Abin da yasa 'yan Najeriya ke tarzoma kan sauya fasalin takardun naira

Protest happun across Nigeria cities sake of di new naira notes

Tarzomar da ta ɓarke a biranen Najeriya masu yawa ta biyo bayan makonnin da 'yan ƙasar suka shafe suna fama da matsalar ƙarancin takardun Naira, lamarin da yasa jama'a suka riƙa biyan har kimanin kashi 20 cikin 100 na ainihin darajar kuɗin domin sayensu daga hannun masu sana'ar tura kuɗi, waɗanda aka fi sani da masu POS.

Fusatattun mazauna biranen Ibadan da Benin da Warri da Port Harcourt da kuma Ilorin sun riƙa ƙona tayoyi baya ga kai wa bankuna hari.

Yawancin 'yan Najeriya sun bayyana rashin jin daɗinsu yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da su a watan Nuwambar 2022 yayin taron majalisar ministoci da aka yi a Abuja.

Jama'ar ƙasar sun riƙa kokawa a shafukan sada zumunta kan sabon fasali da launin da aka saka wa sababbin takardun kuɗin. Wasunsu ma sun kai ga zana nasu sabon fasalin, suna cewa haka ya dace kuɗaɗen su kasance.

Sai dai duk wannan rashin gamsuwar da ta auku ba ta kama ƙafar rudani da ya biyo bayan abubuwan da suka faru ba yayin da aka fitar da sababbin takardun kuɗin a ranar 15 ga watan Disamba.

Ƙarancin takardun Naira

An buƙaci jama'a su kai tsofaffin takardun kuɗinsu zuwa bankuna domin a musanya musu su da kwatankwacin kuɗin amma sababbi, sai dai tun gabanin wannan lokacin babban bankin Najeriya ya yi hani ga 'yan Najeriya su riƙa cirar kuɗin da ya zarce naira 100,000 zuwa naira 500,000 a kowane mako ga kowane ɗan ƙasar ko ga kamfanoni.

Sai dai bankunan ƙasar ba su riƙa bai wa jama'a sababbin takardun kuɗin ba, a maimakon haka sai suka ci gaba da ba su tsofaffin takardun kuɗin har zuwa lokacin da bankin CBN ya umarce su da su daina yin haka.

Amma bankuna da na'urar cirar kudi wato ATM sun gaza samar da isassun kuɗin kamar yadda jama'a ke buƙata, har matsalar da ake zaton za ta wuce cikin kwanaki ta zama ta makonni.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani ƙarin lokaci da gwamnati ta yi ga ranar da ta gindaya ta 31 ga watan Janairu ma bai kawo sauƙin matsanancin karancin kuɗin ba.

Mary Temitope, wata mata mazauniyar birnin Osogbo na jihar Osun ta shaida wa BBC cewa 'yan ƙasar sun faɗa cikin wani mawuyacin hali.

"Babu yadda za a iya auna yawan wahalar da jama'a ke sha a dalilin rashin kuɗi a hannayensu. Na bi dogayen layuka a bankuna daban-daban domin yin amfani da na'urorinsu na ATM. A wasu lokutan ma har sai da na riƙa biyan wasu domin su tsaya min a layin karɓar kuɗin, kuma duk da haka ba za ka iya cirar kuɗin da ya zarce Naira 5,000 ko Naira 10,000 kawai? Tilas a kawo ƙarshen wannan shirmen," inji ta.

Wannan matakin ya tilasta wa jama'a komawa amfani da manhajojin banki domin aikawa da kuɗi, sai dai a nan ma an riƙa fuskantar matsaloli domin sabis din aikawa da kuɗin ya riƙa daukewa ko zama mai tafiyar hawainiya.

A ranar Laraba 8 ga watan Fabrairu, Kotun Ƙolin Najeriya ta bayar da umarnin wucin-gadi na ci-gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu.

Bayan wannan hukuncin na Kotun Ƙolin, 'yan Najeriya sun ci gaba da kashe tsofaffin takardun kuɗin.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya ce zuwa watan Janairu, an mayar wa babban bankin naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin takardun kudin.

Jama'a sun fusata

Fushin da jama'a ke yi ya haiffar da tarzoma a wasu birane da ke kudancin Najeriya a makon jiya yayin da ranar 10 ga watan Fabrairu ta karato. Wannan ce ranar da babban bankin Najeriya ya gindaya na daina karbar takardun naira 200 da 500 da 1,000 zuwa bankunan kasar.

A birnin Benin, mata 'yan kasuwa sun cika wasu titunan birnin suna bayyana bacin ransu kan karancin nairar, daga nan sai wasu bata-gari suka yi kokarin afka wa ginin babban bankin Najeriya amma sai 'yan sanda suka kora su da hayaki mai sa hawaye da yin harbi a sama.

Wasu hotunan bidiyo da BBC ta tantance ya nuna yadda ake kokarin dauke wani mutum da alamar harbin bindiga a cikinsa. Babu tabbacin ko ya tsira da ransa.

Tarzomar ta bazu zuwa birnin Ilorin na jihar Kwara a yankin tsakiyar Najeriya, sai dai sauran yankunan arewacin Najeriya sun kasance babu tashin hankali.

Matakin gwamnatin Najeriya: gaba ko baya?

Yayin da fargabar barkewar rikici ke karuwa, Shugaba Buhari ya yi wa 'yan kasar jawabi, inda yayi kira da a kwantar da hankula, kuma ya yi alkawarin komai zai yi sauki nan ba da jimawa ba.

Ya kuma bayar da umarnin a ci-gaba da amfani da tsofaffin takardun nairar amma na naira 200 kawai, domin a rika kashe su tare da sababbin takardun har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Sai dai wasu 'yan Najeriya na kallon matakin shugaban a matsayin bijirewa umarnin Kotun Ƙolin ƙasar, duk da cewa ya ambaci batun ana shari'a kan batun, amma bai ce komai ba game da hukuncin da ta yanke na ci-gaba da amfani da dukkan tsofaffin takardun nairar.

A halin da ake ciki, akwai wasu jihohin gwamnonin kasar da ke bin sahun takwarorinsu wajen gurfanar da gwamnatin tarayyar kasar a Kotun Ƙoli kan wannan batun. Jihar Legas ita ce ta baya-bayan nan.

Jihohin Kaduna da Kano tuni sun umarci mazauna jihohin da ma kamfanoni da 'yan kasuwa su ci-gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin, kamar yadda kotun ƙolin kasar ta umarta. Jihar Legas ma ta bi sahunsu kan wannan matakin.

Ahmed Bola Tinubu, dan takarar mukamin shugaban kasa a karkashin jam'iyya mai mulki ta APC ma ya koka, yana cewa wasu masu adawa da takararsa ne ke kitsa shirin dagula lamurra domin a kayar da shi a babban zabe mai zuwa.

Wani lauya mai suna Tobi Adebowale ya shaida wa BBC cewa sanarwar da gwaman babban bankin Najeriya da wadda shugaban kasar ke yi cewa an daina amfani da tsofaffn takardun kudin na naira 500 da 1,000 a fadin kasar ba komai ba ne illa taka umarnin kotun ƙolin ƙasar:

"Abin da ya dace shi ne a yi wa dukkan hukunce-hukuncen kotuna biyayya har zuwa lokacin da wata babbar kotun ta soke shi. Haka na faruwa a kowane mataki, inda a wannan matakin sai a jira kotun ƙolin ta sake hukuncin nata. Babu inda jawabin shugaban kasa zai iya ture hukuncin kotun ƙoli, ko da kuwa umarnin nata na wucin-gadi ne."