Mutanen da suka shafe awa 30 a layin yin bankwana da gawar Sarauniya Elizabeth

Kristian Johnson a cikin tanti

Dubban mutane ne suke ta tururuwar zuwa yin bankwana da gawar Sarauniya Elizebeth, a yayin da ya rage kwana uku a binne ta.

Wakilin BBC Kristian Johnson, ya shiga cikin mutanen da suka shafe dare a kan layin shiga ganin gawar Sarauniyar inda har ya yi sabbin abokai a zaman da suka yi cikin zubar ruwan sama a Landan.

Da misalin karfe 10 na yammacin ranar Talata ce aka bude wajen shiga ganin gawar Sarauniyar.

Mutanen da suka yi sabo da juna a wajen kafin su shiga ganin gawar na da dama sosai, kuma sun rinka amfani da lemar juna saboda ruwan da ya sauko a wajen.

Ina daga cikin wadanda suka yi sa'ar shiga wajen.

Ya ce, "Na samu wajen fakewa a jikin ginin wani banki saboda ruwan da ake yi, to amma duk da haka sai da wandona ya jiƙe.

Ba kuma ni kadai ne hakan ta faru da ni ba."

Wata mata da ke wajen ma ta ce sun jiƙe sharkaf, amma daga bisani sun bushe.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yawan 'yan jarida a wajen ya fi na mutane a ranar Litinin, a lokacin da Vanessa Nathakumaran, ta je wajen ta shiga gaban layin.

Daga ita sai 'yar jakarta ta je wajen kuma tana da sa'a fiye da 48 da suka rage mata kafin ta shiga cikin dakin da aka ajiye gawar.

Kristian Johnson, ya ce a lokacin da je wajen da rana ya tarar da ita kuma ya samu an ba shi lamba 17 a cikin wadanda ke kan layi.

Michael Darvill, mai kimanin shekara 85 tare da 'yarsa Mandy Desmond mai shekara 55, sabbin makwabtan dan jaridar ne da tuni suka samu kujeru suka zauna don jiran shiga ganin gawar.

Babu wasu litattafai ko wasu abubuwan da za su iya dauke musu kewa a wajen, illa kawai hira tsakanin wadanda ke wajen.

Babu wanda yake duba wayar salularsa ko kuma ya sanya ta a caji, akwai batutuwan yin hira a kansu a wajen.

A lokacin da ruwan sama ya sauko da rana a ranar Talata, mutum 50 ne kadai suka rage a kan layin in ji dan jaridar.

Wani mutum mai suna Gary Keen, ya rinka bin layi yana raba wa mutane gutsuren pizza.

Jacqueline Nemorin, daga Mauritius, ta rinka rarraba wa matan da ke kusa da ita a kan layi inibi, can kuma sai ga wasu mutane sun isa wajen sun raba kofin shayi da na gahawa.

Yaqub Yousuf, wanda ke zaune a kusa da Gadar Lambeth, ya kawo nasa taimakon wajen, don taimaka wa mutanen da ke kan layin shiga ganin gawar Sarauniya.

Daga bisani mutane da dama sun rinka kai nasu taimakon ciki har da masu kai abinci wajen.

 Wannan matar ta je Ingilane a 1954, shekara guda bayan nadin Sarauniya Elizebeth
Bayanan hoto, Wannan matar ta je Ingila ne a 1954, shekara guda bayan nadin Sarauniya Elizebeth

Duk da kasancewar ana tsakiyar ruwan sama a wajen a lokacin, Andrew Israels-Swenson, ya ci gaba da samun labarai daga wajen wannan dattijuwa mai shekara 85, Truus Nayman.

Ta kuma bayar da labarai daban-daban.

Andrew, wanda ya je wajen daga Minnesota a daren ranar Asabar, ya ce ya samu tikitin zinare saboda samun damar zuwa wajen da wuri har ya shiga layin ganin gawar Sarauniya, ya kwana a kan benci a zaune.

Truus, ta zo ne daga Netherlands, ta shaida mini cewa ta je Landan ne a shekarar 1954, shekara guda bayan nadin Sarauniya Elizebeth.

Ta ce, "Na dan yi tsufa a yanzu musamman wajen bin layin, ni da mijina mun taba bin layi irin wannan a lokacin da Winston Churchill ya mutu a 1965, sai da muka shafe dare muna tsaye a nan."

"A lokacin da Gimbiya Diana ta mutu a 1997, ni da ɗana mun sake bin layi a Fadar Kensington don rubuta ta'aziyyarmu a cikin littafin da aka ware.

"Sannan a lokacin da mahaifyar Sarauniya Elizebeth ma ta mutu a 2002, na zo da kaina na bi layi, ni asalina mai biyayya ce."

Da misalin karfe biyu na dare na shiga tantina na ɗan kwanta.

Ko da na tashi bayan sa'o'i biyu, sai na ga Micheal da 'yarsa Mandy suna dariya duk da rashin baccin da ba su yi ba.

Micheal ya ce, "Mun jiƙe da ruwa tun misalin karfe biyu na dare, kuma ga shi ba mu bushe ba, saboda ruwan yana zuwa ya kuma dauke don haka a cikin ruwa muka zauna."

 Monica Farag ita ce ta shida a kan layi

Cikin ikon Allah, sai ruwa ya dauke a lokacin rana ta fara fitowa.

A nan mutane wasu fara shan gahawa wasu kuma na goge idanunsu yayin da ya rage musu sa'o'i su shiga gani da kuma bankwana da gawar Sarauniyar.

Monica Farag, wadda 'yar asalin Philippines ce, ita ce ta shida a kan layi.

Ba ta samu kujerar zama ba, a haka matar mai kimanin shekara 61 da haihuwa ta rinka kai komo har gari waye.

Ta ce, "Ina matukar daukin gani da bankwana da gawar Sarauniya, ko da yake ban ko rintsa ba.

"Lokaci ne mai matukar tarihi a gare ni saboda na shafe shekara 36 a Ingila."

"Jim kadan bayan wayewar gari aka umarci ta naɗe tanti na, can na hango cuncurundon mutane ga shi kuma kowa ya hau kan layi.

"Da misalin karfe 3 na yamma, sai aka umarci mu shiga amma an kiyasta cewa mutum 20 ne za su rinka shiga a lokaci guda.

"Na bi sahunsu Truus da Andrew da Micheal da Mandy da kuma Paul, wadanda suka kasance makwabtana a wannan dare a lokacin da aka umarci su fara tafiya a hankali zuwa Westminister.

Da misalin karfe 5 na yamma, aka bude kofar majalisar dokoki a hankali daga nan sai aka fara shiga a hankali kuma kowa ya tsit.

A tsakiyar zauren taron na Westminister akwatin gawar Sarauniya ne a ajiye.

Wata mata da ke bayana sai na ji ta fara shesshekar kuka, a gabana kuma Andrew da Truus ne suke tafiya kadafa da kafada.

Na ji dadin shiga wannan zaure bayan na shafe sa'o'i 30 ina jira.