Madubin James Webb ya ɗauko rangaɗeɗen hoton duniyar Neptune da zobenta

Jonathan Amos

Wakilin BBC kan Kimiyya

Details not seen in more than three decades are apparent in the Webb imagery

Asalin hoton, IMAGE SOURCE,NASA/ESA/CSA/STSCI

Bayanan hoto, Fiye da shekara 30 kenan ba a samu bayanai sosai kan duniyar ba kamar na wannan lokacin

Madubin hangen nesa na James Webb da aka aika shi sararin samaniya kwanan nan ya aiko da sababbin hotuna masu ƙayatarwa na duniyar Neptune.

Madubin mai aiko da hotuna tar-tar ya aiko da bayanai sosai irin waɗanda rabon da a samu irinsu tun sanda aka tura rokar Voyager 2 da ta wuce ta gaban duniyar a 1989.

Cikin abin da aka gani har da zobunanta da ƙurar da take zagaye da tsibin ƙanƙararta.

Masana kimiyya sun kuma yi mamakin yanayin gajimaren da suka gani daban-daban, da ke nuna musu cewa akwai abin rubutawa dangane da yanayin sararin samaniyar Neptune.

Baya ga duniyar ita kanta, an kuma ga watanninta manya har bakwai daga cikin 14 da take da su, wanda aka fi gani sosai shi ne Triton.

Watan ya yi kamar tauraruwa a jikin hotunan na Webb.

Hakan ya faru ne saboda Neptune ta yi duhu a jikin madubin. Shi kuma watan Triton ya yi haske saboda ya tatso kashi 70 cikin 100 na hasken da ya faɗa kan ƙanƙanrar da ke kansa. Ya yi haske sosai.

The ice giant Neptune has a total of 14 moons, the largest of which is the geologically active Triton

Asalin hoton, IMAGE SOURCE,NASA/ESA/CSA/STSCI

Bayanan hoto, Neptune tana da wata 14 da ke zagaye ta, kuma babban cikinsu shi ne Triton
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Leigh Fletcher na Jami'ar Leicester yana wajen taron kmiyya na Europlanet da ake yi a garin Granada da ke Spain, "inda kowa ke ƙoƙarin fassara hakan a kan wayoyinmu, amma abin al'ajabi ne ganin waɗannan zobuna, kuma muna duba sigina ta saƙon da madubin ya aiko."

"Abin jin daɗi ne ganin yadda kowa yake ɗoki!" ya shaida wa BBC.

"Sigina ɗin sabbi ne kuma za su iya ba mu damar gano abubuwa da dama tattare da duniyoyin Jupiter da Saturn.

"Gajimaren Neptune suna da ƙarfi sosai fiye da a baya, kuma dukkan iyalan Neptune sun bayyana a nan, tare da zobunanta da watanninta ciki har Triton."

Neptune ita ce duniyar da ta yi nisa da tsakiyar unguwarmu ta rana, tana can gaban Uranus da Saturn, amma kusa da ƙaramar duniyar Pluto.

Tana zagaye rana daga nisan kilomita biliyan 4.5, kuma tana shafe shekara 164.8 kafin ta kammala zagaye ɗaya.

Kamar sauran duniyoyin rana mafiya girma, sararin samaniyarta na ɗauke da iskar hydrogen da helium. Amma akwai kuma ƙanƙara sosai da ruwa da ammonia da methane.

Girman Neptune ya kusa kilomita 50,000, wato ta nunka duniyarmu ta Earth sau kusan huɗu.

The ice giant Neptune has a total of 14 moons, the largest of which is the geologically active Triton

Asalin hoton, IMAGE SOURCE,NASA/ESA/CSA/STSCI