Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Babu hujjar da ke nuna Shugaba Putin na da lalurar ƙwaƙwalwa - CIA
Babu wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin taɓi-taɓi ne ko kuma yana fama da lalura, a cewar shugaban hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA.
An yi ta samun jita-jita a baya-bayan nan cewa Mista Putin, wanda ke cika shekara 70 da haihuwa a 2022, na fama da rashin lafiya kamar cutar daji - wato kansa.
Sai dai William Burns ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da hakan, yana mai cewa "da alama ma lafiya ta yi masa yawa".
Ita ma Fadar Kremlin ta Rasha ta yi watsi da iƙirarin rashin lafiyar shugaban a matsayin "labarin boge".
Lamarin na zuwa ne yayin da Amurka ke cewa za ta aika wa Ukraine ƙarin makamai masu dogon zango.
Tun farko Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce yanzu muradin Rasha ba wai "ƙwace gabashin Ukraine ba ne kawai", yana mai cewa manufarta ta sauya sakamakon ba wa Ukraine irin waɗan nan makamai.
'Mutumin da ya yi imani da ƙarfin iko'
"Akwai jita-jita mai yawa game da lafiyar Shugaba Putin kuma mu dai abin da muka sani shi ne yana cike da ƙoshin lafiya," a cewar Mista Burns yayin wani taro na tsaro mai taken Aspen Security Forum a Colorado.
Da yake mayar da martani cikin raha, ya ƙara da cewa kalaman nasa ba su ne ƙarshe ba game da rahoton hukumomin leƙen asiri.
A ranar Alhamis ne Fadar Kremlin ta musanta batun rashin lafiyar ta Mista Putin bayan wasu da suka kira kansu "ƙwararru kan tattara bayanai" sun yaɗa labarai daban-daban kan lafiyar shugaban.
"Amma ba wani abu ba ne illa labarin ƙarya," kamar yadda kakakin Putin, Dmitry Peskov, ya faɗa wa manema labarai.
Mista Burns wanda ya yi aiki a matsayin jakadan Amurka a Moscow, ya ce ya sha yin hulɗa da shugaban na Rasha fiye da shekara 20.
Mista Putin "ya tasirantu da ƙarfin iko, da tilasta wa mutane, da ramuwar gayya" kuma waɗannan halaye sun ƙara tsauri cikin shekara 10 da suka wuce yayin da adadin mashawartansa ke ƙara raguwa, a cewar shugaban na CIA.
"Ya yi imanin cewa ƙaddara ce ta sharɗanta masa a matsayinsa na shugaban Rasha ya mayar da ƙasar kan turbar iko. Yana ganin babbar hanyar yin hakan ita ce ya faɗaɗa iko a maƙwabtansa kuma ba zai iya yin hakan ba har sai ya samu iko kan Ukraine."
Mista Burns ya je Moscow a watan Nuwamba don yin gargaɗi ga Rasha idan ta sake ta afka wa Ukraine bayan sun samu rahotannin shirin yin hakan.
Sai dai shugaban na CIA ya ce ya bar ƙasar "cikin damuwa fiye da sanda ya shige ta".
Ya ƙara da cewa: "Putin ya yi imani sosai da manufarsa. Na sha jin sa yana faɗa a ɓoye tsawon shekaru cewa Ukraine ba cikakkiyar ƙasa ba ce.
"To, cikakkun ƙasashe na iya mayar da martani kuma abin da Ukraine ke yi ke nan."
Amurka ta yi hasashen cewa an kashe dakarun Rasha kusan 15,000 a Ukraine kuma an raunata wasu kusan 45,000, in ji Mista Burns.