Me ya sa mabiya addinai ke yin layya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Orchi Othondrila
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Musulmai a faɗin duniya na shirin gudanar da bukukuwan babbar sallah, da aka fi sani da sallar layya - inda ake yanka dabbobi - domin yin koyi da annabi Ibrahim, lokacin da ƙudiri aniyar yanka ɗansa Annabi Isma'il.
Annabi Ibrahim A.S shi ne aka fi sani da Abraham a addinan Kiristanci da Yahudanci.
Layya ta samo asali ne lokacin da Annabi Ibrahim ya yi mafarkin Ubangijinsa na ba shi umarnin yanka ɗansa Annabi Isma'il domin neman kusanci da shi.
A lokacin da ya bai wa ɗan nasa (Annabi Isma'il) labarin mafarkin, sai annabi Isma'il ya ce wa mahaifinsa nasa, ''ka yi duk abin da Ubangijinka ya umarce ka a kaina''.
A daidai lokacin da annabi Ibrahim ke dab da yanka ɗan nasa, sai Ubangiji ya dakatar da shi, tare da musanya masa shi da rago, wanda ya yanka a madadinsa.
Daga nan ne Musulmai a faɗin duniya ke yanka dabbobi iri-iri a matsayin ibada, a duk lokacin da ranar ta zagayo.
A addinin musulunci layya wajibi ne idan mutum na da hali.
Ko ya lamarin layya yake a sauran manyan addinai?
Yaya addinan Kiristanci da Yahudanci ke kallon layya?
Addinin Yahudanci

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tarihin layya a addinin Yahudanci da Kiristanci kusan a iya cewa iri ɗaya ne da na Musulunci.
Litattafan addinin Yahudanci, sun yi magana kan sadaukar da dabbobi, a lokuta da kuma wurare daban-daban, kamar yadda Rabbi gary Somers, shugaban sashen addinin Yahudanci na jami'ar Leo Baeck da ke Birtaniya ya bayyana.
“To amma a yanzu ba ma yin waɗannan yanke-yanke, kasancewa wuraren da aka keɓe domin yinsu a yanzu babu su, a maimakon haka mukan tuna da wannan ibada ta hanyar yin addu'o'i,” in ji shi.
Rabbi Dr Bradley Shavit Artson shi ne mataimakin shugaban jam'iar addinin Yahudanci ta Amurka.
“An haramta sadaukar da dabbobi bayan daular Rum ta ruguza wurin bautar addininmu na biyu mafi tsarki a duniya. Da dama daga cikin mabiya addininmu a yanzu sun yi amanna cewa an haramta yanka dabbobi, to amma wasu na ganin cewa bayan zuwan 'Mahadi' an maido da ibadar,'' in ji shi.
Wurin da ake wannan ibadar shi ne 'Dutsen Ibada', wanda ke wurin da Masallacin Al-Aqsa ya ke a yanzu, watau tsohon Birnin Kudus.
Mabiya addinin Yahudanci na fatan sake gina wurin ibadar, suna masu imanin cewa idan aka sake gina wurin bautar, za su ci gaba da yanka dabbobi domin sadaukarwa.

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da mafi yawan mabiya addinin Yahudanci a yanzu ba sa gudanar da ibadar yanka dabbobi saboda rashin wuraren ibadarsu, wasu mabiya addinin kamar Samariyawa a Birnin Kudus har yanzu sukan sadaukar da dabbobin a lokutan bukukuwan 'Passover'.
Wasu kuma na sadaukar da kuɗi kwatankwacin dabbobin da za su yankan.
Sadaukar da dabbobi kamar tumaki da ɓauna ko shanu da awaki - abu ne mai kyau a addinance, in ji Dakta Artson.
“Nau'in dabbobi masu shayarwa ne aka keɓance domin yankawa a matsayin layya , inda ake rabar da naman ga iyalan malaman addinin Yahudanci, sauran kuma waɗanda suka yankan tare da iyalansu su yi amfani da shi'', domin tunawa da tarihi.
Duk da cewa ba kowa ba ne ke sadaukar da dabbobin, amma cin naman dabbobin ya kasance ginshiƙi a duka bukukuwan addinin Yahudanci.
Sadaukar da dabbobi a addinin Yahudanci abu ne mai faɗin gaske, kuma ya bambanta dangane da dalilin yankan.
Tun da farko, bukukuwan ziyarar addinin Yahudanci uku - Pessah (bikin zagayowar tunawa da 'yancin Yahudawa, lokacin da suka fice daga Misra) da Shavout (bikin tunawa da ranar da aka saukar da littafin Attaura, da kuma Sukkot (bikin da ake kwashe kwana bakwai ana gudanarwa, domin tunawa da bai wa Yahudawa kariya a lokacin da suka fice daga Misra) - na da matuƙar muhimmanci wajen sadaukar da dabbobi.
Rabbi Gary Somers, shugaban sashen addinin Yahudanci na jami'ar Leo Baeck da ke Birtaniya ya yi bayanin cewa wasu bukukuwan addinin irin su Rosh Hashanah (Bikin sabuwar shekarar Yahudanci) da ibadar Yom Kippur (Ranar Tsarki) duka ana yanke-yanken dabbobi.
Akwai tarihin Annabi Ibrahim A.S, na layya da ɗansa Annabi Isma'il A.S a cikin littattafan addinin Yahudanci.
To sai dai, Umarnin sadaukar da dabbobi ya zo a wurare mabambanta ga mabiya addinin Yahudancin.
Addinin Kiristanci

Asalin hoton, Getty Images
Addinin Kiristanci ya samo asali daga addinin Yahudanci, kuma littattafan addinan biyu na da abubuwa masu kamanceceniya da juna.
A wancan lokacin, akan yanka dabbobin ne a addinin kirista da nufin neman tuba daga wanu zunubi da aka aikata.
To amma a yanzu mabiya addinin ba sa wannan ibadar, saboda suna ganin mutuwar Yesu a matsayin cikakkiyar sadaukarwa ga mabiya addinin.
Mabiya addinin Kiristanci na ɗaukar Yesu a matsayin 'ɗan Allah'.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa babu tanadin yanka a addinin, a lokuta da dama ''idan mutum ya yi bakance ko alƙawarin sadaukar wa ubangiji wani abu, to akan yanka dabba”.
Baya ga alaƙa da addinin Yahudanci, babu wata ibadar yanka a adinin Kiristanci da sunan sadaukarwa ga ubangiji, in ji Dakta Reberio.
Haka kuma ba a iyakance cin nama a addinin ba. A ƙasashe da dama, al'ada ce cin tsoka a lokutan bikin 'Passover' na mabiya addinin Yahudanci.
Dakta Reberio ya ce a lokutan bikin a Italiya, wajibi ne cin naman kafin bikin Easter.
Haka kuma, a addinin Kiristanci babu ibadar korban - wadda Yahudawa ke yi na yanka dabbobi domin ibada.
Addinin Hindu

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa akwai saɓani dangane da yanka dabbobi a addinin Hindu, ibada ce da wani sashe na mabiya addinin ke gudanarwa.
Alal misali, a wasu sassan Indiya da Bangladesh, akan sadaukar da dabbobi a wasu ibadojin addinin, ciki har da bukukuwan Durga Puja da Kali Puja.
“Mafi yawan littattafan addinin Hindu, kamar littafin Ramayana da Mahabharata, da littafai masu tsarki na Puranas, sun yi magana kan yanka da sadaukar da dabbobi," in ji Dakta Kushal Baran Chakraborty, malami a jami'ar Chittagong da ke Bangladesh.
"A cikin littafin Rigveda, ɗay daga cikin tsofaffin littattafan addinin Hindu an ambaci yanka dabbobi domin sadaukarwa da nufin samun kuɓuta daga bautarwa'', in ji shi.
Sadaukar da dabbobi sanannen abu ne a zamanin Vedic, da aka yi tsakanin shekarar 1500 da 500 BC
Akan sadaukar da naman ga 'abin bauta' sannan kuma malaman addinin su ci naman.
Haka kuma akwai saɓani kan ibadar yanka dabbobi tsakanin masana a wannan zamani a Indiya.
Dakta Chakraborty ya ce har yanzu ana yanka dabbobi domin sadaukarwa a wasu tsoffin wuraren ibadar addinin Hindu.
Ya bayar da misalan wasu wuraren ibadar kamar Dhakeshwari a Bangladesh da Tripura Sundari da Kamakhya da kuma Kalighat Kali a India.
To sai dai Dakta Rohini Dharmapal wata ƙwararriyar addinin Hindu, ta ce a yanzu ba a yawan sadaukar da dabbobi a Indiya.
Dakta Chakraborty ya ce sadaukar da dabbobi a yanzu a addinin Hindu ya ƙarfafa gamsar da kai, da gasa ko kuma shiga wani abu, saɓanin neman kusancin abin bauta.
Ya ƙara da cewa sannu a hankali ibadar na rasa ƙimarta.
Ƙungiyoyi da dama a Indiya sun dakatar da ibadar yanka dabbobi bisa raɗin kansu a wasu wuraren ibadar, sanna suna kiran a haramta yanka dabbobi domin neman kusancin ubangiji.
Mabiya addinin Hindu a ƙasashen Sri Lanka da Nepal sun haramta yanka dabbobi. To sai dai ba koyaushe mabiyan ke biyayya ga haramcin ba.











