Chelsea ta yi wa Jackson farashi, Barcelona ta mayar da hankali kan Rashford

Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea ta ƙayyade farashin fam miliyan 100 kan ɗanwasan Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 wanda yanzu haka AC Milan ke zawarcin sa. (Mail)

Ɗanwasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 ya zama wanda a yanzu Barcelona za ta fi bai wa fifiko a ƙoƙarinta na kawo ɗan wasan gaba na gefe bayan kulob ɗin na Sifaniya ya yi rashin nasara a ƙoƙarin ɗaukan ɗanwasan Liverpool Luis Diaz mai shekara 28 da Nico Williams na Athletic Bilbao mai shekara 22. (Sky Sports)

Juventus ta amince da ƙulla yarjejeniyar euro miliyan 20 da Manchester United kan ɗanwasan Ingila Jadon Sancho wanda yake tattaunawa da ƙungiyar ta Old Trafford game da kuɗin sallama kafin ya yi bankwana. (La Stampa - in Italian)

Tottenham na ci gaba da zawarcin ɗanwasan Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo Yoane Wissa duk da rashin tuntuɓar Brentford bayan samun labarin yi wa ɗanwasan farashin fam miliyan 50 a farkon wannan bazarar. (Standard)

PSV Eindhoven ta shirya cefanar da ɗanwasan Belgium Johan Bakayoko mai shekara 22 yayin da Everton da Nottingham Forest da Bournemouth har ma da RB Leipzig da Bayer Leverkusen suke zawarcinsa. (Fabrizio Romano)

Nottingham Forest na duba yiwuwar ƙara wani abu kan tayin da ta yi da zai kai fam miliyan 25 kan ɗanwasan Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 James McAtee sai dai Manchester City ta yi wa mai shekara 22 ɗin farashin kusan fam miliyan 40. (Mail)

Atalanta na son tayin aƙalla fam miliyan 50 kafin ta duba yiwuwar cefanar da ɗanwasanta ɗan asalin Italiya Giorgio Scalvini wanda Newcastle United da Manchester United ke zawarci. (i paper)

Aston Villa na dab da kammala ƙulla yarjejeniyar sayen golan Netherlands mai shekara 34 Marco Bizot daga Brest da ke Faransa. (Athletic - subscription required)

Arsenal na ci gaba da zawarcin ɗanwasan Real Madrid Rodrygo mai shekara 24 duk da cewa suna dab da cimma yarjejeniyar ɗaukan ɗanwasan Chelsea Noni Madueke mai shekara 23. (GiveMeSport)

Ɗanwasan Colombia Daniel Munoz mai shekara 29 na fatan yin bankwana da Crystal Palace a wannan bazarar duk da cewa a watan Afrilu ya sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar. (Mirror)

Fenerbahce da ke Turkiyya ta kusa ƙulla yarjejeniyar sayen ɗanwasan Sifaniya Marco Asensio mai shekara 29 daga Paris St-Germain. (Football Italia)