Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea na bincike kan nuna wariyar da aka yi wa Son
Chelsea ta ce za ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo game da binciken da take yi na nuna wariyar da aka yi wa dan wasan gaban Tottenham Son Heung-min a Stamford Bridge.
Wannan lamari ya faru ne lokcin da Son ya je bugo kwana a minti 45 na biyu na wasan, wanda aka tashi 2-2 a Premier.
A baya kungiyar ta taba haramtawa wasu magoya bayanta shiga kallon wasanta na har abada saboda irin wannan laifi na nuna wariya.
Cikin wata sanarwa Chelsea ta ce ba za ta yarda da nuna dabi’ar nuna wariya ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Chelsea ba za ta jurewa cin zarafin abokan wasanta ba ko nuna musu wariya ba, sai dai akwai wasu bara gurbi da ke kiran kansu magoya bayan Chelsea da ke da irin wannan dabi’un, wanda kuma abin kunya ne ga kungiyar da kocinta da ‘yan wasanta da ma’aikatanda har ma da magoya bayanta na gaskiya.
“Muna bincike kan wannan lamari, kuma idan aka gano wadanda suka yi wannan za su fuskanci tsattsauran hukunci daga kungiyar.
“Ba za mu taba amincewa da wariyar launin fata ba a Chelsea ko kuma kasarmu.”