Shin kotu za ta iya raba rikicin da ya turnuke a jam'iyyar PDP?

Lokacin karatu: Minti 3

A bayanne ta ke cewa rikicin cikin gida na babbar jam'iyyar hammaya ta PDP na ƙara dagulewa, bayan da wasu ƴaƴanta suka bai wa hammata iska a shalkwatar jama'iyyar da ke Abuja.

Magoya bayan shugabancin Tanimu Turaki, da kuma na Abdulrahman Muhammad da ke samun goyon bayan ministan babban birnin tarraya Abuja, sun yi taho mu gama a gaban jami'an tsaro yayin da dukkansu ke neman karɓe iko da shalkwatar jam'iyyar, har ta kai ga jami'an tsaro sun harba hayaƙi mai sa hawaye.

Wannan ya biyo bayan irin kulli-kurciyar da aka rinka yi da hukunce-hukuncen kotu kan batun shugabanci da takarar shugabanci da kuma shi kansa babban taron da jam’iyyar ta gudanar a baya-bayan nan.

A bisa tsari, kotu ce za ta raba gardama, sai dai ya zuwa yanzu, hukunce-hukuncen kotunan da aka samu ba su yi wani tasiri ba wajen yayyafa ruwa ko samar da mafita ga matsalolin jam’iyyar ba.

Masana harkokn siyasa a Najeriya irin su Farfesa Abubakar Kari sun ce al'amarin bai ba su mamaki ba.

''Duk da yake abin bai yi daɗi ba, ka ga irin wannan kacaniyya da tirka-tirka, a zo da ƴan sanda a jefa borkonon tsohuwa da sauran su''.

''Kuma abubuwan da suka biyo baya duka, ba wani abin mamaki ba ne, abu ne da aka yi hasashen cewa zai faru,'' in ji shi.

Masanin ya ce dalilin da ya sa ya faɗi haka shi ne jam'iyyar ta riga ta dare gida biyu kuma kowane na iƙirarin cewa shi ne na zahiri kuma muddin irin wanann ya faru to dole a yi sa-in-sa.

''Wannan gwada ƙwanji da aka yi, daman abin da ake son a cimmawa shi ne kowane ɓangare ya nuna wa duniya cewa shi ne yake riƙe da madafun iko kuma shi ne ya kamata a saurara''.

Farfesa Kari ya ce wannan ya nuna cewa rikicin na PDP ya kai intaha saboda ba ya tsamanin ɓangarorin biyu za su saurari juna.

Masanin ya ce akwai wasu da ke nuna shakkun cewa abu ne mai wuya a shawo kan rikicin saboda ana zargin cewa babbar anniyar ɗaya daga cikin ɓangarorin ita ce gurgunta jam'iyyar.

''Su abin da suke so shi ne wutar wannan rkici ta ci gaba da ruruwa, ta yadda ba za a samu maslaha ba, kuma ya zuwa yanzu haƙarsu na cimma ruwa''.

Sai dai masanin ya gabatar da wasu hanyoyin shawo kan matsalar saboda a cewarsa akwai ƴan jam'iyyar da dama da ke son su ga an kashe wannan wuta.

''Ya kamata su yi zawarcin waɗanda ba sa wancan ɓangare kuma akwai su da dama, akwai waɗanda suka koma gefe, sun sa wa sarautar Allah ido kuma irin wadannan mutane suna nan da yawa''

''Ya kamata waɗanda suke son a sasanta wannan rigima su neme su, su yi zama da su, a rarrashesu su mara wa jam'iyya baya sannan ya kamata a yi zawarcin irin su Sule Lamido domin jin ƙorafe-ƙorafensu,'' in ji shi.

Masanin ya ce idan aka yi haka ne za su iya tunkarar ɓangaren da ba ya son a yi sulhu saboda su na da ƙararraki a gaban kotu.

''Ƙarshen ta dai makomar jam'iyyar PDP kotu ce za ta yanke shi kamar a baya,'' in ji shi.