Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko za mu iya sanin mutum nawa aka kashe a yakin Ukraine?
Wani hari ta sama da Rasha ta kai kan wani gini a garin Lysychansk, na Luhansk a Ukraine ya kashe mutum hudu da ke boye a ciki.
Sannan a kusa da birnin Severodonetsk wasu karin mutum biyu sun mutu kwana guda bayan da Rasha ta yi wa birnin luguden wuta ta sama.
Haka kuma mutum guda ya rasa ransa bayan da sojojin Ukrain suka kai harin bom a wajen birnin Donetsk.
Kazalika sojojin Rasha sun kashe wasu mutum hudu bayan da suka bude wuta a garin Sadivska da ke arewa masu yammacin yankin Sumy.
Ana tunanin duka mutanen da aka kashe a wadannan hare-hare da suka faru a rana guda a cikin watan Yuni fararen-hula ne.
Tun daga ranar 24 ga watan Fabrairu, mutum guda cikin uku da suka mutu a Ukraine na mutuwa ne ta wannan hanya, kamar yadda wata kungiya mai zaman kanta a Amurka da ke kula da yakin soji, mai suna Armed Conflict Location and Event Data Project (Acled) ta bayyana.
Masana na ganin cewa yawan wadanda suka mutu a wannan yaki ya zarta yadda ake hasashe.
Kasashen biyu dai sun yi ikirarin cewa dubban mutane ne suka mutu a yakin, sai dai babu wata hukuma mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin.
Domin sanin hakikanin adadin mutanen da suka rasu a kowanne irin yaki, dole a yi la'akari da majijyoyi masu zaman kansu kamar Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin kasashe da kuma masu sa ido daga kasashen waje.
A ina mutane suka fi mutuwa?
Kudanci da kuma gabashin kasar Ukraine da ke kan iyakar Rasha inda a nan ne aka fara kaddamar da farmaki ta kasa na cikin wani mummunan yanayi, kamar yadda binciken kungiyar Acled da ke kididdige daidaikun kashe-kashe da suka faru sakamakon yakin, irin su musayar wuta tsakanin dakarun da ke fada da juna, da hare-hare ta sama, ya nuna.
End of Wasu labarai masu alaka
Wuraren da aka samu mace-macen
Kungiyar ta Acled ta ce fiye da mutum 10,000 ne suka mutu tun ranar 24 ga watan Fabrairu lokacin da aka soma yakin.
Birnin Mariupol da ke kudu maso gabashi, da Kharkiv, sai kuma birnin Bilohorivka da ke gabashin kasar, nan ne aka fi samun mafiya yawan wadanda suka mutu.
Fararen-hula nawa ne suka mutu?
Daga adadin da kungiyar Acled ta fitar BBC ta gano cewa kusan fararen-hula 3,600 ne suka mutu zuwa tsakiyar watan Yuni.
To amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum 4,700 ne suka mutu zuwa karshen watan Yuni.
Majalisar Dinkin Duniya na tabbatar da mutuwa ta hanyar amfani da bayanan 'yan sanda, da na asibitoci, da na wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam.
To amma bayanan da kungiyar Acled ke fitarwa sun kunshi mutanen da suka mutu sakamakon wasu al'amura na daban kamar yunwa da rashin magunguna, ba wadanda suka mutu sakamakon yakin kai-tsaye ba.
Wannan na da matukar muhimmanci a wuraren musamman ga birnin Mariupol, wanda ya shafe lokaci mai tsawo a hannun dakarun Rasha inda fararen hula da dama ke makale.
"An yi kiyasin cewa (kari a kan adadin mutuwar da aka tabbatar) akalla fararen-hula 3,000 ne suka mutu a biranen da Rasha ta kwace ko ake tafka kazamin fada, saboda rashin samun magunguna, tare da tashin hankalin da suke ciki sakamakon yakin," a cewar shugabar ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine Matilda Bogner ta bayyana.
Ta yaya ake kashe fararen hula?
Babban abin da ke janyo mutuwar fararen-hula a Ukraine shi ne hare-hare ta sama tare da luguden rokoki kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tare da binciken kungiyar Acled.
Haka kuma kungiyar Acled ta ce kusan fararen-hula 1,000 ne aka kashe a hare-haren kurkusa mafiya yawancinsu a lokacin da aka karbe iko da birnin Kyiv.
A karkashin yarjejeniyar Geneva da kuma sauran yarjejeniyoyi na duniya, kai wa fararen-hula hari ko kuma wani abu da ke da matukar muhimmanci ga more rayuwarsu, babban laifin yaki ne.
Babban mai shigar da kara na Ukrain ya zargi Rasha da aikata dubban laifukan yaki a lokacin wannan yakin, wadanda da suka hadar da kai wa fararen-hula hari kai-tsaye, zargin da Rasha ta sha musantawa.
Sojoji nawa ne suka mutu?
Bayanan adadin sojojin da suka mutu a fagen yaki abu ne na sirri, kuma zai iya sauya yadda yakin ke tafiya ga duka bangarorin da ke yakin, a cewar Gavin Crowden na kungiyar da ke tattara alkaluman asarar rayukan da aka yi a yaki.
Wannan wani batu ne da kowacce kasa za ta fi mayar da hankali a kai, in ji shi.
Ukraine dai ba ta sanar da alkaluman sojojin da aka kashe mata ba a lokacin yakin.
To amma a farkon watan Yuni wani babban hadimin shugaban Ukrain ya shaida wa BBC cewa sojojin kasar 100 zuwa 200 ne suke mutuwa kowacce rana a yankin Donbas.
A watan Afrilu, Rasha ta ce ta kashe kusan dakarun Ukraine 23,000.
To amma ita Rasha jifa-jifa takan bayyana adadin asarar dakarun da ta yi.
Adadin na baya-bayan da ta bayyana shi ne ranar 25 ga watan Maris inda ta ce sojojinta 1,351 ne suka mutu tun farkon mamayar.
A watan Afrilu gwamnatin Burtaniya ta ce kusan dakarun Rasha 15,000 ne suka mutum.
Amma kasar Ukrain na yawan fitar da adadin sojojin Rasha da ta kashe, inda ta yi ikirarin cewa dakarun Rasha 35,000 ne suka mutu zuwa karshen watan Yuni.
To sai dai kawo yanzu ba a iya tabbatar da sahihancin wannan ikirari nata ba.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce ba ta la'akari da alkaluman da kasar da ake yakin da ita ke fitarwa.
To sai dai Sashen Rasha na BBC ya tabbatar da mutuwar dakarun Rasha 4010, inda sashen ya wallafa sunayen sojojin da suka mutu tun farkon yakin.
Daga ciki dakaru 685 manyan hafsoshi ne, hudu daga ciki kuma manyan janar-janar ne, a yayin da mafiya yawa daga cikinsu kananan kafsoshi ne tare da kurata masu tarin yawa.
Sojojin wadanda aka mayar da gawarwakinsu Rasha, an gano sunayensu ne ta hanyar amfani da kafofin yada labaran kasar, da kafafen sada zumunta, tare kuma da samun bayanai daga hukumomin kasar, da yin magana da mutanen da suka sansu.
Haka kuma adadin sojojin da har yanzu gawarwakinsu ke Ukrain ba a kai ga gano suba.
"A kowacce rana yakin na haddasa hasarar rayukan gomman fararen hula tare kuma da nasojojin dake yakin", a cewar Ms Bogner.
Ta kara da cewa "hakika ran dan adam ba shi da wani muhimmanci a gare su."