Yadda mai buƙata ta musamman ke bai wa matasa shawara kan rayuwa

Chris
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
  • Lokacin karatu: Minti 6

Haɗa takalmi wata sana'a ce da ake koya domin dogaro da kai da ɗaukar ɗawainiyar wasu ta hanyar tsarawa da haɗa ƙayatattun takalma a cikin gida da ake kasuwancinsu domin samun kuɗin shiga.

Amma shi a wajen Chris, wanda ake kira da Sir Chris, sana'ar ba tsaya a hanyar samun abinci kaɗai ba, a wajensa, sana'a ce da za a yi amfani da ita domin haɗin kai tsakanin musulmi da kirista da ƙaunar juna.

A Kaduna - jihar da ta daɗe tana fama da rikice-rikicen kaɓilanci da suke riƙewa zuwa na addini - an wayi gari da samun wani matashi mai suna Chris, wanda ɗan ƙabilar Urhobo a jihar Delta ta yankin Niger Delta.

Matashin wanda kuma Kirista ne yana yunƙurin kawo sauyi wajen samar da haɗin kai da ƙaunar juna tare da watsi da yaƙi da wariya ga nakasassu ta hanyar amfani da haɗa takalma.

Shagonsa ya zama wata matattara matasan Hausawa da suke koyon sana'a cikin wasa da dariya, inda suke koyon sana'a da kuma koyon muhimmancin ƙaunar juna ba tare da bambancin addini ba ƙabila ba.

Asalin sunansa Christopher Difference, amma an fi saninsa da Sir Chris, amma daga baya wasu suka koma kiransa "United", sunan da ya ce har yanzu bai san me ya sa aka laƙana masa ba.

Daga shiga shagon, za ka ci karo da matasa - yawanci Hausawa - kowa na ta aiki. Daga masu yanka fatar haɗa takalma sai masu ɗinki da masu buga ƙusa da masu shafa gam.

A can gefe kuma gwanin sha'awa ga oga Chris a keken guragu yane aiki, sannan yana bayar da umarnin wasu aikace-aikace cikin wasa da dariya. Sannan kuma ga sauti na tashi kamar yadda Hausawa suke cewa taɓa kiɗi taɓa karatu.

'Ba mu san bambancin addini ba'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da yadda Chris ya taso da kuma yadda yake rayuwa cikin matasan Hausawa musulmi, ya ce duk da cewa shi ɗan kudancin Najeriya ne, a yankin arewacin ƙasar aka haife shi.

"Nima Bahaushe yanzu," in ji Chris cikin murmushi a lokacin da yake ganawa da BBC Hausa.

Ya ce a lokacin da yake tasowa a Zaria da ke jihar Kaduna, "mun kasance muna rayuwa ne kirista da musulmi ba tare da bambancin addini ko ƙabilanci ba. Babu wancan ɗan'uwana ne, wancan ba ɗan'uwana ba ne. Don haka a irin rayuwar da na taso a ciki ke nan."

Ya ce wannan ya sa shi har yanzu yake cigaba da rayuwansa a haka. "Inda nake cin abinci gidan Musulmi ne.

To faɗa min, saboda ni ba Musulmi ba ne, sai in ce ba zan taimaka wanda ba Musulmi ba? ai hakan ba daidai ba ne. Tsarin rayuwata babu bambanci irin wannan.

Tsarin rayuwata shi ne inda nake zama ne ya fi kamata su fara cin moriyata. Wannan ya sa nake ƙoƙarin jawo su jikina ina taimaka musu. Bayan haka ma ai dukkanmu kakanmu ɗaya ne wato Annabi Adamu."

Ya ƙara da cewa bambancin addini ba shi da amfani, inda ya ce kowa ya yi addininsa kawai.

"Ba wanda zai taɓa maka addini, kai ma kar ka taɓa ma wani addini. Idan muka yi haka za mu zauna lafiya," in ji shi, inda ya ƙara da cewa "Dukkanmu muna rayuwa ne a ƙarƙashin Allah ɗaya. Don haka dole mu yi haƙuri mu cire bambancin addini da ƙabilanci da duk wani abu da zai hana mu ci gaba."

Chris ya ce bambancin addini ne ke jawo rikice-rikice, wanda a cewarsa ke jawo kashe-kashe.

"Wannan ya sa muke ƙoƙarin jawo matasa muna koya musu sana'a domin idan sun zo aiki, har suka kai yamma, da sun koma gida ai sun gaji. Ba za su yi tunanin rikici ba."

Shi ma wani matashi mai suna Ibrahim, wanda yake koyon sana'a a wajen Chris mai suna Ibrahim ya ce shi dai sai sambarka.

"Babu wani bambancin addini a shagonmu," in ji Ibrahim, wanda ya koya aikin takalma a wajen Chris.

Ya ce wasu lokutan Chris ne yake cewa su tafi masallaci idan lokaci ya yi, sannan yana ƙara ƙarfafa musu gwiwar girmama iyayensu.

"Ai ba dole sai wajen wanda addininku ɗaya ba ne za ka koya sana'a. Wani lokacin ma wanda ba addininku ɗaya ba sai ya koya maka aikin ya kuma riƙe ka sama da wanda addininku ɗaya," in ji shi.

'Abokai suka hana ni komawa kudu'

Yaran Chris

Chris ya ce ya taɓa fara yunƙurin tattara i-nasa-i-nasa ya koma kudancin Najeriya, amma a cewarsa, saboda jin daɗin zama, musulmin yankin suka ce ba za su bari ba.

Ya ce "shekara 7 da suka gabata na samu wani na faɗa masa cewa 'idan Allah Ya ba ni dama na samu wasu kuɗaɗe kamar naira miliyan 3, zan bar Arewa in koma Kudanci. Kawai sai ya ce to da yardar Allah ba zan samu kuɗin ba, idan har kuɗin zai sa in koma kudu.

A game da yadda musulman yankin suka ƙarbe shi, ya ce babu wata matsala da su. "Maganar gaskiya babu abin da zan ce wa ƴan unguwar da nake sai godiya. Ni dai ban sani ko a bayana ana yi, amma a gabana ban taɓa ji wani ya min ba daidai ba. Idan ma wani ya nuna min yatsa, to ina tabbatar ma za a karya yatsar saboda ina da kariya sosai," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa har alfarma yake nema ma wasu a unguwar.

Burin Chris na gaba

Chris, wanda zuwa yanzu ya koyar da matasa da dama da ya ce ba zai iya ƙididdigewa ba, ya ce yana da buruku da yake son cimmawa a nan gaba idan ya samu dama.

Ya ce ko yanzu ya samu nasara, domin a cewarsa a duk unguwar da yake zaune ta Hayin Banki, duk idan ka ga mai sana'ar haɗa takalmi, "har ya buɗe shago idan bai zama ni na koya masa ba, to zai zama jikana ne.

Shi ya sa zai yi wahala a iya ƙirga su. Amma wanda na san cewa wannan ni na ba su satifiket da hannuna, sun haura 25, sannan akwai waɗanda suka koya, suka tafi, kuma yanzu haka akwai aƙalla yara 18, ciki har da mai buƙata ta musamman."

Ya ce yana amfani da sana'ar wajen kawar da hankalin matasa daga ayyukan ɓata gari da shaye-shaye.

"Ina jin daɗin taɓa rayuwar mutane. Ba wai mutanen unguwar Hayin Banki kaɗai nake taimako ba, ba kuma jihar Kaduna ba ce kawai, Najeriya ce baki ɗaya."

Sai dai ya ce ba gina gidaje manya da hawa motoci ba ne a riba a wajensa, "kullum tunanina shi ne abin da za a riƙa tunawa da ni. Kuma ina tunanin ina da lada a wannan aikin. Ka ga ke nan ina da riba daga duniya har lahira."

Sai dai ya ce akwai abin da yake so idan ya samu dama zai yi, "ka san ɗan'adam yana mutuwa ne da buri.

Kun ga inda shagon yake babu kaya sosai, kuma yanayin da Najeriya ke ciki ya sa jarina ya yi ƙasa sosai. Idan Allah ya taimake mu, a nan gaba burina shi ne in samu jari da kayan aiki domin in faɗaɗa wajen aikin ya zama kamfani babba."

Ya ce idan ya faɗaɗa wajen yaran da ya koyar ba na sai sun je wani wuri sun yi aiki ba.

"A nan za mu yi creating din karamin kamfani wanda duk wata, burina in ga cewa duk wata ina biyan ma'aikatana albashi. Yanzu ba mu kai matakin ba, saboda koyarwa kawai muke yi, wanda aka koyar aka ba shi satifiket sai ka ga ya tafi saboda ba mu kai matakin riƙe su ba. Amma ina tabbatar maka cewa idan na samu jari da kayan aiki, za mu riƙa takalman da za a riƙa fitarwa zuwa ƙasashen waje."

Imani da ƙaddara

A game da yadda ya samu nakasa, Chris ya ce tun yana ƙarami ne ya kamu da wani irin zazzaɓi da ya yi sanadin mayar da shi haka.

Ya ce a haka ya cigaba da zuwa makaranta, amma bayan sakandare ya je makarantar koyon sana'a, inda ya zaɓi koyon haɗa takalma.

"Ba a haka aka haife ni ba. Ina da shekara 6 zuwa 7 Allah ya yi aikinsa na tsinci kaina a haka kuma ba mu taɓa cewa me ya sa ya faru ba don Allah ya san daidai kuma ina godiya ga Allah. Duk da yake akwai nakasan, ni ba na ganin nakasana, saboda alamu zai nuna muku cewa lalle ni ba zan ga nakasa ba, da kuka zo ai kun ga irin mutanen da suke kewaye da ni, ba masu nakasa ba ne."

"Makaranta ce ta masu buƙata ta musamman da ke garin Kakuri a jihar Kaduna. A makarantar na samu horo na shekara 3. So bayan nan kuma da yake Allah Ya sa dai muna da mutane, sai na ƙara haɗuwa da wani abokina, na koma wajensa na sake yin wata shida na ƙara ƙwarewa. Kafin daga bisani ya buɗe nawa."