Firaministar Birtaniya ta sauka daga muƙaminta

Asalin hoton, Getty Images
Firaministar Birtaniya Liz Truss ta sauka daga muƙaminta bayan kwana 45 da hawa kan mulki.
Ƴan majalisa na jam'iyyar Conservatives sun buƙace ta da ta ajiye mulki bayan da gwamnatin tata ta ci karo da matsaloli.
Ajiye muƙamin nata ya zo ne bayan da wata minista mai matuƙar muhimmanci ta ajiye aiki, yayin da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka yi mata bore.
A watan Satumba ne aka zaɓi Truss a matsayin firaminista, sai dai kwarjininta ya yi ƙasa bayan soke wasu daga cikin tsare-tsaren da ta ɓullo da su.
Yanzu Liz Truss ta zamo firaminista mafi ƙarancin wa’adi a tarihin Birtaniya – wanda yake biye mata shi ne George Canning, wanda ya yi 119 kafin rasuwar sa a shekarar 1827.
Mene ne ya tursasa wa Truss ajiye muƙami??

Asalin hoton, PA Media
Gwamnatin Truss ta fara tangal-tangal ne bayan da ministan kuɗi na ƙasar, Kwasi Kwarteng ya ajiye muƙami, lokacin da ƙaramin kasafin kuɗin da ya gabatar ya rikirkita ɓangaren kuɗi na Birtaniyar.
Sai kuma batun saukar ministar cikin gida ta Birtaniya
Ms Truss ta kori Kwasi Kwarteng, sannan ta naɗa Jeremy Hunt a matsayin ministan kuɗi, wanda shi kuma ya yi watsi da ƙaramin kasafin kuɗin.
Ta kuma yi ƙoƙarin soke batun zabtare haraji a ƙoƙarinta na kwantar da hankula.
Daga nan ne aka rinƙa samun ruɗani a majalisa sanadiyyar rashin gamsuwa da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka fara nunawa.
Saukar ta a yau ta biyo bayan hargowar da aka samu a majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba.
Lokacin da ta amsa tambayoyi a zauren majalisar dokokin, Truss ta ce za ta ci gaba da fafutikar ganin lamurra sun daidaita, kuma ba za ta gudu ba, bayan da jagoran jam’iyyar Labour Sir Keir Starmer ya tambaye ta dalilin da ya sa ba ta sauka daga muƙamin ba.
Sai dai da tsakar ranar Alhamis ne Liz Truss ta jefra da ƙwallon mangwaro domin ta huta da ƙuda.










