Dole Chelsea ta biya fam miliyan 5 idan ta fasa sayen Sancho

Lokacin karatu: Minti 1

Idan ƙungiyar Chelsea da ke Ingila ta fasa sayen Jadon Sancho na dindindin, dole za ta biya ƙungiyar Manchester United kuɗi har fam miliyan biyar.

Ɗan wasan mai shekara 24 ya koma Chelsea ne a matsayin aro daga Machester United na shekara ɗaya a watan Agustan bara, inda a cikin yarjejeniyar aka amince Chelsea na da zaɓin sayensa a kan tsakanin fam miliyan 20 zuwa miliyan 25 matuƙar kulon ɗin ba ta haura ta 14 ba a teburin gasar Premier ta Ingila a kakar bana ba.

Yanzu dai Chelsea ce ta huɗu, kuma saura wasa tara kakar ta ƙare.

Yanzu dai shawara ta rage ga Chelsea, inda take da zaɓin ko dai ta saye shi, ko kuma ta mayar da shi kulob ɗinsa, ta biya makudan kuɗin.

Da farko dai Chelsea ta nuna sha'awar riƙe ɗan wasan, amma yanzu rahotanni na nuna cewa hankalin ƙungiyar ya fara rabuwa kan cigaba da riƙe shi.

Ɗan wasan ya fara ƙwallo a Chelsea da ƙafar dama, amma daga bisa abubuwa suka sauya, inda a wasa 18 da suka gabata, sau ɗaya kawai ya taimaka aka zura ƙwallo.

Rahotanni dai na cewa tuni Chelsea ta fara zawarcin wani ɗan wasan gefen da na gaba.