Yadda Rasha ta yi wa Ukraine fintinkau a nahiyar Afirka

    • Marubuci, Daga Paul Melly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa Programme, Chatham House, London

Jawaban da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yake yi wa taruka da majalisun dokoki a fadin duniya sun zama tamkar ruwan dare a tsarinsa na difilomasiyya na watannin baya bayan nan.

Sai dai a lokacin da ya yi jawabi ga Kungiyar Tarayyar Afirka ranar Litinin, shugabannin kasashe hudu ne kawai daga nahiyar suka saurare shi, sauran sun samu wakilci ne daga jami'an kasashensu.

Rashin halartar taron daga bangaren shugabannin Afirka wata alama ce da ke nuna irin wahalar da Ukraine take sha wurin isar da sakonta ga nahiyar mai kunshe da kasashe 54 inda take da ofisoshin jakadanci 10 rak - wato daya bisa hudun wadanda Rasha take da su a nahiyar.

Don haka a yunkurin da Mr Zelensky yake yi na sauya tunanin kasashen Afirka game da mamayar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi musu, ba zai iya yin amfani da batun siyasa ko tsaro ya ja hankalinsu idan aka kwatanta da yadda Moscow take yi ba.

Ukraine ba sananniya ba ce a duniya game da karfin soji kuma ba mambar dindindin ta Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba ce, kamar Rasha.

Hakan ne ya sa shugabannin kasashen nahiyar afirka suka yanke shawarar cewa ba za su iya yin fito-na-fito da Rasha kamar yadda kasashen Yamma suke yi ba.

Matakin nasu yana da matukar muhimmanci a yanzu musamman ganin yadda Rasha ta hana Ukraine fitar da hatsi irin su alkama zuwa kasashen waje.

Lamarin ya ta'azzara matsalar rashin abinci da ake fama da ita, batun da ya sa aka samu hauhawar farashin kayan abinci kamar alkama da man girki da makamantansu a Afirka, inda ake da karancinsu.

A farkon watan da muke ciki shugaban Senega Macky Sall, wanda shi ne shugaban Tarayyar Afirka a yanzu, ya je wurin shakatawa na Sochi da ke gabar tekun Bahar Aswad da ke Rasha domin tattaunawa da Mr Putin kan yadda za a kawar da tarnakin da ake fuskanta wajen fitar da kayan abinci daga Rasha da Ukraine zuwa kasashen waje.

Kazalika a makon jiya shugaban kasar Afirka ta kud Cyril Ramaphosa ya kira Mr Putin ta wayar salula domin tattaunwa kan fitar da kayan abinci da irin shuka da takin zamani daga Rasha zuwa Afirka.

A gefe guda, alamu sun nuna cewa mamayar da Rasha take yi wa Ukraine tana iya sa wa ta rage yawan sojojinta a Afirka, yayin da aka samu wasu rahotanni da ba a tabbatar ba da ke cewa Rasha tana yin kiranye ga sojojin hayar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka wadanda aka girke a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Hakan ba zai zama abin mamaki ba, idan aka yi la'akari da matukar bukatar da Rasha ke da ita ta sojoji da za ta tura yankin Donbas.

Sai dai babu wata alama dake nuna cewa an rage sojojin haya na Wagner daga Mali - inda ake yawan ganinsu suna aiki tare da dakarun kasar.

Dangantaka kan sha'anin tsaro

Bugu da kari, ana ci gaba da yaukaka dangantaka ta soji da tsaro tsakanin Raha da nahiyar Afirka.

Kamaru ita ce kasa ta baya bayan nan da ta kulla irin wannan jarjejniya da Rasha.

Ministan Tsaron kasar Joseph Beti Assomo ya ziyarci Moscow a watan jiya inda ya hadu da takwaransa na Rasha Sergei Shoigu suka sanya hannu kan jarjejeniyar tsaro ta shekara biyar.

Manufar wannan jarjejeniya ita ce musayar bayanan sirri da bayar da horo da hada gwiwa wajen yaki da ta'addanci da fashin teku. Kazalika sun amince su gudanar da atisayen hadin gwiwa.

A hakikanin gaskiya, wata yarjejeniya da suka kulla a 2015 ta bayar da dama ga Rasha ta aike da makaman atilari da kayan yaki a sama - wadanda ke da matukar amfani wajen yaki da masu ikirarin jihadi da ke lardin Arewa Mai Nisa na kasar Kamaru.

Ko da yake jarjejeniyar da suka kulla a baya bayan nan ba ta yi cikakken bayani ba, amma ta jawo ce-ce-ku-ce a kasashen Yammacin duniya.

Makonni kadan bayan haka, darakta kan kasashen Afirka a Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa, Christophe Bigot, ya ziyarci Yaoundé, da alama domin ya tabbatar wa Firaiministan Kamaru Joseph Dion Ngute cewa Paris za ta ci gaba da goyon bayansu a kan sha'anin tattalin arziki da al'adun gargajiya da kuma hadin kai wurin yakar 'yan ta'adda.

Shugabannin kasashen Yamma suna kallon Rasha a matsayin wata babbar barazanar tsaro, wadda ke kalubalantar tsarin dimokuradiyyar da suka kafa a sassan duniya.

Sai dai wasu kasashen Afirka suna ganin ba haka batun yake ba, suna masu cewa bai kamata a rika yi wa gwas,mnatin Putin kallon maras imani ba.

Kyamar kasashen Yamma tana karuwa

Wasu daga cikin kasashen da suka dade suna kawance da Yammacin duniya sun ki sukar matakin da Mr Putin ya dauka.

Alal misali, Senegal, ta zabi kin bayar da goyon baya ga kudurin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya na ranar 2 ga watan Maris wanda ya bukaci a tilasta wa Rasha ta daina amfani da karfi a kan Ukraine.

Kazalika Kamaru ma ta dauki irin wannan mataki - jakadanta a Majalisar Dinkin Duniya ya koma kasarsu a farkon watan Maris domin ya kaurace wa kada kuri'a a kan batun.

Haka kuma ranar 7 ga watan Afrilu kasar ta kaurace wa kada kuri'a a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya domin dakatar da Rasha daga Hukumar kare hakkin bil adam ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ra'ayoyin 'yan kasar sun taka muhimmiyar rawa kan batun.

Goyon bayan Faransa da Amurka da Birtaniya ba batu ne da al'ummar nahiyar Afirka suke so a-kai-a-kai ba kuma gwamnatin Kamaru, kamar sauran kawayenta, sun amince cewa ba za su goyi bayan lamarin da 'yan kasashensu ba sa kauna ba.

A hannu guda kuma, Kamaru na ɗaukar matakin sanya hannu kan yarjejeniyar aikin soji da Rasha, duk da cewa Rashar na ci gaba da kai hare-hare biranen Ukraine.

Kamaru ta yi hakan ne don matsalolin tsaron da take fama da su.

Shugaban ƙasar Paul Biya na fama da matsalolin tsaro biyu a lokaci guda - da yaƙi da ƙungiyar Boko Haram da ƙungiyar Iswap a arewa mai nisa, a hannu guda kuma tana fama da ƴan awaren da ke son ɓallewa da suke yankunan renon Ingila a kudu maso yamma da arewa maso yammacin ƙasar.

Baya ga Rasha, Kamaru ta ƙulla yarjejeniya da Faransa da China da Brazil da Turkiyya - da kuma Amurka.

A Jamhuriyar Tsakiyar Afirka kuwa, tun shekarar 2018 Wagner ke horar da sojoji kuma mutanensa sun taimaka wa dakarun gwamnati suka daƙile wani harin ƴan aware da aka kai Bangui a farkon 2021.

Amma ƙwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun zargi Wagner da aikata munanan take hakkin bil adama a kan fararen hula; a baya-bayan nan an zargi mayaƙansa da kashe fararen hula ƴan ƙauyukan da ke kusa Bria, cibiyar da ake haƙar zinare.

Sannan kuma Wagnere na aiki da dakarun sojin Mali, inda aka yi zargin an aikata take hakkin ɗan adam, ɓangarorin dakarun biyu abokan juna sun azabtar da kashe mutanen ƙauyukan.

An zargi dakarun sojin Mali da sojojin haya na Rasga da kashe fiye da mutum 300 a Moura a watan Maris.