Abin da ake nufi da nuna ƙyama ga Yahudawa da kafa ƙasarsu

Yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin Isra'ila da Gaza, mutane da dama a shafukan sada zumunta na ƙoƙarin fahimtar bambancin da ke tsakanin nuna ƙyama ga Yahudawa (anti-semitism) da adawa da kafa ƙasar Yahudawa a Falasɗinu (anti-zionism).

Me waɗannan kalmomi ke nufi?

  • Antisemitism na nufin nuna ƙyama ga Yahudawa kuma wannan abu ne da aka shafe ƙarni ana yi
  • Anti-Zionism shi kuma yana nufin nuna adawa ga kafa ƙasar Isra'ila

Mene ne nuna ƙyama ga Yahudawa?

Yahudawa sun fuskanci ƙyama da ƙabilanci da cin zarafi na tsawon gomman shekaru.

Lokacin yaƙin duniya na biyu, Yahudawa miliyan shida 'yan Nazi ko mataimakansu suka kashe a abin da ake kira kisan kiyashin Holocaust.

Nuna wa Yahudawa ƙyama a zamanin yanzu na iya ɗaukar ma'ana da dama kamar hare kan wasu tunane-tunane ba game da ikon Yahudawa kan tsarin kuɗi a duniya da kafofin yaɗa labarai da hare-hare kan gine-ginen addini da cin zarafi da kalaman ƙiyayya a shafukan sada zumunta.

Wasu lokutan mutane masu banbancin ra'ayi kan Isra'ila za su ƙi yadda a kan ko wasu kalamai ko ra'ayoyi na nuna ƙyama ne ko a a.

Galibi, tattaunawa sun haɗa da Isra'ila da kalmar "Zionism" - ra'ayin samar da ƙasar Yahudawa.

Mene ne rajin kafa ƙasar Yahudawa?

An soma neman kafa ƙasar Yahudawa a matsayin ƙungiyar siyasa a Turai a ƙarshen ƙarni na 19; an nemi a samar da ƙasar Yahudawa a Falasɗinu - da Yahudawa suka sani a matsayin daɗadɗiyar ƙasar Isra'ila.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da shawarar raba Falasɗinu zuwa ƙasar yahudawa da Larabawa, kuma a 194 aka ayyana ƙasar Isra'ila.

Sai dai Larabawa da dama da ke zaune a Falasɗinu da yankunan da ke kewayen sun nuna adawa da samar da ƙasar Isra'ila, suna kallon lamarin a matsayin hana 'yancin Larabawa.

Akwai ra'ayoyi mabanbanta game da samar da ƙasar Falasɗinu - misali, wasu masu wannan ra'ayin na ganin Isra'ila na da 'yanci kan wasu yankunan da ba nata ba. Wasu kuwa sun nuna ja.

Akasarin Yahudawa sun goyi baya ko tausayawa muhimman tsare-tsaren kafa ƙasar - ma'ana a samar da ƙasar Yahudawa a abin da yanzu yake Isra'ila.

Wasu tsiraru sun nuna adawa da haka, ko dai saboda dalilai na addini ko siyasa.

Su ma mutanen da ba Yahudawa ba ma suna iya zama masu ra'ayin kafa musu ƙasa.

Mene ne adawa da kafa ƙasar yahudawa?

Anti-Zionism za a iya fassara shi da nuna adawa da kafa ƙasar Isra'ila.

Akwai masu rajin kafa ƙasar da ke sukar manufofin gwamnatin Isra'ila kamar mamaye gaɓar yamma da kogin Jordan da hanyar da ta raba su (da Isra'ila ke ginawa a ciki da wajen gaɓar yamma da kogin Jordan wanda ta ce ta gina ne a matsayin kariya daga mahara Falasɗinawa.

Magoya bayan Falasɗinawa dai na kallon haka a matsayin wata hanya ta ƙwace (kasar Falasdinawa) da kuma gina matsugunai a ciki.

A wasu lokutan da mutane suka soki Isra'ila, ya zama abu mai wahala a san ko caccakar ta samo asali ne daga masu ƙyamar Falasɗinawa.

Wannan ya janyo zarge-zargen cewa adawa da samar da ƙasar Falasɗinu - ma'ana fatali da ƙasar Yahudawa - kawai wani salo ne na nuna ƙyama ga Yahudawa.

Shirin tunawa da kisan kiyashin da aka Holocaust ya ce wasu ikirari da zarge-zarge da ake yi wa Isra'ila ya zama nuna ƙabilanci ga Yahudawa.

Waɗanda suka ƙi amincewa da hakan sun ce ana amfani da jayayyar a matsayin wani makami da magoya bayan Isra'ila ke amfani da shi wajen murƙushe caccaka mai ma'ana da ake yi wa Isra'ila ta hanyar bayyana sukar a matsayin ƙabilanci.

Wasu sun ce ana iya amfani da kalmar "Zionist" a matsayin wani shiri na sukar Yahudawa yayin da wasu ke cewa gwamnatin Isra'ila da magoya bayanta da gayya suke rikicewa kan kalmonin 'anti- zionism' da 'antisemitism' domin kaucewa suka.