Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dokar Kare sirrin bayanai ta BBC
Amincewar da kuka yi mana na da matukar muhimmancin a wurinmu. BBC ta kudirin aniyyar kare dukkan bayanan da suka shafe ku, a duk lokacin da kuke hulda da wasu abubuwa na BBC.
Yana da matukar muhimmanci ku karanta wadannan bayanai domin sanin yadda za mu yi mu'amula da bayananku.
Wannan dokar ta kare sirrin bayanan na bayyana yadda za mu karbi bayananku da kuma yadda za mu yi amfani da bayanan a lokaci da kuma bayan huldarmu da ku, bisa doron dokar kare bayanan sirri.
Abin da ya sa muke karɓar bayananki da kuma yadda za ku shiga gasar
Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru, don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa. Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
BBC za ta karɓi bayananku ta hanyar intanet ko kuma imel, ya danganta da yadda ku ka aike da bayanan naku.
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa.
Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne, bisa jagorancin ma'aikacin BBC za ta zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su zaɓi ta biyu da ta uku.
Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu ko wane irin bayani kan masu shiga gasar ba.
Waɗanda su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (naira miliyan daya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu dari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu dari biyar) ga wadda ta zo ta uku. Idan haɗaka ce to za a raba kyautar kuɗin tsakaninki da ƴr uwar haɗakarki.
BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.
Duka labaran da aka naɗa za su ƙunshi sunan labarin da sunan marubuciyar. Ma'aikatan BBC Hausa za su karanta labaran da suka cancanci yabo cikin mako 12.
Waɗanda suka yi nasara za su karanta labarinsu gaba ɗaya da kansu a ɗakin gabatar da shirye-shirye na BBC.
Za a watsa karatun labaran da aka naɗa a tashar BBC Hausa da tashoshin rediyo na abokan hulɗarmu.
Za a wallafa kuma a watsa muryoyi da sunaye da adireshi da shekarun marubutan da labaransu suka yi nasara a gasar da aka naɗa da sunan marubutan, a shafin BBC Hausa na intanet da BBC Hausa Rediyo da shafukan sada zumunta na BBC kamar Twitter da Instagram da Facebook.
BBC ka iya barin labarin naki a kan intanet domin amfanin gaba bayan karantawa a rediyo.
Domin ƙarin bayani kan yadda BBC za ta yi amfani da bayanan naku,
BBC ka iya gayyatar waɗanda suka yi nasara da wasu waɗanda labaransu suka cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja.
BBC za ta ɗauki nauyin kuɗin mota da masauki wanda bai wuce ƙima ba. Waɗanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya.
Tawagar BBC Hausa za ta karɓi bayananku don Gasar Gajerun Ƙagaggun Labarai ta Mata.
Tawagar BBC Hausa za ta amsa bayananku ta adireshin imel da shafin intanet da BBC ke amfani da shi.
Idan muka watsa labarinki, yana iya kasancewa a shirye-shiryen da ake adanawa a intanet kuma ana iya amfani da labarin naki a shirye-shiryenmu na gaba. Domin karin bayani dangane da yadda BBC ke alkilta bayananmu za ku iya ziyartar shafin da ke bayani dangane da yadda muke amfani da abokan huldarmu:
Me muke karɓa kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?
Dole ne shekarunki su kai tsakanin 18 zuwa 35 sannan za ki iya shiga gasar ya zuwa ranar 24 ga watan Agustan 2024. BBC za ta karɓa kuma ta yi aiki da bayanan da suka shafe ki waɗanda kika aiko mana.
Dole ne a aika duka labarai ta hanyar manhajar uploader da ke (Yadda za a shiga gasar) wanda ke kan shafinmu na bbchausa.com kuma dole ne bayanan su ƙunshi waɗannan dangane marubuciya/marubuta:
- Suna
- Lambar Waya
- Adireshin email
- Adireshin gida (gari ko ƙauye)
- Shekarunki
- Taƙaitaccen tarihinki
- Taƙaitaccen bayani kan labarinki
Idan aka zaɓi labarinki, BBC na da ikon buƙatar ganin shaidar shekarunki don tabbatar da cewa kin cika sharuɗɗan shiga gasar. Idan aka buƙaci ganin shaidar shekarunki, za a yi haka ne ta hanyar gani da ido.
Waye Mai Sarrafa da Bayanai?
BBC ce 'sarrafa bayanai' da kika aiko. Hakan na nufin cewa BBC za ta yanke shawarar abin da za ta yi da bayananki, da hanyoyin da za a yi amfani da su.
Don guje wa shakku, za a karɓi bayananki kuma a yi amfani da su bisa dalilin da aka tsara a bayanan tsare sirrinki kawai.
Sarrafa bayananki kan ƙa'ida
BBC ta dogara ne kan buƙatunta da ke bisa ƙa'ida a matsayinta na kafar yaɗa labarai don sarrafa bayananki wajen shiga gasar, da bibiyar gawarazan gasar da mu'amala da masu bibiyarmu.
A wajen dogaro da buƙatunta da ke bisa ƙa'ida don sarrafa waɗannan bayanan, BBC za ta daidaita buƙatunta wajen tallata wannan gasa tare da kare bayanan sirrinki.
Muna aika wa wasu a wajen BBC bayananki?
Idan kika shiga gasar, BBC za ta aika bayananki zuwa wani shafin sarrafa bayanai da BBC ta saba amfani da shi, wanda kuma zai samar wa BBC wurin da zai taimaka mana mu gudanar da gasar.
Muna tabbatar da cewa shafin da za mu yi amfani da shi yana da ƙa'idojin da suka dace wanda zai tabbatar da cewa ba za su iya yin komai da bayananki ba sai idan mun ba su umarnin yin haka.
Ba za mu yaɗa bayananki da wani ko wasu ba har sai idan doka ta ba mu izinin yin haka.
BBC na aiki da wasu waɗanda ba ma'aikatan BBC ba waɗanda muke aiki da su domin gudanar da ayyukanmu. Waɗannan abokan hulɗar suna amfani da bayananku a maimakon BBC ba a ƙashin kansu ba. Muna amfani da tsarin rumbun aiko da saƙonni wajen karɓa da killace bayanan naku na sirri saboda wannan gasar.
Idan kin samu nasara to za a miƙawa alƙalan gasar bayananki.
Harwayau, gidajen rediyo FM abokan hulɗarmu su ma za su iya watsa labaran naku.
Za kuma mu iya bai wa wasu abokan hulɗar tamu bayanan naki idan akwai buƙatar hakan ko kuma idan doka ta amince.
Adana bayananki
Idan labarin da kika aiko bai yi nasara ba, BBC za ta adana bayananki da abin da kika aika har tsawon wata shida daga ranar da kika ɗora bayanan, daga nan kuma za a goge shi.
Idan aka sanya labarinki cikin waɗanda suka kai mataki na gaba ko kuma ke ce kika yi nasara, za mu adana bayananki har tsawon shekara biyu bayan an rufe gasar.
Idan kika kai mataki na gaba ko kuma ke ce tauraruwar gasar, sannan muka wallafa labarinki tare da sunanki, to BBC za ta adana bayananki har abada saboda dalilai na aiki. Za a adana bayananki a tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka.
Haƙƙoƙinki da ƙarin bayanai
Kina da haƙƙoƙi ƙarƙashin dokokin kare bayanai. Za ki iya neman kwafin bayananki da BBC ta adana.
Kina da ƴanci ki nemi a goge bayananki da muka karɓa sai dai akwai iyakoki da togaciya kan wannan ƴancin, abin da zai sa BBC ta ki amincewa da buƙatarki.
A wasu lokutan, kina da ƴanci ko taƙaita ci gaba da amfani da bayaninki ko ki nuna rashin amincewa da ci gaba da neman bayananki.
Kina da ƴancin ki nemi mu tura miki bayananki ko wata hukumar, a wasu lokutan.
Za ki iya tuntubar Ofishin Kare Bayanai a Data Protection Officer idan kina da tambaya, idan kuma kina so ki samu ƙarin bayanai a kan ƴancinki, ziyarci sashin Bayanan Sirri na BBC da Ka'idojin Kare Bayanai:
Idan kina da wata damuwa kan yadda BBC take mu'amala da bayananki na sirri, za ki iya bayyana damuwarki da hukumomin da suke sa ido a Birtaniya, wato Ofishin Kula da Bayanai (ICO):
Sanarwa kan sabunta wadannan bayanai
Za mu sabunta waɗannan bayanai idan akwai gagarumin sauyi kan yadda muke amfani da bayananki.