Wane ne layya ta wajaba a kansa?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Layya ɗaya ce daga cikin fitattun ayyukan ibada na addinin Musulunci, wadda ta zamo koyi da umarnin da Allah SWT ya bai wa annabi Ibrahim, na yin sadaka da ɗansa Isma'il.

Kasancewar ta ɗaya daga cikin ayyukan ibada masu muhimmanci, abu ne da ya kamata Musulmai su mayar da hankali a kai domin fahimtar yadda ake yin ta.

Mene ne hukuncin layya?

Sheikh Tukur Adam Almannar

Imam Tukur Adam Almannar, malamin addinin Musulunci a birnin Kaduna da ke Najeriya, ya ce "Layya sunna ce ta manzon Allah, mai ƙarfin gaske, ba ta kai girman wajibi ba.

"Sunna ce wadda manzon Allah bai taɓa bari ta wuce shi ba. Duk lokacin da layya ta zo manzon Allah yana yi da raguna biyu, ɗaya ga iyalinsa, ɗaya kuma ga al'ummarsa."

Wane ne layya ta wajaba a kan shi?

Game da waɗanda layya ta wajaba a kansu, Sheikh Tukur Almannar ya ce "Layya tana rataya a kan kowane Musulmi, namiji ko mace, baligi, mai hankali , mai yanci, wanda ke da halin yin layyar."

Wannan na nufin idan mutum Musulmi na sana'a ko aikin da ake biyan shi albashi wanda zai wadace shi biyan buƙatu har ya samu ragowa, to layya ta rataya a kansa.

Malamai sun nuna cewa babu bambancin wajen nauyin da ya rataya na yin layya a kan mace Musulma ko namiji Musulmi.

Waɗanda layya ba ta wajaba a kansu ba

Malamin ya bayyana cewa layya ba ta wajaba a kan akasin waɗanda aka wajabta wa yin ta.

"Ba ta wajaba a kan wanda ba musulmi ba, haka nan ma karamin yaro wanda bai balaga ba, ba ta wajaba a kan bawa, ko wanda ba ya da hali, da kuma wanda ba ya da halin sayen dabbar layya," in ji Sheikh Tukur Almannar.