol wanda ya yi aiki a Tafkin Volta da kuma ke gudanar da bincike kan shirin ceto yara, ya bayyana a cikin sirri cewa ana nuna damuwa kan ayyukan kungiyar.

Ya faɗa wa BBC cewa IJM na biyan ma'aikatanta kuɗaɗe da yawa.

"Barazanar rasa wani babban muƙami ka sanya mutane yin duk abin da za su iya domin ɗaukar yaran," in ji Dakta Okyere.

.
Bayanan hoto, Garin su Fatima mai suna Mogyigna na a wani yanki ne mai nisan sa'o'i kaɗan daga babban garin yankin

Kungiyar IJM ta musanta zarge-zarge marasa kyau da ake yi kanta da kuma nuna damuwa kan irin ceto da take yi.

Ta fitar da wasu hotunan bidiyo na irin ayyukanta a Ghana. A cikin wani bidiyo, an nuna wani wuri mai sosa rai lokacin da aka sake haɗa wani yaro da kakansa bayan ceto shi daga tafkin.

Kamfanin da ya samar da bidiyon, ya ce ya tara wa IJM kuɗi da ya kai dala mikiyan 1.25.

Sai dai lokacin da Fatima, ta koma ƙauyensu babu irin wannan yanayin.

Kakan Fatima, wanda ya kalli yadda ƴan bindiga suka kutsa cikin gidansa tare da ɗaukar jikarsa, ya mutu lokacin da aka tafi da ita.

"Kakana mutumin kirki ne, ya kasance yana ba mu kyaututtuka," in ji Fatima.

"Lokacin da na dawo, ina ta kuka, tun da kakanmu ya tafi ya bar mu, a ina za mu sake ganinsa?"