Darussa biyar da suka kamata Arewa ta koya game da katsewar lantarki

Asalin hoton, TCN
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Kamfanin da ke rarraba wuta a Najeriya, TCN ya ce wuta ta samu a wasu jihohin arewa da suka haɗa da Kano, Nassarawa, Benue, Kaduna, Bauchi da Gombe bayan gyara da jami'ansa suka yi a ranar Laraba.
Kamfanin ya ce wutar ta samu ne bayan aiki a kan layin Apir-Lafia 330kV wato ɗaya daga cikin layika biyu da suke a Shiroro-Ugwaji da suka lalace, inda kuma TCN ɗin ya bayar da tabbacin cewa jami'ansa na aiki a kan ɗaya layin domin tabbatar da kowane gari ya samu wutar kamar a baya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da yankin na arewa ya kwashe kwanaki 10 cif-cif ba tare da wutar lantarki ba, al'amarin da janyo tsaiko a fannonin aiki da kasuwanci da ma lafiya.
Usman Minjibir, ma'aikacin BBC Hausa ya yi duba dangane da darussa biyar da ya ce sun fito fili daga katsewar wutar a arewacin Najeriya kamar haka.

1) Girman matsalar tsaro
Kamfanin rarraba wutar na Najeriya, TCN dai ya yi zargin ƴanta'adda ne suka yi amfani da abubuwan fashewa kan turken layi ɗaya daga cikin layuka biyu na wutar da ke garin Ugwaji-Apir da ke tsakanin Shiroro zuwa Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa ƴanbindigar da ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya ne suka lalata turken.
Masana harkar tsaro na yin kira ga gwamnatocin tarayya na jihohin arewa da su tashi tsaye wajen tunkarar matsalar tsaro wadda ke neman durƙusar da yankin musamman yadda rashin wutar ya jefa arewa cikin duhu.
Harin da ƴanbindigar suka kai kan wani sansanin horas da sojoji a Kwantagora wanda bayanansa suka fito fili a farkon makon nan. Sansanin wanda ke kusa da inda ƴanbindigar suka lalata turken wutar, na ɗaya daga manyan sansanonin horas da sojoji a Najeriya.
2) Ƙarancin ɗaukar matakan gaggawa
Abu ne dai a buɗe a Najeriya cewa akwai ƙarancin ɗaukar matakan gaggawa a ƙasar a duk lokacin da irin wannan al'amari ya faru mai kama da bala'i domin matsalolin da ya kamata a tunkarar a lokaci ƙanƙane kan ja dogon lokaci.
Misali a bin da ya faru na katsewar wutar idan a watar ƙasar ne za a samar da ɗaukin gaggawa wajen warware wannan matsalar ta wuta wanda ta nemi kassara yanki gabaɗaya - kuma babban yanki kamar arewacin Najeriya.
3) Asarar dukiya
A bayyana take cewa wutar lantarki ita ce ƙashin bayan cigaban Najeriya da ma duk kasashen duniya inda tattalin arziƙin ƙasashe ke dogara ga wutar lantarki.
Katsewar wutar a yankin na Arewa ya janyo masana'antu ƙanana da manya sun tsaya cak baya ga asarar da suka musamman bisa la'akari da katsewar wutar a daidai lokacin da man fetur ya yi tsadar gaske.
Wakilan BBC a birnin Kano sun rawaito yadda masu sana'ar kifi da nama suka yi asara saboda rashin wutar. Haka ma masu sana'o'in hannu kamar walda da ɗinki da sauran su duk sun tsaya cak.
Duk da cewa kawo yanzu masana harkar tattalin arziƙi da hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ba su fitar da alƙalauman yawan asarar da aka yi a tsawon kwana 10 da yankin ya kwashe ba tare da wuta ba, amma abu ne a fili an tafka asara.
4) Buƙatar jihohin arewa na kafa wutarsu
Kafin faruwar katsewar wutar ga arewacin Najeriya, bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa jihohi uku ne suke da tsarin samar da wuta domin rage dogaro ga wutar tarayya.
Jihar Kano tana da tashar samar da megawatts 10 a dam ɗin Tiga duk da cewa a baya-bayan nan injinan da ke samar da wutar sun samu ƴar tangarɗa.
Sai kuma jihar Sokoto da ke da daɗaɗɗen burin samar da wutar mai ƙarfin megawatts 38 to amma har yanzu mafarkin bai kai ga cika ba shekaru 16 da dasa ɗanba.
A jihar Katsina, gwamnatin jihar ta ƙaddamar da aikin samar da wuta ta hanyar iska a 2005, inda a 2007 gwamnatin tarayya ta karɓi aikin. To sai dai har kawo yanzu mafarkin bai kai ga zama gaske ba.
5) Haɗin kan gwamnonin arewa
Za a iya cewa katsewar wutar ta janyo wani taron gwamnonin arewa da sarakunan gargajiyar yankin a Kaduna, kusan irinsa na farko, inda ba tare da banbancin siyasa ba suka tattauna matsalar da yankin ke fama da shi wato tsaro wanda shi ne ya haddasa matsalar katsewar wutar.
Masana dai na ganin cewa taron ya sanya shugabannin yankin yin nazari wanda ake wa kallo na gaskiya ne saboda ƙalubalen da ke gaban yankin.
Fatan ƴan arewacin Najeriyar dai a yanzu bai wuce ganin gwamnonin yankin sun ƙaddamar da abubuwan da suka cimma a lokacin taron nasu na Kaduna, kasancewar an yin ruwa ƙasa na tsotsewa - babban fatan dai shi ne wannan katsewar wutar lantarki ta zama wani darasi na tunkarar ƙalaubalen da yankin ke fuskanta.











