Yadda kunya ke hana mata neman hutu a lokacin jinin al'ada

Asalin hoton, Getty Images
Sifaniya ta zama ƙasar Turai ta farko da ta ɓullo da hutu ga matan da ke shan wahala a lokacin jinin al'ada.
Dokar wadda ta samu rinjayen ƙuri'a 185 a majalisar dokokin ƙasar, za ta kawar da ƙyama da ake yi wa masu jinin al'ada a ƙasar, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.
"Rana ce ta tarihi game da masu rajhin kare haƙƙin mata," kamar yadda ministar daidaito Irene Monterota wallafa a shafinta na Tuwita, wadda ta ce matakin wani yunƙuri ne na magance matsalolin da suka daɗ suna ci wa mata tuwo a ƙwarya.
Dokar ta tanadi cewa ma'aikatan da ke fuskantar tsananin ciwo a lokacin jinin al'ada za su samu hutu tsawon kwanakin da suka ɗauka suna al'adar, to amma hutu game da sauran lalurorin da suka shafi lafiya na buƙatar sahalewar likita, kuma doka ba ta tanadi tsawon lokacin hutun ba.
Ƙasashen ƙalilan ne - a faɗin duniya suka yi dokokin samar da hutu ga mata ma'aikata a lokacin jinin al'ada - waɗanda suka haɗa da Japan da Taiwan da Indonesiya da koriya ta Kudu da kuma Zambiya.
An fara yin doka ta farko kan jinin al'ada ne a tarayyar Soviet a shekarar 1922.
Masu goyon bayan dokar sun ce tana da matuƙar muhimmanci kamar na hutun haihuwa.
To sai dai masu suka na ganin dokar za ta haifar da rashin ɗaukar mata aiki a wasu kamfanonin.
Shirin mata 100 na BBC ya tattauna da mata a wasu ƙasashen da suka tanadi hutu ga mata masu jinin al'ada, cikin watan Mayu a lokacin da ƙasar Sifaniya da gabatar da ƙudurin dokar domin gano yadda dokar ke aki.

Asalin hoton, Getty Images
'Maza abokan aikina sun yi ta suka ta'
Irine Wardhanie wata 'yar jarida a gidan talbijin na Indonesiya ta ce ta sha wahalar sosai a kan jinin al'ada tun lokacin da take makaranta. A yanzu tana samun hutun kwana biyu a kowanne wata daga inda take aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Kafin jinin ya zo min, nakan samu kaina cikin matsanancin ciwon mara. Nakan ji tsananin gajiya da ciwon kai, idan al'adar ta fara nakan ji ciwon gaɓoɓi, nakan ji tashin zuciya tare da zazzaɓi. Nakan shafe kana biyu zuwa uku ina jin wannan yanayi,'' in ji Ms Wardhanie.
"Ya za a yi ace sai ka tambayi namiji kafin ka tafi hutun don jinin al'ada'', in ji ta.
"Da fari nakan damu kan yadda mutane za su kalleni, dan haka nake tura saƙon imel ga manajojina domin sanar da su idan lokacin ya yi, kuma suka bani haɗin-kai," kamar yadda ta bayyana.
"Abu ne mai sauƙi a inda nake aiki, abin da nake buƙata kawai shi ne na tura wa na gaba da ni saƙon email, sai kuma na sanar da mai tsara ayyukan ma'aikata.
"Wasu ƴan ƙalilan a cikin abokan aikina maza su ne kaɗai suke suka ta kan lamarin."
Ba kamar Irine ba, mata da yawa a Indonesia ba su da zaman dokar da ta ba su damar ɗaukar hutun kwana biyu ba a lokacin da suke yin jinin al'ada."
"Na tattauna da wasu mata da ke aiki a kafafen yaɗa labaru a Indonesia waɗanda ba su san da dokar ba, saboda haka sukan tursasa kansu su yi aiki duk da cewa suna fama da ciwon mara a lokacin al'ada."

Asalin hoton, Getty Images
Wajibi ne ga ma'aikatu su bai wa mata hutun kwana 24 na al'ada a kowace shekara, to amma ba a cika aiwatar da dokar ba.
"Wasu ma'aikatun da dama kan bayar da hutun kwana ɗaya, wasu kuma ba su bayar da ko ɗaya" kamar yadda Hukumar kula da ƙwadago ta duniya ta ruwaito.
Vivi Widyawati na cikin masu ƙoƙarin ƙwato wa mata ƴanci, kuma tana aiki a ɓangaren masaƙu na ƙasar, ta ce akwai matuƙar wahala ga masu aiki a ɓangaren masaƙu su samu hutun jinin al'ada a kan sauran ɓangarori.
Ms Widyawati ta ce "mata da ke aiki a ɓangaren ƙananan masana'antu da yawan su ba su san suna da damar ɗaukar hutun al'ada ba. Daya daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta shi ne dole sai sun samo takarda daga wurin likita.
"Haka nan kuma sukan iya fuskantar maganar banza ko kuma su rinƙa jin kunya a lokacin da suke tambaya hutun. Sannan kuma yawancin kamfanoni ba su biyan ma'aikata a lokacin da suka yi hutun al'ada."

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne ciwon mara na al'ada?
- Yawancin mata sukan fuskanci ciwo a lokacin da suke yin jinin al'ada, amma wasu nasu ciwon marar kan yi tsanani sosai, ciwo ne da kan iya hana su yin komai.
- Yawanci yakan zo ne a matsayin ciwon mara, wanda yakan kai har gadon baya, zuwa kafafu, yakan kuma haifar da tashin zuciya, da gudawa da kuma ciwon kai mai tsanani.
- Akwai abubuwa da dama da ke haifar da radadi a lokacin jinin al'ada - misali shi ne rashin daidaiton yawan sinadarin jiki (hormone), wanda ake kira protaglandin, wanda kwayoyin halitta da ke jikin mahaifa suke fitarwa, wadanda kan sa mahaifa ta rinka matsewa. Yawan irin wannan sinadari da fatar jikin mahaifa ke fitarwa shi ne zai tantance karfin matsewar da mahaifa za ta rinka yi, wanda hakan ke janyo ciwo sosai.
- Bincike ya nuna cewa akasarin mata na fuskantar irin wannan ciwo a lokacin al'ada, wanda zafinsa kan iya hana kimanin kashi 20% na mata aiwatar da lamurransu yadda ya kamata.
- Wani nazari da aka yi wa tashar BBC Radio 5, a 2016 a kan mata 1,000, ya gano cewa ciwon mara a lokacin al'ada ya hana kashi 52% na mata gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, amma kashi 27% ne kawai suka fada wa shugabanninsu na wurin aikin gaskiyar abin da ya faru da su.
'Har yanzu abu ne da ba a son yin magana a kai'
'Yancin daukar hutu ga mata masu al'ada doka ce a kasar Japan tun shekaru 70 da suka gabata - inda ma'aikatan kamfanonin da masu hakar ma'adanai ke da damar su dauka idan babu isassun makewayi a wurin aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai masu fafutika sun ce daukar irin wannan hutu ya yi karanci sosai.
"Mata kalilan ne kawai suke daukan hutun jinin al'ada a Japan," in ji Ayumi Taniguchi, shugabar kungiyar Minna No Seiri, wadda ke fafutikar kwato wa mata masu jinin al'ada hakkinsu.
Alkaluman gwamnati sun nuna cewa kashi 0.9% ne kacal na mata ma'aikata suka nemi a ba su hutun jinin al'ada daga Afrilun 2019 zuwa Maris din 2020.
Ayumi Taniguchi ta ce "akwai tsangwama a kan jinin al'ada, masu jinin al'ada na shan wahala a kokarin yin magana domin samun izinin hutun al'ada, musamman a ma'aikatun da maza suka fi yawa."
"Sannan da yawan kamfanoni ba su bayar da hutun jinin al'ada, wato da yawa sai dai su dauka daga cikin hutunsu na shekara a maimakon dauka daga cikin hutun jinin al'ada da doka ta ba su yanci. Ya zama tamkar babu bukatar a tambaya saboda abu ne da ba a son yin magana a kai."











