Lesotho na son ƙwato filayenta daga daga Afirka ta Kudu

Asalin hoton, AFP
Ana sa ran majalisar dokokin Lesotho za ta yi muhawara a ranar Laraba domin tattaunawa kan wani kuduri da zai bai wa ƙasar damar sake ƙwato filayenta a wasu sassan Afirka ta Kudu.
Wani ɗan majalisa na ɓangaren adawa na son ƴan majalisa su ayyana ɗaukacin yankin Free State da ɓangaren arewa da gabashi da Mpumalanga da kuma na KwaZulu-Natal a matsayin yankin Lesotho.
Wani daftari na majalisar ya ce za su yi haka ne karkashin wata shawara da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar a 1817 wanda kuma babban zauren majalisar ya zartas a watan Disamban 1962.
A tarihi dai, ana samun mutanen Lesotho a yankunan Free State da gabashi da arewaci da Mpumalanga da kuma wasu ɓangarorin KwaZulu-Natal.
An tilasta musu yin hjira zuwa ƙasar Lesotho ta yanzu saboda yaƙe-yaƙe da aka yi ta gwaɓzawa a wancan lokaci.






