Afcon 2025: Super Eagles tana rukuni da Tunisia da Uganda da Tanzania

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Afirka, Caf ta sanar da raba jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a gudanar a bana a Morocco.

A bikin da ta gudanr a Mohammed V National Theatre a birnin Rabat ranar Litinin ya ƙunshi tawaga 12 da aka raba su rukuni shida ɗauke da hurhuɗu kowanne.

Tun a cikin rukunin da akwai wasannin da za suyi zafi kuma na hamayya da suka haɗa a fafatawa tsakanin Moroccco da Mali da na Najeriya da Tunisia.

Sauran sun haɗa da karawa tsakanin Senegal da Jamhuriyar Congo da na Algeria da Burkina Faso da na Cote d'Iovire da Kamaru.

Za a fara da buɗe labulen babbar gasar tamaula ta Afirka a 2025 da wasa tsakanin mai masaukin baƙi, Morocco da Comoros.

Za a fara gasar cin kofin Afirka daga ranar 21 ga watan Disambar 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.

Yadda aka raba jadawalin Afcon 2025:

Rukunin farko: Morocco, Mali, Zambia, Comoros

Rukuni na biyu: Egypt, South Africa, Angola, Zimbabwe

Rukuni na uku: Nigeria, Tunisia, Uganda, Tanzania

Rukuni na huɗu: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana

Rukuni na biyar: Algeria, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan

RRukuni na shida: Cote d'Ivoire, Cameroon, Gabon, Mozambique