Manyan 'yantakara uku a zaɓen gwamnan jihar Edo

'Yan takarar gwamnan jihar Edo
Lokacin karatu: Minti 3

Zaɓen gwamnan jihar Edo na ɗaya daga cikin zaɓukan gwamnan da ake yi a 2024, inda jami'yyun siyasa 18 ke kokawar karɓar ragamar mulkin jihar.

Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP na kammala wa'adin mulkinsa na biyu bayan shafe shekara takwas a matsayin gwamnan jihar.

A ranar Asabar 21 ga watan Satumban 2024 ne za a gudanar da zaɓen a faɗin jihar mai ƙananan hukukomi 18.

A zaɓen 2020 ne Gwamna Obaseki ya koma jam'iyyar PDP bayan samun saɓani da ɓangaren jam'iyyar APC da ya fara cin zaɓen wa'adin farko a ƙarƙashinta.

A zaɓen gwamnan jihar da ya gabata, Mista Obaseki ya samu nasara da ƙuri'a 307,955, yayin da babban abokin hamayyarsa na APC Osagie Ize-Iyamu ya samu 223,619.

Sai dai a wannan karon, zaɓen fafatawa ce tsakanin sabbin 'yantakara bayan wa'adin Obaseki, wanda zai ƙare ranar 11 ga watan Nuwamban 2024.

Yayin da mutum 2,629,025 suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, mai ƙananan hukumomi 18 da kuma rumfunan zaɓe 4,519, yanzu abin da kowa ke son sani shi ne wane ne zai maye gurbin Obaseki?

Kan wannan ne muka yi nazarin manyan 'yantakara uku da ke gaba-gaba a zaɓen.

Asuerinme Ighodalo na PDP

Asuerinme Ighodalo
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Asuerinme Ighodalo ne ɗan takarar jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

An haifi Ighodalo - masanin tattalin arziki, lauya kuma ɗan siyasa - cikin watan Yulin 1959 ƙauyen Okaigben da ke gundumar Ewohimi na ƙaramar hukumar Esan ta Kudu Maso Gabas da ke jihar.

Mai shekara 64, na da ƙwarewa a fannin hada-hadar hannayen jari da kamfanoni, da kuma ƙwarewa a fannin dokokin da suka shafi kasuwanci.

Asue, kamar yadda ake kiransa a jihar, tsohon shugaban bankin Sterling ne, sannan kuma ya yi aiki da kwamitin tattalin arziki ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole, da kuma gwamna mai ci Godwin Obaseki.

Cikin wata hira da BBC , Mista Ighodalo ya bayyana dalilinsa na jingine harkokin hada-hadar hannayen jari da mayar da hankali kan takarar gwamnan jihar.

Ighodalo ya samu goyon bayan gwamnan jihar, Godwin Obaseki, abin da ake ganin ya taimaka masa wajen kayar da mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu a zaɓen fitar da gwani, sai dai Mista Ighodalo ya shaida wa BBC cewa ba shi da uban gida a siyasa.

Monday Okpebholo na APC

Mista Okpebholo

Monday Okpebholo ya doke 'yantakara 11 bayan samun ƙuri'a 12,433 a zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumba.

Okpebolo ɗansiyasa ne - wanda aka haifa a ƙauyen Udomi na ƙaramar hukumar Esan da ke tsakiyar jihar a shekarar 1970, inda ya fara harkokin kasuwanci kafin ya koma siyasa.

Ɗan takarar mai shekara 53 - yanzu haka ɗan majalisar dattawa ne mai wakiltar Edo ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Okpebolo na samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar, kuma jagoran APC a jihar Adams Oshiomhole, lamarin da ya sa wasu ganin zai yi tasiri sosai a zaɓen.

Olumide Akpata na LP

Olumide Osaigbovo Akpata

A ranar Juma'a 23 ga watan Fabrairu ne Olumide Osaigbovo Akpata ya samu nasarar zama ɗantakarar jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar Edo.

Fitaccen masanin harkokin shari'a ne, daga baya kuma ya rikiɗe zuwa siyasa.

An haifi Mista Akpata a shekarar 1972, inda ya karanci fannin shari'a.

Ya zama lauya a watan Disamban 1993, inda daga baya ya kafa ofishinsa na ƙashin kai mai suna Templars.

Mai shekara 51 - wanda ya riƙe matsayin shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar (NBA) - ya ce abin da ya ja hankalinsa wajen takarar gwamnan shi ne tallafa wa al'ummar jihar.

Akwai mace cikin masu takarar?

Abin mamaki mace ɗaya ce kawai cikin jerin mutanen da ke takarar kujerar gwamnan jihar a wannan zaɓen. Ita ce Key Patience Ndidi ta jam'iyyar PRP.

Sai kuma wasu matan huɗu da ke a matsayin 'yantakarar mataimakain gwamna.

Za a yi matuƙar fafatawa a wannan zaɓe, kuma komai zai iya faruwa a zaɓen yayin da al'ummar jihar ke muradin sauya gwamnati.

Dangane da wanda zai maye gurbin Obaseki kuwa, lokaci ne kawai zai fayyace.

Ana dai sa ran samun sakamakon zaɓen a ranar Lahadi 22 ga watan Satumba daga hukumar zaɓen ƙasar.