Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake cin zarafin ƙananan yara a mahaƙar ma'adinai a Afirka ta Kudu
- Marubuci, Mayeni Jones
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg
- Lokacin karatu: Minti 5
Labarin na ƙunshe da bayanai, har da bidiyo, da ka iya tayar da hankalin wasu.
Abu mafi kaɗuwa ga Jonathan, wanda ya jurewa tsananin wahala tsawon wata shida yana zama da kuma aiki a wata mahaƙar zinare a Afirka ta Kudu da aka daɗe ba a aiki cikinta, shi ne cin zarafin da ya gani da idonsa ana yi wa ƙananan yara.
Ana ɗaukar wasu su yi aiki, wasu kuma ana kai su wajen saboda dalili guda - a yi amfani da su, in ji masu fafutika.
Jonathan, mai shekara 20, ya yi ƙaura zuwa Afirka ta Kudu bisa alƙawarin samun kuɗi ta dalilin haƙar zinare a ɗaya daga cikin mahaƙa da ta daina aiki, da aka rufe saboda rashin riba.
Mun kare bayanansa sabda fargabar martani daga ƙungiyoyin gungun masu laifuka da ke gudanar da wuraren da ake haƙar ma'adinan ba bisa ƙa'ida ba, kan magana da kafafen yaɗa labarai.
Cikin sanyin murya, ya bayyana zafin ranar da ya fuskanta, da lokuta masu tsawo da yake shafewa ba tare da cin abinci ko samun isasshen bacci ba, wani abu da ya yi tasiri a jikinsa.
Ya kuma bayyana irin halin da matasa masu ƙananan shekaru ke shiga a wuraren hakar zinare da suke aiki.
"Nakan ga waɗanan yaran a mahaƙar - matasa ƴan shekara 15 zuwa 17.
"Wasu kan yi amfani da su a wasu lokuta. Abin akwai fargaba, kuma ban gamsu da halin da na tsinci kaina a ciki ba."
Ya ce manya cikin masu haƙar zinaren kan yi musu fyaɗe, inda suke yi musu alƙawarin ba su zinare idan suka amince da su.
"Idan aka samu yaro mai tsananin son kuɗi, shikenan sai ya yarda."
Jonathan ya bayayna yadda yara ke tunkarar tawagar masu haƙar zinare domin neman kariya, ''amma sai tawagar ta ce tana da sharaɗi''.
Haka kuma manyan kan yi amfani da fyaɗe a matsayin hanyar ladabtarwa idan yaro ya kasa aiwatar da aikin da suka sanya shi.
Jonathan ya ce duka yaran da ke aiki a mahaƙar da yake ƴan ƙasashen waje ne, kuma ba su san hatsarin da suke jefa kansu ba.
Makhotla Sefuli wani mai bincike kan haƙar zinare kuma ɗan gwagwarmaya ya goyi bayan wannan furuci.
Ya ce gungun masu laifi kan ɗauki ƙananan yara domin aikin haƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba a Afirka ta Kudu.
Da yawa daga cikinsu ana kama su ne daga maƙwabtan ƙasashe sannan a yi safararsu zuwa ƙasar, ana yaudararsu da samar musu ayyuka a fannin ma'adinan ƙasar.
"Da zarar sun shiga ƙasar, sai a ƙwace musu ''passport'' ɗin su... abu ne da kowa ya sani ana cin zarafin yaran,'' a cewar Mista Sefuli says.
BBC ta zanta da masu haƙar ma'adinan waɗanda suka yi aiki a aƙalla wurare biyu na haƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba, inda kuma suka tabbatar da cewa sun ga yadda ake cin zarafin ƙananan yaran da ke aiki a wuraren.
Tshepo, wanda ba sunansa na gaskiya ba, ya ce ya ga yadda manyan mutane ke tilasta wa ƙananan yara (Maza) saduwa da su cikin ramukan haƙar ma'adinan.
"A wasu lokutan suna yaudararsu da kuɗi. Wasu kuma a kan hakan ma ake ɗaukarsu aiki, saboda kuɗin da za su samu a saduwar da za a yi da su cikin ramukan''.
Ya ƙara da cewa cin zarafin ya matuƙar shafar yaran.
"Sun zauya musu ɗabi'u da halaye kuma a yanzu ba sa yarda da kowa. Ba sa son kowa ya raɓe su, saboda suna ganin kowa ba abin yarda ba ne.''
Bayanan cin zarafin sun fito fili ne a shekarar da ta gabata lokacin wata arangama tsakanin ƴansandan Afirka ta Kudu da dubban masu haƙar ma'adinan ba bisa ƙa'ida ba.
Abubuwan da suka faru a mahaƙar zinare ta Buffelsfontein da ke kusa garin Stilfontein da ke lardin Arewa maso Yamma, sun ja hankalin duniya a lokacin da labarin samamen jami'an tsaro a wurin a bayyana.
Hukumomi na ƙoƙarin kakkaɓe ayyukan masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, wanda gwamnati ta ce ya janyo wa ƙasar asarar dala biliyan 3.2 a shekarar da ta gabata.
A watan Disamban 2023, ne ƴansanda suka ƙaddamar da samamen da suka kira da 'Vala Umgodi' ma'ana rufe ƙofa, inda ta alƙawarta ɗaukar tsauraran matakai kan gungun masu laifin.
A wani ɓangare na samamen, ƴansanda sun taƙaita yawan abinci da ruwan sha da ake kai wa mahaƙar ma'adinai ta Stilfontein kamar yadda ɗaya daga cikin ministocin ƙasar ya bayyana hakan da, "kawar da" masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.
Jami'ai sun ce mutanen da ake zargi da laifukan sun ƙi fitowa daga ramukan saboda fargabar kamasu.
Daga nan ne bidiyoyi suka fara ɓulla daga mahaƙar da ke nuna gomman mutane a rame da wasu gawarwaki suna kiran a kuɓutar da su.
Nan take kuma kotu ta umarci hukumomi su kuɓutar da su.
Daga cikin wadanda aka ceto da dama masu ƙananan shekaru ne, amma da yawansu ƴancirani ne marasa cikakkun takardu ta yadda ba za aiya gano shekarunsu ba.
Hukumomi sun gudanar da gwaje-gwaje a kansu domin ƙiyasin shekarunsu.
Daga baya hukumomi sun tabbatar da cewa 31 cikin wadanda aka kuɓutar a mahaƙar Stilfontein ƙananan yara ne, kuma dukansu ƴan ƙasar Mozambique ne, yayain da aka mayar da 27 daga cikinsu gida a watan Nuwamban da ya gabata.
Ƙungiyar Agaji ta Save the Children ta Afirka ta Kudu ta taimaka wajen fassara hirar da aka yi da wasu daga cikin masu ceton.
"Sun shiga cikin tsanancin tsoro, saboda a gaban wasunsu ake yi wa wasu fyaɗe,'' in ji shugabar ƙungiyar, Gugu Xaba.
"Saboda fargabar ba za su kuɓuta ba, tunanin ƙananan yaran ya taɓu''.
"Manyan kan fara ne da ƙaraffa musu gwiwa, ta yadda za su riƙa yin aiki kamar su.''
Ya ce daga nan sai a fara yi wa yaran fyaɗe a kowace rana har su saba sa jima'i.
"Za ka samu mutum guda na yara uku zuwa hudu da yake aikata irin wannan masha'ar da su," in ji ta.
Misis Xaba ya ce gungun masu haƙar ma'adinan kan ɗauki yaran aiki saboda sauƙin jan ra'ayinsu da kuɗaɗe ƙalilan.
"Ƙananan yaran ba sa ganewa idan ka ce musu: ''Zan ba ka rand 20 (dala guda) a kowace rana''.
A wasu lokutan manyan suka daina aikin, inda za su tilasta wa yaan ci gaba da aikin. saboda sukan tilasta yaran cikin sauƙi su yi aikin, don haka suke ɗauko yaran marasa galihu domin gudanar da aikin.
Baya ga cutar da su don samun kuɗi, Misis xaba ta ce akwai wasu gungun mutanen da ke ɗaukar ƙananan yaran kaɗai saboda da saduwa da su.
Da dama cikin masu haƙar ma'adinai kan shafe watanni a ƙarƙashin ƙasa, inda kasuwanci ke bunƙasa a wurin yayin da ake ƙoƙarin kai musu abin da suke buƙata.
"Da dama cikin ƙananan yaran ana safararsu domin yin jima'i da su. Kuma suna samun inda za su kashe kuɗin, don haka ne akwa amfani da yaran a kowace rana.''
BBC ta tuntuɓi ƴansanda da DSD mai kula da rayuwar ƴanƙasar, ko akwai wanda aka gurfanar kan zargi cin zarafin yaran ta hanyar lalata.
To amma ba su amsa tambayarmu ba.
Wata majiya da ke aiki a mahaƙar Stilfontein ta ce da yawa cikin yaran ba sa son bayayana halin da suka shiga.
Yanzu haka dai sana'ar haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na ci gaba a Afriak ta Kudu.
Yayin da ake da ƙiyasin guraben aiki 6000 a ɓangaren, akwai yiwuwar ba za a kai ƙarshen haramtacciyar sana'ar nan kusa ba, lamarin da ya sa dubban yara marasa galihu ke cikin hatsari.