‘Abin da ya sa muka bijire wa Taliban kan zuwa Olympics’

- Marubuci, Firuz Rahimi and Peter Ball
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service in Aigle, Switzerland
Fariba Hashimi ta tashi daga sirdin kekenta na fam 15,000 a kan wata hanya da ke cikin tsaunukan alps da ke Switzerland, kuma ta dage kan tukin da ta ke yi wa keken domin ta rage tazarar da ke tsakaninta da ƴar uwarta, Yulduz, da ke wasu ƴan mitoci a gabanta.
Tseren atisaye irin wannan ne mataki na ƙarshe a tafiyar da ƴa’ uwan biyu suka fara daga yankunan karkarar Afganistan, suna fafatawa a kan kekunan aro, kafin su tsere lokacin da ƴan Taliban za su hau mulki.
Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gasar Olympics a birnin Paris. Kuma, duk da hukuncin da Taliban ta yanke na haramta wa mata wasanni, za su fafata a ƙarƙashin tutar ƙasarsu.
Babban ƙalubale

Yayin da mafi yawan da manyan ƴan wasa ke fara motsa jiki kusan da zarar sun fara iya tafiya, Fariba, mai shekara 21, da Yulduz, mai shekara 24, sun ɗan makara wurin fara tseren keke.
Sun taso ne a yankin Faryab, ɗaya daga cikin lardunan yankin karkara da ke ƙarƙashin ikon masu ra'ayin mazan jiya a Afganistan, inda ko tunanin ganin mata a kan keke ba a yi.
Fariba tana da shekaru 14 ita kuma Yulduz na da shekara 17 lokacin da suka ga tallar wata gasar tseren keke kuma suka yanke shawarar shiga.
Akwai matsaloli guda biyu; ba su da kekuna kuma ba su ma iya tuƙawa ba.
Wata rana ƴan‘uwan sun karɓo aron keke a wurin maƙwabcinsu. Bayan ƴan sa'o'i kaɗan, sai suka ji sun sami ƙwarewa.
Ƙalubale na gaba da suka fuskanta shi ne yadda za su guje wa kar danginsu su gano abin da suke yi saboda irin tsangwamar da ake yi wa mata da ke shiga wasanni a yankunan da ke ƙarƙashin ikon masu ra'ayin mazan jiya a Afghanistan.
Ƴan’uwan sun yi amfani da sunaye na ƙarya, suka kuma yi shiga ta batar da kamanni inda suka sanya manyan riguna, da manyan lulluɓi, da tabarau don kada mutane su gane su.
Da ranar tseren ta zo, abin mamaki ƴan’uwan sun zo na ɗaya da na biyu.
Fariba ta ce, "Abin mamaki ne." "Na ji ni kamar tsuntsuwar da za ta iya tashi."

Sun ci gaba da shiga tseren kuma suka ci gaba da samun nasarori har sai da iyayensu suka gano lokacin da suka ga hotunan su a kafafen yaɗa labarai na cikin gida.
Fariba ta ce "Da farko ransu ya ɓaci, sun ce in daina tseren keke." "Amma ban karaya ba, a asirce na ci gaba," ta ce yayin da ta ke murmushi.
Amma dai lamarin ya zo tattare da haɗurra - mutane sun yi ƙoƙari su buge su da motoci ko amalanke yayin da suke kan keke ko kuma akan jefe su yayin da suke wucewa.
"Mutane sun kasance masu zagin mu. Amma ni abin da nake so in yi shi ne lashe tsere," in ji Yulduz.
Kuma lamarin ya kusa ƙara muni.
Tserewa daga gidansu
A shekara ta 2021, shekaru huɗu bayan da ƴan‘uwan suka fara tseren keke, Taliban suka mamaye ƙasar tare da tauye hakkin mata, inda aka hana su damar samun ilimi tare da takaita yadda za su yi balaguro. Sun kuma haramta wa mata shiga harkar wasanni.
Yulduz da Fariba suna da burin wata rana su fafata a gasar Olympics. Yanzu sun san idan suna son yin tseren keke dole ne su bar Afghanistan.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta dallilin mutanen da suka sani a harkar tseren keke sun sami nasarar samun kujeru a cikin jirgin jigilar mutanen Italiya, tare da abokan wasansu uku.
Da suka isa Italiya, matan sun shiga ƙungiyar masu tseren keke kuma sun samu horon da ya dace a karon farko.
"A baya a Afghanistan, ba mu samu horaswar ƙwararru ba," in ji Yulduz. "Abin da muka saba yi shi ne ɗaukar kekuna mu hau."
Amma barin ƙasarsu da danginsu ba abu ne mai sauƙi ba.
Fariba ta ce "Babban abu a gare ni shi ne na rabuwa da mahaifiyata." "Ban taɓa tunanin cewa saboda hawan keke za a raba ni da ƴan‘uwana maza da mata ba."
"Na sadaukar da abubuwa da yawa."
Karɓe ikon da Taliban ta yi a Afganistan ya jefa shakku kan ko ƙasar ma za ta iya shiga gasar Olympics.
Ya kamata kwamitocin wasannin Olympic na ƙasa su zabi ƴan wasa a gasar ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.
Yayin da haramcin da Taliban ta yi wa mata ya karya wannan doka, ta hanyar hana zaɓar mata a cikin tawagar wasannin Afghanistan, hakan ya sa an yi kira da a haramta wa ƙasar shiga gasar ta Olympics - kamar yadda aka yi a lokacin da ƙungiyar ta yi mulki a baya.
Amma hukumar wasannin Olympics ta duniya ta so nemo hanyar da za ta bai wa matan Afghanistan damar shiga gasar.
An yi tattaunawar bayan fage tsakanin shugabannin ƙungiyoyin wasanni na Afghanistan, ciki har da wasu da ke gudun hijira, game da haɗa tawaga ta musamman da za ta wakilci ƙasar a birnin Paris.
Sun kama hanyar zuwa Paris
Yayin da lokaci ya fara kurewa, kuma gasar Paris 2024 ke ƙara ƙaratowa, da alama babu ƴan wasan Afghanistan da za su halarci gasar.
A cikin watan Yuni, hukumar gasar Olympics ta duniya ta sanar da cewa, ta shirya wata tawaga ta musamman mai daidaiton jinsi da za ta wakilci Afghanistan a gasar ta Olympics ta Paris. Za ta kasance kunshe da mata uku da maza uku. Kuma ƴan‘uwan biyu na cikin su.
Fariba ta ce: "Wannan babban abin mamaki ne gare mu.''
Yulduz ta ƙara da cewa "Mun daɗe munada burin shiga gasar Olympics, wannan ya tabbatar da cikar burinmu."
"Duk da ƴancin da aka daƙile mana, za mu iya nuna cewa za mu iya samun gagarumar nasara, za mu iya wakiltar matan Afghanistan miliyan 20."

IOC ta ce babu wani jami'in Taliban da za a ba shi izinin halartar gasar Paris 2024.
Shirye-Shiryen ƙarshe
Ƴan mata suna shirye-shiryen gasar tseren keken Olympics yayin da suke tare da ƙungiyar ci gaba da UCI ke gudanarwa da ke kuma samun tallafi a Cibiyar tseren Kekuna ta Duniya, a wani wurin atisaye na zamani a garin Aigle na Switzerland.
Ƙasaitaccen wurin atisayen ya matuƙar bambanta daga hanyoyi masu ƙura na Afghanistan inda Yulduz da Fariba suka fara koya wa kansu hawa keke.
Amma gwiwarsu ba taɓa karyewa ba.
Yulduz ta ce "Mu ke bai wa juna ƙwarin gwiwa - ina goyon bayanta kuma ita ma tana mara min baya."
Fariba ta ƙara da cewa "Nasarar da muka samu ta Afganistan ce." “Wannan ta matan Afghanistan ce. Saboda su zan je gasar Olympics."











