Semenyo ya fi son Liverpool kan Man U da City, Chelsea za ta sayar da Jackson

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan mai kai hari na kasar Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, ya fi son ya koma Liverpool a maimakon Manchester City ko Manchester United idan ya yanke shawarar barin Bournemouth a watan Janairu.(Guardian)

Bayern Munich ta shirya yi wa Manchester United tayin kusan Yuro miliyan 50 kan dan wasan tsakiya na Portugal kuma kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes,mai shekara 31. (Fichajes)

Chelsea ta fara neman kungiyoyin da za ta sayar wa dan wasan kasar Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 yayin da ba zai ci gaba da zaman aro a Bayern Munich ba idan wa'adin zamansa ya zo karshe . (CaughtOffside)

Filip Jorgensen na son ya bar Chelsea saboda takaicin kasancewa mai tsaron gida na biyu, duk da cewa sai da amincewar kungiyarsa dan wasan Denmark mai shekara 23 zai iya barin kungiyar kuma a shekarar 2031 ne wa'adin kwantaraginsa zai so karshe. (Teamtalk)

An sanar da Liverpool cewa watakila dan wasan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26, ya koma Anfield a 2026. (Teamtalk)

Sai dai, Barcelona na sha'awar Bastoni, da kuma dan wasan Manchester City da Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 23. (Mundo Deportivo )

Aston Villa na bibiyar golan Barcelona da Jamus Andre ter Stegen, mai shekara 33, wanda ke son a rika ba shi damar buga wasa akai -akai gabanin gasar cin kofin duniya da za a yi a badi . (Mundo Deportivo )

Dan wasa mai kai hari na Athletic Club da Sifaniya Nico Williams, mai shekara 23, wanda ya ɗau hankalin Liverpool da Arsenal da kuma Chelsea, na son ya koma Real Madrid. (Football Transfers)

Arsenal ta tuntubi wakilan dan wasan tsakiya na Lille, Ayyoub Bouaddi wanda take son ta siya kan Yuro miliyan 45 a watan Janairu, duk da cewa Manchester City, da Manchester United da Liverpool suna zawarcin dan kasar Faransa mai shekaru 18.(Mirror)

Everton na zawarcin dan wasan Leeds United Jayden Bogle, mai shekara 25, kuma wakilanta sun gamsu da yadda ya rika tamaula a gasar Firimiya ta wannan kaka. (Football Insider)

AC Milan na son a ba ta aron dan wasan Arsenal mai kai hari Gabriel Jesus, mai shekara 28, yayin da dan wasan kasar Brazil bai cika samun mintunan farko a wasanin tawagar kungiyarsa ba. (Gianluigi Longari)