Muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Gasar Kofin Afirka

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Lahadi 21 ga watan Disamba ne za a fara fafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta 2025, wadda ita ce ta 35 da aka buga a tarihin gasar, kuma ita ce babbar gasar tamaula a Afirka.

A wannan lokacin hankulan masu bibiyar tamaula zai koma kan ƙasar Morocco da take Arewacin Afirka, wadda take cikin haɗakar kasashen da za su karbi bakunci. gasar kofin duniya a 2030.

Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 na tattare da ƙalubale, fiye da waɗanda aka yi daga shekara 10 zuwa 15 baya, inda tawaga 24 za ta kece-raini a filayen wasa tara cikin biranen ƙasar shida.

A baya ana buga gasar tsakanin Yuni zuwa Yuli, amma a gasar bana za a yi ne cikin watan Disamba, saboda wasannin gasar kofin duniya da za a yi a 2026 daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.

An tsara cewa za a yi gasar ne daga Disamban 2025 zuwa Janairun 2026.

Kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Sai dai akwai wasu muhimman bayanai da suka kamata a sani game da gasar, waɗanda BBC ta tattaro.

Ƙasar da ta fi lashe gasar

Ƙasar da ta fi lashe gasar a tarihi ita ce ƙasar Masar, wadda ta lashe gasar sau bakwai.

Masar ta lashe gasar ne a shekarun 1957 da 1959 da 1986 da 1998 da 2006 da 2008 da 2010.

Haka kuma ta zo a ta biyu sau uku a shekarun 19621 da 2017 da kuma 2021, sai ta zo ta uku a shekarun 1963 da 1971 da 1974, sannan ta zo ta huɗu sau uku shi ma a shekarun 1976 da 1980 da 1984.

Jimillar nasarori

Ƙasar da ta fi tarin nasarori, wato yawan zinare da azurfa da tagulla idan aka hada baki daya, wato ƙasar da ta fi zuwa wasannin na ƙarshe ko kusa da ƙarshe ita ce ƙasar Najeriya, inda jimilla ta samu nasarar lashe ko dai kofin ko ta zo ta biyu ko ta uku sau 16.

Ta lashe gasar sau uku a shekarun 1980 da 1994 da 2013, sannan ta zo ta biyu sau biyar a shekarun 1984 da 1988 da 1990 da 2000 da 2023, sai kuma ta zo ta uku sau takwas a shekarun 1976 da 1978 da 1992 da 2002 da 2004 da 2006 da 2010 da kuma shekarar 2019.

Ƙasar da ta fi cin wasanni

A ɓangaren wasanni da tara maki, ƙasar Masar ce kan gaba, inda ta halarci gasar sau 26, sannan a ciki ta buga wasa 111.

A cikin wasannin, ta samu nasara a guda 60, ta yi canjaras sau 24, sannan aka doke ta a wasa guda 27.

Idan aka yi amfani da tsarin maki, wato maki uku a nasara, da maki ɗaya a canjaras sai rashin maki a rashin nasara, ƙasar Masar tana da jimillar maki 204.

Ƙasar da ke biye mata ita Najeriya, wadda ta je gasar sau 20, inda ta buga wasa 104, ta samu nasara a wasa 57, ta yi canjaras a wasa guda 24, sannan aka doke ta a wasa 23, inda jimilla ta tara maki 195.

Lashe gasar a jere

Haka kuma a ɓangaren tarihin lashe gasar a jere, ƙasar Masar ɗin ce dai ta fi samun nasara.

Masar ta lashe gasar sau uku a jere a shekarar 2006 da 2008 da 2010.

Lashe gasar a zuwa na farko

Ƙasashe guda uku ne suka samu nasarar lashe gasar a karon farko da suka fara zuwa gasar:

Masar ta lashe gasar a shekarar 1957 da ta fara buga gasar, sai Ghana da ta lashe gasar a shekarar 1963 da ta fara buga gasar, sai kuma ƙasar Afirka ta Kudu da ta lashe gasar a shekarar 1996 da ta fara buga gasar.

Zura ƙwallaye

Ɗan wasan ƙasar Kamaru Samuel Eto'o ne ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar, inda ya zura ƙwallo 18 a wasa 29 da ya buga a gasar guda shida da ya buga.

Ya halarci gasar a shekarun 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010.

Wanda ke biye masa shi ne Laurent Pokou na ƙasar Ivory Coast, wanda ya ci ƙwallo 14 a wasa 12 da ya buga a gasar. Sai kuma ɗan ƙwallon Najeriya Rashidi Yekini wanda ya zura ƙwallo 13 a wasa 20.

Ƙwallon farko a gasar

Wanda ya fara cin ƙwallo a gasar shi ne ɗan wasan ƙasar Masar, Raafat Attia, wanda ya fara zura ƙwallo a gasar ta farko.

A wasan farko na gasar ta farko, wanda aka buga a ranar 10 ga watan Fabrailun shekarar 1957 wanda aka fafata tsakanin Masar da Sudan, shi ne ya zura ƙwallo ta farko a wasan wanda Masar ta samu nasara da ci biyu da ɗaya.

Yawan buga wasa

Ƴanwasan da suka fi taka wasanni a gasar su ne Rigobert Song na ƙasar Kamaru, wanda ya wakilci ƙasar tsakanin shekarar 1998 zuwa shekarar 2010, da kuma André Ayew na ƙasar Ghana wanda ya wakilci ƙasar tsakanin shekarar 2008 zuwa shekarar 2023.

Kowannensu ya buga wasa 36 ne a gasar.