Rikici ya kunno kai a PDP kan zargin ba da cin hanci

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon rikici ya dabaibaye babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya kan zargin bayar da cin hanci.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.
Wasu mambobin kwamitin gudanarwar PDP NWC ne suka mayar wa jam’iyyar naira miliyan 122.4 da aka ba suka ce an saka musu a asusun ajiyarsu na banki.
Mambobin sun yi zargin cewa sun ga shigar kuɗi ne bayan da suka fara rikici da jam’iyyar kan inda aka kai makudan kudi har biliyan 10 da aka samu wajen sayen fam ɗin zaɓukan fitar da gwani.
Sun ce naira biliyan goman ta ƙanƙance zuwa naira biliyan ɗaya a wani yanayi da ba a san yadda ya faru ba, lamarin da ya jawo tashin hankali a cikin kwamitin gudanarwar.
Mambobin NWC shida ne suka zargi shugaban jam’iyyar ta PDP Iyorchia Ayu, da bai wa mambobi cin hanci kan goyon bayan da suka ba shi a zargin da ake masa na facaka da kuɗaɗe.
A wata wasiƙa da kafafen yaɗa labaran Najeriya suka ce sun samu ganinta, wacce mambobin shida suka rubuta, sun ce an ba su kuɗaɗen ne don su biya hayar gida na shekara biyu.
Mambobin wadanda dukkansu ƴan kudancin ƙasar ne, an ce sun mayar wa jam’iyyar kuɗaɗen da aka aika musu ɗin waɗanda suka kama daga naira miliyan 28 zuwa miliyan 36.
Me PDP ta ce kan zargin?
Kwamitin amintattu na PDP NWC ya ƙaryata waɗannan zarge-zarge na aikata ba daidai ba wajen biyan jami’an alawus din kama hayar gidan.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta Debo Ologunagba, ya ce kudin ba cin hanci ba ne.
Sanarwar ta ce: “An jawo hankalin kwamitin NWC na PDP kan rahotannin da ba daidai ba da ake yaɗawa a kafafen yada labarai kan kudaden alawus na kama gida ga mambobin NWC.
“Mun gano cewa wata kafar yada labarai ce ta fara wallafa labarin cewa kudaden alawus din kama gidan da aka bai wa mambobin NWC cin hanci ne.
“Don kawar da kokonto, PDP tana so ta fada ɓaro-ɓaro cewa ba a saka kudi a asusun bankin kowane mamba da nufin ba da cin hanci ba.
“Kafin a bayar da kudaden ma, sai da aka bi tsarin da jam’iyyar ta tanada na biyan haƙƙoƙi da alawus-alawus ga ma’aikata da mambobinta,” in ji sanarwar.
Su waye suka dawo da kudin?
Zuwa yanzu dai waɗanda suka dawo da kudaden sun hada da mataimakin shugaban jam’iyya na kudancin kasar, Ambasada Taofeek Arapaja da ya mayar da naira miliyan 36.
Sai mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar kudu maso yamma Olusoji Adagunodo da ya mayar da naira miliyan 28.8.
Ita ma shugabar mata ta PDP Farfesa Stella Effah-Attoe da ta mayar da naira miliyan 28.8 da kuma shugaban yankin kudu maso kudu Cif Dan Orbih da ya mayar da naira miliyan 28.8.
A wata wasiƙa da mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu ya aika wa Ayu ranar 29 ga watan Satumba, ya ce ya yanke shawarar mayar da kuɗin da aka aika masa naira miliyan 36 ne saboda bai san me ya sa aka aika masa ba.











