'Ba zan zuba ido ina kallon masu cin dunduniyar jam'iyyarmu su kai ta ƙasa ba'

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ake ci gaba da takaddama kan taron jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, Sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa, wajen haɗa kan ƴan jam'iyyar musamman waɗanda ke ganin an ɓata musu, don samun nasararta a zaɓen 2027 da ke tafe.

A hirarsa ta farko da sashin Hausa na BBC Tanimu Turaki wanda aka zaɓa a baban taron jam'iyyar na ƙasa da aka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo, ya ce a yanzu lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi da ƙarfe don ciyar da jama'iyyar gaba.

Ko da yake ya yi gargadin ba zai zuba ido yana kallo masu cin dunduniyar jama'iyar su kai ta ƙasa ba.

'' Abu na farko da zamu fara yi shi ne, za mu je mu bi duk ƴaƴan jam'iyyarmu da waɗanda suka fusata domin an ɓata mu su rai da waɗanda suka fusata ba da wani ƙwararan dalili an saɓa mu su ba da kuma waɗanda suke nan suka zauna suka zura wa sarautar Allah ido da kuma wadanda suka fita za mu je mu nemi su''

''Wanda ya kamata a ba shi hakuri, zamu ba shi hakuri, wanda ya kamata mu durƙussa mu ce mun tuba domin a dawo a taimaki dimokraɗiyya, domin dimokraɗiyya za a taimakawa '', in ji shi.

Sai dai akwai waɗanda suke ganin rikicin na PDP ya riga ya kai wani mataki da ba za a iya warware shi ba musaman idan aka yi la'akari da cewa a yanzu shugabanci biyu ne a jam'iyyar.

A yanzu bayan shi da aka zaɓa akwai wani ɓangaren da ke iƙirarin cewa shi ne halasttacen shugabancin jam'iyyar kuma ana ganin wannan babban ƙalubale da ke gaban sabon shugaban jam'yyar.

Haka kuma wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar sun ƙi amincewa da matakan da aka ɗauka a babban taron ciki har da sallamar ministan Abuja Nyesom Wike da kuma wasu daga jam'iyyar.

Sai dai Tanimu Turaki cewa yayi:

'Ba zai yu a ce a kwamitin gudanarwa na jam'iyya a ce akwai mutane 21 ba, a wayi gari a ce guda 3 sun yi wa jam'iyyar zagon ƙasa, an ladabtar da su, su ce sun koma gefe su ma sun dakatar da mutane 18 ''

''Na biyu ba zai yiwu a ce a ko yau she ku zo ba abinda ku ke yi , sai cin mutuncin jam'iyyar, ku na yi ma ta zagon ƙasa, ku ce a bar ku, ai yanzu dai an riga an koresu'' inji shi

Shugaban na jami'iyyar PDP ya nanata cewa za su yi sulhu ne da waɗanda suke son sulhu.

''Za mu nemi a yi sulhu da waɗanda suke sulhuntuwa, mutumin da ya ɗauko makami ya riƙe. Ya ɗauki wuka, ya ɗauki sanda ya afkawa maka, ka ce zo mu yi sulhu?''

''Duk mutumin da zai fito kullum, ba abinda yake yi sai yi wa jam'iyya zagon ƙasa da zagin shugabanni yaushe za ka je ka zauna ka ce za ka yi sulhu da wannan mutumin''

Shugaban jami'yyar ta PDP ya kuma ce yana da ƙwarin gwiwar cewa jam'iyyarsu ce za ta ƙwace mulki a zaɓen 2027.

''Mu kali halin da ƙasar nan ta ke ciki a maganar tsaro da tattalin arziki, wani ɗan Najeriya ne a yanzu za ka ce ya zo ya zaɓi jam'iyyar APC'',

''Abin da ke gabanmu shi ne da ƙuri'a nawa ne za mu ci zaɓe, domin an gama mana kamfe, in Allah ya yarda Jam'iyyar PDP za ta sake kafa gwamnati a 2027'' in ji shi.