Muna ganin kuraye na farautar namanmu lokacin da muke hannun 'yanbindiga - Janar Tsiga

Asalin hoton, Channels TV
Tsohon shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima a Najeriya, Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya bayyana irin taskun da suka shiga a hannun masu garkuwa da suka kama shi, inda suka dinga ganin kuraye na farauta a kusa da su.
A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto janar ɗin mai shekara 72 bayan kwana 56 a hannun 'yanbindigar da suka sace shi a garinsu na Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina a raewacin Najeriya ranar 5 ga watan Fabrairu.
Bayan ceto shi ne kuma aka miƙa su ga ofishin Nuhu Ribadu - mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja - tare da wasu mutum 18.
Da yake magana bayan isarsu ofishin Nuhu Ribadu a ranar Alhamis, tsohon janar ɗin ya bayyana irin wahalhalun da suka sha, ciki har da yadda namun daji ke yawo a kusa da su.
"Kwana ɗaya kafin na baro wurin, muna zaune a kan dutsen da aka ajiye mu kwatsam sai muka ga kura tana kewayawa don neman abinci. Wane abinci take nema idan ba mu mutane ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa sun sha ganin macizai da kunamu a lokacin da suke hannun 'yanbindigar.
Kazalika ya bayyana abin da ya kira "amfani da su a matsayin garkuwa" da ɓarayin dajin ke yi duk lokacin da sojoji suka kai musu hari ta sama.
"Duk lokacin da aka kai musu hari, sai su fito da mu waje saboda jirgin ya hare mu. Amma kun san Allah mai rahama ne. NSA ya faɗa, CDS ma ya faɗa - mutanen kirki ba za su ƙare ba."
Haka nan, ya bayar da labarin wani hari da aka kai musu kai-tsaye amma kuma makamin ya gaza fashewa.
"Suka kawo makamin rokar inda nake kwanciya suka ɓoye shi ta yadda da zarar na taɓa shi zai tashi da ni. Amma kuma mai jin ƙai ne."
A cewarsa, masu garkuwar na tunanin cewa kodayaushe jami'an gwamnati na ɗauke da kuɗaɗe, "abin da ya sa kenan suka haura gidana tare da saka abubuwan fashewa".
'Tsoron jirgi sama da tsoron Allah'
Da yake ci gaba da bayyana abubuwan da suka gani, Janar Tsiga ya ce ɓarayin da ke karakaina a dazuka sun fi jin tsoron jirgin saman sojin Najeriya sama da komai.
"Ba su tsoron Allah. Za su ce maka kada ka kira musu Allah, kawai ka ba su kuɗi. Amma da zarar sun ga jirgin sama sai su fara gudu har da shanunsu," kamar yadda ya bayyana.
Baya ga duka da suka dinga sha a kullum, ya ce sau ɗaya ake ba su abinci.
"Ina da hawan jini, su kuma gishiri kawai suke amfani da shi. Kowa ya san cewa akwai abincin da mai ciwon hawan jini ba zai ci ba. Yanzu kalli jikina, ko matattakalar nan ba zan iya hawa saboda gishiri da kuma dukan da suke yi mana kullum."
A cewarsa, tuwon dawa kawai ake ba su a matsayin abinci.











