Najeriya ta kai ƙarar DR Congo kan 'amfani da ɗan wasan da bai dace ba'

    • Marubuci, Emmanuel Akindubuwa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Najeriya na fatan cewa damarta ta zuwa gasar Kofin Duniya a baɗi na nan, bayan gabatar da ƙorafi da ta yi wanda ke zargin cewa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta saka ƴan wasan da ba su cancanta ba a ƙarawa da suka yi a wasan ƙarshe na ƙasashen Afirka masu neman gurbin zuwa kofin duniya na 2026 a watan da ya gabata.

Kongo ta doke Najeriya a bugun fenariti don samun damar zuwa wasan gurbi na ƙasashe daga nahiyoyi da za a yi a watan Maris na shekara mai zuwa, wanda zai bai wa ƙasa damar zuwa gasar da za a yi a ƙasashen Canada, Mexico da kuma Amurka.

Sai dai iƙirarin Najeriya na cewa Kongo ta yi "coge" ya ta'allaka ne kan cewa ɗan wasan da ta saka bai daɗe da sauya ƙasar da yake buga wa wasa ba.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta yi imanin cewa ƴan wasa irin su Aaron Wan-Bissaka da Axel Tuanzebe, waɗanda dukkansu suka buga wasan da aka yi a Moroko, ba su cancani bugawa ba saboda dokokin ƙasar Kongo ba su bai wa mutum damar zama ɗan ƙasa biyu ba.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Kongo (Fecofa) ta yi watsi da iƙirarin NFF.

"Matsayar mu ita ce cewa an yaudari Fifa wajen tantance ƴan wasan," in ji sakataren hukumar, Mohammed Sanusi.

"Dokar Kongo ta ce ba za ka iya mallakar damar zama ɗan ƙasashe biyu ba, amma wasu ƴan wasansu na da fasfo ɗin Turai da kuma na Faransa.

"Akwai abin da muke kira karya dokoki Fifa. Abin da suka yi saɓa wa doka ne."

NFF ta ƙara da cewa ta gabatar da takardu da kuma hujjoji kan ƙorafin da take yi ga hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.

BBC ta tuntuɓi Fifa don ji daga gare ta, kuma tana jiran martani.

Sai dai, Fecofa ta kwatanta ƙorafin NFF a matsayin ƙoƙarin samun nasara "ta wata hanya".

"Ya kamata a buga gasar Kofin Duniya cikin gaskiya da jajircewa. Ba ta ɓarauniyar hanya ba," a cewar wani sako na shafin sada zumunta da tawagar kwallon kafar ƙasar Kongo ta wallafa.

Sakon ya kuma kwatanta Najeriya a matsayin "masu rashin nasara" da kuma watsi da ƙorafin har ma da cewa wannan ba halin dattaku ba ne.

Me zai faru?

Dokokin Fifa sun bayyana sharuɗɗa da ɗan wasa zai bi don sauya ƙasar da zai buga wa kwallo.

Karkashin waɗannan dokoki, ɗan wasa na iya neman buƙatar sauya ƙasar da zai iya buga wa kwallo sau ɗaya kacal, kuma lamarin na buƙatar yin rubutu wanda kwamitin Fifa mai kula da ƴan wasa ke da alhakin amincewa.

Yayin da Fifa ke son ɗan wasa ya riƙe fasfo ɗin sabuwar ƙasar da yake son wakilta, suna kuma da damar riƙe wani ƙarin fasfo.

Amma ba haka batun yake ba a dokokin Kongo.

Idan ƙorafi ya kai ga Fifa, akwai abubuwa da dama da za su iya faruwa:

  • Kora: Fifa za ta iya ɗaukar ƙorafin NFF da cewa ba shi da isassun hujjoji don haka ta yi watsi da ƙarar, inda hakan ba zai shafi Kongo ba a hanƙoronta na kai wa gasar Kofin Duniya.
  • Bincike da kuma saka takunkumi: Fifa za ta iya yin bincike, idan ta samu an tafka ba daidai ba lokacin tantancewa za ta saka wa ƙasar takunkumi (Alal misali cin tara, da kuma gargaɗi) amma ba za ta sauya sakamakon wasa ba.
  • Takunkumi a ɓangaren wasanni: A hukunci mai tsanani da za ta iya yankewa, Fifa ko kuma hukumar kula da kwallon kafa a Afirka za ta bayar da umarnin ƙwace maki ko bai wa ɗaya ƙasar nasara, ko kuma rage maki idan ana gurbin wasan rukuni.

A wani misali a baya-bayan nan, Fifa ta rage wa Equatorial Guinea maki shida lokacin wasannin rukuni na neman gurbin zuwa gasar kofin duniya na 2026 bayan da aka samu cewa kyaftin ɗin tawagar ƙasar Emilio Nsue bai cancanci buga wasa ba saboda buga wa tawagar matasan Sifaniya wasanni a baya.

Yayin da aka soke matakin daga baya, ba a mayar wa ƙasar makinta ba.

Afirka ta Kudu ma an kwace nasarar da ta yi kan Lesotho a wasannin neman gurbin zuwa kofin duniya na 2026, inda aka bai wa abokan adawarsu nasara da ci 3-0, saboda saka ɗan wasan da bai cancanta ba.