Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Arewa da aka rushe wa kasuwa a Lagos na neman diyya
'Yan kasuwar Alaba Rago da ke karamar hukumar Ojo a jihar Lagos, na neman gwamnatin jihar ta biya su diyyar biliyoyin naira bisa asarar da suka yi a yayin wani rusau da jami'an gwamnatin jihar suka yi a mafi yawa daga babbar kasuwar.
'Yan kasuwar wadanda yawancinsu 'yan yankin arewacin Najeriya ne sun yi zargin cewa wasu daga cikinsu sun hada baki da jami'an gwamnati don aiwatar da rushe-rushen, duk kuwa da ci gaba da yarjejeniya tsakanin shugabannin 'yan kasuwar da gwamnan jihar na bunkasa kasuwar da kudadensu.
Mutanen sun bukaci gwamnatin Lagos ta biya su diyya ko kuma su bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin kwato hakkinsu, kamar yadda suka yi barazana.
Suna kokawa ne saboda girman rusau din da suka ce ya wuce yanda hankali zai dauka, ganin irin asarar dukiya da suka yi.
Sun ce tun da ba wani laifi suka aikata ba, ko wata yarjejeniya suka saba ta zamansu a kasuwar ta Alaba Rago ba, gwamnatin jihar ta zo kwatsam ta yi musu wannan rusau, to ya kamata ta biya su hakkinsu na dukiya da ta janyo musu asara.
'Yan kasuwar sun yi nuni da cewa a baya sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar kuma ba wannan ba ce yarjejeniyar da suka yi da ita ba, da za ta yi musu wannan rusau ba.
Alhaji Adamu Katagum wanda shi ne Wazirin Sarkin Alaba Rago ya ce asarar da 'yan kasuwar suka yi ta biliyoyin naira ce:
''An rusa dukiyoyin mutane na biliyoyin kudi babu notis kayanka ma ba za a bar ka ka dauka ba.
''Dukkan wani inda ake hada-hadar kasuwanci - sayar da shinkafa, sayar da wake, sayar da masara, masu nika an rusa shagunansu, an rusa gidagen ajiyar kayan kasuwa hawa biyu, hawa uku an rusa,'' in ji shi.
Dangane da diyyar da suke nema gwamnatin jihar ta biya su - saboda lalata musu dukiyar da ya ce an yi, Alhaji Adamu ya ce, bangaren rago ba za su ce an taba rago ba.
''Bangaren dukiyoyi da aka taba na mutane tsakani da Allah ba za mu yarda ba. Muna neman hakkinmu na diyyarmu na wanda muka raya wannan guri tun iyayenmu kusan shekara hamsin har ya shigo idon gwamnati ta ga cewa za ta amfana akwai hakkinmu da ya kamata ta ba mu.'' Ya ce.
Alhaji Bala Kofar Sabuwa wanda yana daya daga cikin 'yan kasuwar da rusau din ya shafa, ya ce jami'an gwamnatin sun shammace su ne kamar sun zo su yi aikin titi da motoci sai suka shiga rushe musu shaguna.
Ya kara da cewa: ''Yin wannan aiki ya janyo bata-gari sun shiga kasuwa sun fa shagunan mutane sun kwashe musu kaya, yanzu mutane suna zaune a rana, wasu kuma suna gadon asibiti a sanadiyyar wannan abu da ya faru.
Gwamnatin Legas ta fara aikin rushe kasuwar ta Alaba rago ne tun daga ranar Lahadi 17 ga watan nan na Agusta, 2025 ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 20 ga watan na Agusta.
A bara ma gwmantin jihar ta yi yunkurin rushe kasuwar amma Sarkin hausawan Legas Alhaji Aminu Yaro Dogara da tawagarsa suka sa baki gwamnatin ta dakatar da rushe-rushen.
Kasuwar ta Alaba Rago matattara ce ta 'yan kasuwa daga arewacin Najeriya, yawanci inda ake shigar da kayan abinci da dabbobi daga arewacin kasar.
Gwamnatin jihar Legas na nuna cewa tana yin irin wadannan ayyuka ne na rusau da nufin zamanantar da manayan kasuwannan jihar ta yadda za su da ce da zamani.