Abu biyar da ya kamata ku sani kan zaɓen jihar Edo

People standing for queue to vote on election day

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar 21 ga watan Satumban 2024 ne mazauna jihar Edo za su fita domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar da zai maye gurbin Godwin Obaseki.

Hukumar zaɓe ta Najeriya (Inec) ta ce ta shirya tsaf kuma tana kira ga duk wanda ya kai shekarun da ya fito domin yin zaɓen.

A ranar Alhamis da dare aka rufe kamfe yayin da 'yantakara 18 za su fafata.

Ga wasu abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da zaɓen.

Yaushe za a buɗe rumfunan zaɓen kuma ta yaya za a kaɗa ƙuri'ar?

Inec official dey accredit voter during di 2023 general election

Asalin hoton, EPA

Za a fara kaɗa ƙuri'a da ƙarfe 8:30 na safe a faɗin jihar, amma ana sa ran ma'aikatan Inec za su isa rumfunan zaɓen kafin wannan lokaci.

Waɗanda ke da katin zaɓe ne kaɗai za su kaɗa ƙuri'ar.

Idan mai kaɗa ƙuri'a ya je rumfar zaɓe, zai nuna katinsa, sai ma'aikatan Inec su duba kuma su tantance shi a na'urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) ta ɗaukar zanen yatsunsa da kuma hoton fuskarsa.

Za a yi hakan ne domin tabbatar da cewa akwai sunanasa a rajistar zaɓen.

Daga nan sai a ba shi takardar jefa ƙuri'a, inda shi kuma zai nemi jam'iyyar da yake so kuma ya dangwala mata ƙuri'a bayan ya shiga lokon da ke kaɗa ƙuri'ar.

Za a saka masa tawada a hannu da ke nuna shaidar ya yi zaɓe.

Mutum nawa ne za su kaɗa ƙuri'a kuma a rumfuna nawa?

Jihar Edo na da ƙananan hukumomi 18 da rumfunan zaɓe 4,519.

Alƙaluman da Inec ta fitar sun nuna cewa mutum 2,629,025 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar.

Sai dai masu sharhi na cewa mutanen da za su kaɗa ƙuri'ar ba za su kai haka kamar yadda aka saba gani a sauran zaɓuka.

Yaya batun tsaro?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar ta Edo ta ce a shirye take tsaf domin ba da tsaro a zaɓen.

Mai magana da yawun rundunar, Moses J. Yamu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa aƙalla jami'ansu 35,000 ne za su yi aikin gudanar da taro a ranar.

Su wane ne 'yantakara?

Di three main candidates for di Edo govnorship election
Bayanan hoto, Manyan 'yan takara uku a zaɓen

Maza 16 ne da kuma mace ɗaya ke takarar neman kujera mafi girma a jihar.

Sai dai ana ganin uku daga cikinsu kawai ke da damar lashe zaɓen - 'yantakarar PDP, da APC, da LP.

Ga sunaye da kuma jam'iyyun 'yantakarar:

  • Iyere Kennedy – Accord Party (A)
  • Iseghohi Tom – Action Alliance (AA)
  • David Udoh Oberaifo – African Action Congress (AAC)
  • Derek Izedonmwen Osarenren– Africa Democratic Congress (ADC)
  • Kingson Akhimie Afeare – Action Democratic Party (ADP)
  • Monday Okpebholo– All Progressives Congress (APC)
  • Isaiah Osifo – All Progressives Grand Alliance (APGA)
  • Odaro Ugiagbe– Allied Peoples Movement (APM)
  • Amos Areloegbe – Action Peoples Party (APP)
  • Edeipo Osiariame – Boot Party (BP)
  • Olumide Akpata – Labour Party (LP)
  • Friday Azemhe Azena – New Nigeria Peoples Party (NNPP)
  • Asuerinme Ighodalo – Peoples Democratic Party (PDP)
  • Patience Key Ndidi – Peoples Redemption Party (PRP)
  • Abdulai Anerua Aliu – Social Democratic Party (SDP)
  • Paul Okungbowa Ovbokhan – Young Progressives Party (YPP)
  • Akhalamhe Amiemenoghena - Zenith Labour Party (ZLP)

Kazalika, masu sharhi na ganin takarar za ta fi zafi tsakanin PDP da APC.

Yaushe za a sanar da sakamako?

Matakin ƙarshe na zaɓen shi ne sanar da sakamakonsa da hukumar zaɓe za ta yi.

Baturen zaɓe na kowace mazaɓa zai tura sakamakon zuwa ga cibiyar tattara sakamako ta ƙaramar hukuma.

Sai baturen tattara sakamako ya tattara su kuma ya aika su zuwa cibiyar tattara sakamako ta jiha, inda baturen zaɓe na jiha zai karɓa.

A nan ne kuma babban baturen zaɓe na jihar zai tattara su kuma ya sanar da abin da kowace jam'iyya ta samu, kafin daga baya ya faɗi wanda ya samu ƙuri'u mafiya yawa, sannan ya faɗi wanda ya ci zaɓe.

Ɗantakara zai yi nasara ne kawai idan ya samu:

  • Ƙuri'u mafiya yawa da aka kaɗa
  • Kada su gaza kashi ɗaya cikin huɗu na ƙuri'un da aka kaɗa a cikin aƙalla biyu cikin uku na duka ƙananan hukumomin jihar

Ana sa ran yin duka wannan tun daga ranar Asabar zuwa Lahadi ko Litinin.

A zaɓen da ya gabata na 19 ga watan Satumban 2020, Inec ta sanar da sakamakon a ranar 20 ga watan - kwana ɗaya kenan bayan kaɗa ƙuri'ar.