Ma'auratan da suka yanke shawarar mutuwa tare

Jan (70) and Els (71) photographed two days before they died
Bayanan hoto, Hoton Jan (70) da Els (71) kwana biyu kafin su rasu.
    • Marubuci, Linda Pressly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Jan da Els ma'aurata ne da suka kwashe kusan shekara 50 da aure. Sun mutu tare a farkon watan Yuni, da taimakon likitoci biyu da suka basu maganin da ya taimaka masu suka mutu. A ƙasar Netherlands, hakan ba laifi bane , ya halasta, sai dai hakan bai yi fice ba amman duk shekara ana samun ma'aurata da ke mutuwa ta wannan hanyar.

Gargaɗi: Akwai abubuwan da ka iya tayar da hankali a cikin wannan labarin.

Kwana uku kafin su rasu bisa raɗin kansu, Jan da Els sun zauna a cikin rana a Friesland dake Arewacin Netherlands. Ma'aurata ne da ke son tafiye-tafiye, kusan rayuwarsu a cikin motar tafi da gidanka suke rayuwa ko kuma kwale-kwale.

"Mun yi ƙoƙarin mu rayu cikin gida amman muka kasa,"

Jan ɗan Shekara 70 na zaune kan sitiyarin motar tafi da gidanka, ya yi irin zaman da yake yi domin samun sauƙin ciwon bayan da ke damunsa. Matarsa Els tana da shekara 71 kuma tana da matsalar ƙwaƙwalwa, hakan ya sanya magana ke mata wahala.

"Wannan yana da kyau" ta ce tare da miƙewa tsaye tana nuna jikinta. " Wannan kam akwai matsala, " sai ta nuna kanta.

Jan da Els sun haɗu ne a makaranta a ajin rainon yara a lokacin suna ƙananan yara, sun kwashe tsawon rayuwasu suna soyayya. A lokacin Jan yana matashi yana bugawa ƙungiyar ƙwallon hockey ta ƙasar Netherlands wasa. Inda daga bisani ya zama kocin ƙungiyar. Els malamar makarantar Firamari ce.

A lokacin da suke matasa sun yi rayuwa ne a cikin jirginruwa mai tafi da gidanka. Daga bisani sun sayi jirgin ruwa na daukar kaya domin yin kasuwancin jigilar kaya a cikin Netherlands.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Els ta haifi ɗansu guda wanda ta buƙaci a sakaya sunansa. Yana zama makaranta ne sai hutun ƙarshen mako yake komawa gida wajen iyayensa

Els ta haifi ɗansu wanda suka nemi a ɓoye sunansa. ya kasance yana zama makaranta a kwanakin zuwa makaranta yayin da hutun ƙarshen mako yake zuwa wajen iyayensa. A lokacin hutun makaranta, Jan da Els na ƙirƙirar tafiya mai dogon zango zuwa wurare masu ƙayatarwa.

A 1999, an samu yawaitar masu sana'a irin ta Jan, kuma gashi yana fuskantar ciwon baya sakamakon gwamman shekarun da ya kwashe yana aiki. Saboda hakasai Jan da matarsa suka koma rayuwa cikin gari, sai dai daga bisani sun sake komawa rayuwarsu ta bakin ruwa.

Anyi wa Jan aikin ciwon baya a 2003, sai dai ba a samu nasara, yayin da dukkan magungunan kashe zafi suka daina yi masa aiki, sai dai duk da haka Els na ci gaba da yin aikin ta na koyarwa.

Jan ya shaidawa Iyalinsa cewa baya so yayi tsawon rai da wannan ciwon baya da yake fama da shi, inda a nan ne suka shiga kungiyar dake rajin karre haƙƙin masu so su mutu a Netherlands.

Jan pictured with his son in 1982
Bayanan hoto, Hoton Jan da ɗansa a 1982

A 2018, Els ta yi ritaya daga aikinta na koyarwa. A lokacin alamomin cutar mantuwa sun fara bayyana a jikinta sai dai ta yi ƙoƙarin ganin likita, wanda ake ganin hakan ya fara samunta ne sakamakon mutuwar babanta, a haka har sai da take matakin da cutar ta bayyana ƙarara.

A watan Nuwanba, 2022, a lokacin da gwaji ya tabbatar da tana da cutar mantuwar ta tafi ta bar mijinta da ɗanta a dakin duba marasa lafiya.

Jan ya ce "Zani iya tunawa ta yi fushi mai tsanani"

A lokacin da Els ta fahimci cewa rashin lafiyarta da ta mijinta Jan babu sauƙi, sia suka fara tattaunawa da ɗansu kan mutuwa tare ta hanyar taimakon likitoci.

A ƙasar Netherlands, hakan ba laifi banem, a 2023, mutum 9,068 suka mutu ta hanyar taimakon likitoci, kashi biyar na mutanen da suka rasu.

“ Da yawan likitoci basa son taimakawa mutane masu lalurar mantuwa wajen mutuwa” in ji Dr Rosemarijn van Bruchem ƙwararriya a asibitin Erasmus dake Rotterdam

Hakan ce ta faru tsakanin Jan da Els da likitansu, saboda likitoci na fargabar ta ya zasu samu amincewar wanda bai san ma inda kan shi yake ba ?

“Shin bazan iya yin wasu abubuwa masu mahimmanci ba ? Ba zani iya gane kwoa daga cikin iyalaina ba ? Idan har aka iya tabbatar da haka kuma aka samu ƙwaƙwarar shaida daga ɓangaren likitan mai lalurar mantuwar, sannan aka samu daidaito tsakanin likitan da likitan da zai aiwatar da kisan cikin sauƙi, shikenan za a iya taimakawa masu lalurar mutuwa cikin sauƙi.”

Els, photographed in 1968

Asalin hoton, ELS VAN LEENINGEN

Bayanan hoto, Hoton Els a 1968, wadda daga bisani ta kamu da cutar mantuwa.

A lokacin da likitan Jan da Els ya ƙi amincewa da buƙatarsu, sai suka tafi asibitin tafi da gidan dake taimakwa masu son su mutu cikin sauƙi. Kuma idan ma’aurata nason su mutu tare, dole sai ƙwararru sun tabbatar da cewa ba ɗaya ne yake tilastawa ɗan uwansa ba.

Dr Bert Keizer ɗaya daga cikin likitocin da suka taimakawa masu so su mutu. Ya ce zai iya tunawa akwai lokacin da wasu ma’aurata suka je wajensa kuma ya fahimci lallai mijin ne ke tilastawa matar daukar matakin, saboda haka sai ya yi ƙoƙarin tattauanwa da matar ita kaɗai, kuma nan ne ya fahimci mijin ne ke fama da rashin lafiya mai tsanani kuma shine ke son mutuwa amman banda ita.

Dr Keizer ya ce matar ta shaida masa cewa tana da wasu abubuwa da dama da take son cimmawa a rayuwa kuma bata shirya mutuwa ba

Hakan ya snaya likitan bai aiwatar da hakan ba inda daga bisani mijin ya mutu sakamakon cutar da ke damunsa ita kuma matar har yanzu tana raye.A lokacin da likitan Jan da Els ya ƙi amincewa da buƙatarsu, sai suka tafi asibitin tafi da gidan dake taimakwa masu son su mutu cikin sauƙi. Kuma idan ma’aurata nason su mutu tare, dole sai ƙwararru sun tabbatar da cewa ba ɗaya ne yake tilastawa ɗan uwansa ba.

Dr Bert Keizer ɗaya daga cikin likitocin da suka taimakawa masu so su mutu. Ya ce zai iya tunawa akwai lokacin da wasu ma’aurata suka je wajensa kuma ya fahimci lallai mijin ne ke tilastawa matar daukar matakin, saboda haka sai ya yi ƙoƙarin tattauanwa da matar ita kaɗai, kuma nan ne ya fahimci mijin ne ke fama da rashin lafiya mai tsanani kuma shine ke son mutuwa amman banda ita.

Dr Keizer ya ce matar ta shaida masa cewa tana da wasu abubuwa da dama da take son cimmawa a rayuwa kuma bata shirya mutuwa ba

Hakan ya snaya likitan bai aiwatar da hakan ba inda daga bisani mijin ya mutu sakamakon cutar da ke damunsa ita kuma matar har yanzu tana raye.

Els and Jan on their wedding day, 1975
Bayanan hoto, Els da Jan a ranar aurensu, 1975

Kwana ɗaya kafin Jan da Els da su je wajen likitan da zai taimaka masu su mutu tare cikin sauƙi, sun zauna tare da ɗan su da jikokinsu. Jan ya yi ƙoƙarin yi wa ɗan nasu bayani kan motarsu ta tafi da gidanka da hanyar da zai bi wajen sayar da shi.

"Na yi tattaki tare da mahaifiyata zuwa bakin teku, yarana sun yi ta wasa da ita, ranar ta kasance mai tada hankali," inji ɗan Jan da Els

"Zani iya tuna lokacin da muka ci abincin dare tare, na riƙa zubar da hawaye a lokacin da na kallesu a matsayin wadanda muke zaune da su zama na ƙarshe tsakaninmu."

A ranar Litinin da safe, manyan abokanansu sun hallara da ƴan uwansu da ɗan su da matarsa.

"Mun kwashe sa'o'i biyu kafin likita ya zo, mun tattauna kan yanayin rayuwarmu a baya.....mun kuma saurari waƙoƙin da suke so tare"

"Rabin sa'a ta ƙarshe da muka kasance tare da su ta kasance mafi muni,likitoci na zuwa komai ya faru cikin sauri, anyi duk abinda ya dace cikin ƴan mintoci komai ya ƙare," inji ɗan Jan da Els

An yi wa Jan da Els allurai da magungunan da suka taimaka masu wajen mutuwa cikin sauƙi a ranar litinin 3 ga watan Yuni, 2024.

Har yanzu ba a sayar da motarsu mai tafi da gidanka. Ɗan Jan da Els ya yanke shawarar barin shi zuwa wani lokaci inda yake son zuwa hutu da matarsa da ƴanƴansa da motar.

"A ƙarshe dai dole zani sayar da ita amman kafin nan inason in samu wani abu da zamu riƙa tuna wa ni da iyalaina kan motar."