'Sai na ji na zama kamar wata shaiɗaniya saboda ba na son haihuwa'

Caroline Mitchell mai shekara 46 ta daɗe da sanin cewa ba ta son haihuwar yara

Asalin hoton, Caroline Mitchell

Bayanan hoto, Caroline Mitchell mai shekara 46 ta daɗe da sanin cewa ba ta son haihuwar yara
    • Marubuci, Sammy Jenkins
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, West of England

Ana samun ƙaruwar yawan matan da ba su son haihuwa kuma ƙarancin haihuwar a duniya na ƙaruwa.

Yayin da suke ba da dalilai daban-daban kamar sauyin yanayi da na tattalin arziki da lafiya, waɗanda ke ƙaurace wa haihuwar kan ce har yanzu al'umma ba su gama gane manufarsu ba, inda suke jin babu daɗi a lokuta da dama.

BBC ta tattauna da mambobnin wata ƙungiya mai suna Bristol Childfree Women, inda take da mambobi fiye da 500 wadda kuma mata suka kafa domin matan da suka yanke shawarar zama babu haihuwa.

Yayin da Caroline Mitchell ta ƙudurce a ranta cewa ba ta son haihuwar yara, ba ta taɓa tunanin irin wahalar da ke tattare da kaiwa shekarun haihuwar ba.

'Yar shekara 46 da ke zaune da mijinta a Brislington da ke birnin Bristol, ta ce duk da cewa bai taɓa damun ta ba a loakcin da take ƙarama, ba ta taɓa tunanin fuskantar irin tambayoyin da mutane ke yi mata ba lokacin da ƙawaye da 'yan'uwanta suka fara haihuwa.

"Na ji kamar na zama wata shaiɗaniya saboda aƙidata," a cewarta.

"Na ji cewa tunanina da fahimtata ba za su karɓu ba."

Caroline na ganin cewa an gina al'umma ne a kan haihuwa.

"Abu ne mai wuya duk lokacin da na haɗu da mutane saboda kusan duka maganar dai ita ce ta matan da za ku haɗu a bakin ƙofar makaranta ko kuma a majalisar mata ta marubuta."

Caroline ta ce tana tunanin wani lokacin mata masu 'ya'ya kan ce "an tsara duniya ne" saboda matan da ba su son haihuwa su ji daɗi.

"Tabbas za ki ji kamar babu ke ake rayuwa," in ji ta.

Yayion da Caroline take da tabbas 100 bisa 100 game da aniyarta, ta amince cewa wasu lokutan takan ji "haushin" aƙidar tata.

Megan Stanley

Asalin hoton, Megan Stanley

Bayanan hoto, Megan Stanley ta ce ta ƙagu ta kai lokacin daina yin jinin-al'ada

Alƙaluman da aka fitar a 2022 sun nuna cewa matan da ke kaiwa shekara 30 ba tare da son haihuwa ba na ƙaruwa.

Sama da rabi (kashi 50.1 cikin 100) na matanIngila da Wales da aka haifa a shekarun 1990 ba su haihu ba lokacin da suka kai shekara 30 a 2020, wanda su ne ƙarni na farko da suka yi hakan, a cewar ofishin ƙididdiga na ƙasa a Birtaniya.

Megan Stanley 'yar asalin Oxfordshire kuma mazauniyar Bristol, ta san cewa tabbas ba ta son haihuwa kuma ta dinga neman a fiɗiye ta tun tana shekara 19.

Game da ciwon mara lokacin jinin al'adarta, Megan ta ce "azaba ce" mace ta dinga shiga "irin wannan ciwon duk wata", abin da ta ce ba ta buƙata.

"Sai likitoci su ce mani 'har yanzu matashiya ce ni' ko kuma 'za ki sauya shawara ne'," a cewarta.

Megan da abokin zamanta Ashley sun yarda cewa ba za su haifi 'ya'ya ba

Asalin hoton, Megan Stanley

Bayanan hoto, Megan da abokin zamanta Ashley sun yarda cewa ba za su haifi 'ya'ya ba

Abu mafi girma da ta Megan ta taɓa yi shi ne lokacin da ta nemi ganin likita tana shekara 29.

"Na shirya komai - bayanan lafiyata, da duka tunanina. Har ma na je na karɓo bayanai daga wani mai ba da shawarwari da nake gani. Na shirya tsaf," in ji ta.

Sai dai kuma, ba a samu damar yin hakan ba lokacin da likitan ya nemi sanin bayani game da aurenta.

Ta faɗa wa likitan cewa abokin zamanta ma ba shi so haihuwa kuma ma har an yi masa tiyatar hana haihuwa.

'Jikina ne'

Megan ta ce likitan ya faɗa mata idan an yi wa abokin zamanki tiyata b a sai an yi mata ba ita ma.

Daga nan ne Megan ta ce ta tabbatar "ba za iya guje wa lamarin ba" kuma ba za su yi ba.

"Me ya sa zan jingina abin da zan yi wa jikina da abin da ya yi wa nasa jikin?" a cewarta.

"Yanzu har na fara zaƙuwa lokacin daina jinin-al'ada ya zo. Abin da nake jira kenan."

Caroline ta ce abu ne mai wuya ta kauce wa abin da al'umma suka saba da shi

Asalin hoton, Caroline Mitchell

Bayanan hoto, Caroline ta ce abu ne mai wuya ta kauce wa abin da al'umma suka saba da shi

Caroline na ganin matan da ba su son haihuwa "za su iya taimakawa" wajen cigaba da raya al'adu a yadda suke.

"Ba mu iya magana a kan lamarin - saboda haka ne kowa ke ganin kawai ya kamata a yi abin da kowa da kowa ke yi," a cewarta.

Fiona Powley

Asalin hoton, Fiona Powley

Bayanan hoto, Fiona Powley ta kama shugabancin ƙungiyar Bristol Childfree Women shekara 12 da suka wuce

Fiona Powley ta ce tun tana shekara 12 ta ji ba ta son zama uwa a rayuwarta bayan ta ga yadda mahaifiyarta ta dinga fama da raino.

"Kawai na yi tunanin cewa zama uwa ba abu ne mai sauƙi ba," ta ce.

Matar mai shekara 49 yanzu, tana jagorantar ƙungiyar Bristol Childfree Women a daidai lokacin da take fuskantar alamun daina jinin-al'ada, amma kuma ba ta jin wata fargaba ko da-na-sani.

"Ni babu wani abu da nake ji," in ji ta.

'Son-kai'

Sai dai kamar Caroline da Megan, Fiona ta ce ta san mutanen da za ta haɗu da su za su nuna rashin jin daɗinsu idan ta faɗa musu aniyarta.

"Za a yi ta ce maki za ki yi da-na-sani. Mene ne amfanin rayuwarki? Idan ba ki da 'ya'ya ke ba cikakkiyar mace ba ce," a cewar Fiona.

An taɓa siffanta Fiona da mai "son kanta", wasu ma sun tambaye ta wane ne zai kula da ita idan ta tsufa.

"Babu mamaki don ba su taɓa tunanin cewa suna da zaɓi ba ne."

Caroline Mitchell

Asalin hoton, Caroline Mitchell

Bayanan hoto, Caroline ta ce akwai 'rikita-rikita' mai yawa game da rashin son haihuwa

Megan ta yi iƙirarin cewa mutane sun yi mata kallon "maƙiyiyar yara, ko kuma muguwa" saboda hakan.

Fiona ta ce akwai dalilai masu yawa da ya sa mutane ba su son yara.

'Magana ce ta zaɓi'

Caroline ta ce za ta iya zama "uwa mai gardama", tana mai cewa akwai "rikita-rikita mai yawa" game da rashin son haihuwa, kamar mayar da hankali kan ƙaunar da take yi wa mijinta da kuma sauran abubuwan da ta fi so.

Megan na ganin hakan ita ma.

"Akwai farin ciki game rashin son yara," in ji ta.

"Ba wai maganar 'yanci ba ce kawai ko kuma kuɗi, magana ce ta zaɓi."