Barcelona ta sayi Olmo daga RB Leipzig

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta kammala ɗan wasan tsakiyar Spaniya Dani Olmo daga RB Leipzig ta Jamus.
Dan shekara 26 ya koma Barcelona ne kan kuɗi fan miliyan 51, kuma ya buga wa tawagar matasan Spaniya wasa kafin daga bisani ya koma Dino Zagreb ta Croatia a 2014.
Olmo ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara shida da Barcelona.
Yana cikin jerin waɗanda suka fi cin kwallo a Euro 2024 inda ya ci kwallo uku kuma ya taimakawa Spain ta lashe gasar karo na hudu a jere.
"Duk lokacin da yake taka leda sai ya zama ya fita zakka cikin abokan kwallonsa, ga shi yana da kwazo idan yana kwallo tsakanin abokansa," kamar yadda sanarwar Barcelona ta zayyana.
"Yana da nasarar cin kwallo kamar yadda ya nuna kansa a Euro 2024, kuma yana iya cin kwallo daga ciki ko kuma wajen yaji na 18."
Olmo ya ci kofin Jamus biyu tare da RB Leipzig a 2020.
"Kulub ɗin matasa ne. Kuma za mu girma tare mu ci kwallaye tare da kofina mu kafa tarihi tare," Olmo ya rubuta a shafinsa na X.
"Ina godiya RB Leipzig, har abada kuna raina."











