Yadda harin 'yan bindiga ya haifar da fargaba a Filato

Asalin hoton, @CalebMutfwang
A Najeriya, rahotanni na cewar, ana ci gaba da zaman dar-dar a wasu garuruwa biyar na yankin karamar hukumar 'Bokkos ta jihar Filato, sakamakon wasu hare-hare da 'yan bindiga suke kai wa yankin.
Hakan dai ya yi sanadin asarar rayuka fiye da talatin, wasu da dama kuma suka sami munanan raunuka a 'yan kwanakin nan.
Yanzu haka kuma ana can ana neman wasda ake kai wadannan hare-hare.
Sai dai alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da hare-haren da ke aukuwa a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato, sakamakon yadda wannan matsala ta sake kunno kai a 'yan kwanakin nan.
Barista Farmasum Fuddang, shugaban kungiyar raya yankin na 'Bokkos, ya shaidawa BBC cewar lamarin ya kai ga fara ta'adi.
"Jiya aka yi jana'izar mutane, wadan da suka mutu, sun kai mutum 30, sai wadan da ke karbar magani da wadan da aka kwantar a asibiti, ammam suna da yawa. Akwai karin wasu mutanen da har yanzu baa san inda suke ba," In ji Barista Farmasum Fuddang
Haka kuma Barista Farmasum Fuddang ya ce 'wasu mutanen ne suka zo da rana suka zo suka ringa harbi kan mutane, fuskokinsu a bude, don fulani ne, ammam ba fulani makiyaya ba ne, a'a fulani yan ta'adda don dauke suke da muggan makamai, sai dai bamu san daga inda suka zo ba, amma ba fulanin da muke tare da su ba ne', in ji shi.
Ba wai iya kungiyar al'ummar Bokkos ne kadai ke wannan koke ba, itama ta makiyaya ta Mi Yetti Allah ta koka, kan ire-iren wadannan hare-hare da ta ce yak an shafe su. Alhaji Ibrahim Yusuf Babayo, shi ne shugaban reshen kungiyar na jihar ta Filato.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Kamar yadda suke fada wasu yan ta'adda ne ke kawo wannan hari, su ma fulani ana kashe su da dabbibinsu', in ji Alhaji Ibrahim Yusuf Babayo.
Sannan Alhaji Ibrahim Yusuf Babayo din ya ce 'saboda kaucewa chakuduwa da bata gari yasa muka yi wa mutanemu gargadi, su kaucewa tashin hankali, tare da kiyaye dokokin gwamanti, ba ma barin mutanen mu su hadu da bata gari ba, wajen hada kai da su don tada hankali ba,' a cewar sa.
Haka kuma ya yi kira ga gwamantin jihar ta Fulato da ta dauki matakai, na ganin an kamo wadn ke aikata wannan balahira tare da hukuntansu
A yanzu dai baki ya zo daya, tsakanin bangaren shugabannin al'ummar yankin Bokkos da na Fulani makiyaya, cewa ya kamata a yi kokarin gano bakin zaren, dangane da hare-haren da ke aukuwa a yankin, don a kawo karshen matsalar.
Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da ƙabilanci da kuma addini, amma a baya-bayan nan 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa sun ta'azzara matsalar.










