Gagarumin sauyi a dashen sassan jiki zai ƙarfafa zukatan dubbai a Uganda

Majalisar dokokin Uganda tana nazari kan wani ƙudurin doka da zai ba da damar yin dashen sassan jiki karon farko a ƙasar, abin da zai kawo sauyi ga rayukan dubban mutanen da ke fatan samun tiyata. Annita Twongyeirwe tana hangen makoma iri daban-daban ga rayuwarta. Sai dai tun da aka gano ta kamu da ciwon ƙoda shekara uku da ta wuce, matashiyar 'yar shekara 28 ta damu da batun wankin ƙoda da kuma tunanin karo na gaba da za a sake yi mata.
"Abin yana ci min rai," in ji ta, duk jikinta a sanyaye. A lokacin wankin ƙoda wata na'ura ce da ke aiwatar da aikin ƙoda da wanke gurɓataccen jini da ruwan da ya yi wa jiki yawa. Duk karon da za a yi, wankin ƙoda yana ɗaukar kimanin sa'a huɗu kuma tana zuwa asibiti sau biyu a mako ɗaya. A lokacin da ba za ta je wankin ƙoda ba, akasari tana gida - gidan danginta - tana taya su aikace-aikacen gida da za ta iya, da kuma duba abubuwan da ake wallafawa a zauren Whatsapp da ta kafa don kawaye da masu yi mata fatan alheri su iya ba da gudunmawar kuɗi. "Ni yarinya ce mai dogon buri. Ina son na je ƙaro karatu. Mai yiwuwa na zama budurwa ko matar wani, to kun ga an datse rayuwa ke nan. Lamarin ya tafi da duk burukan da nake da su," ta ƙara da cewa. Dashen ƙodar na iya dawo mata da su. Sai dai, tiyata a ƙasar waje, a yanzu zabin da kaɗai take da shi, ya kai tsadar $30,000 (N21,600,000) - wannan kuwa ya fi ƙarfinta. Daruruwan 'yan Uganda waɗanda kamar Annita Twongyeirwe ba za su iya biyan haka ba, za su ci gaba da rayuwa a kan wankin ƙoda tsawon lokaci. Sai dai ko farashi mai rangwame na $100 (N72,000) duk mako don shan magani da kula da lafiya, hakan ya ninka har sau biyar kan jimillar kuɗin shigar da 'yan Uganda ke samu kuma shi ne kaɗai zabin da rukunin al'ummar ke da shi. Dakin kwanciya na Babban Asibitin Kiruddu na Kasa da ke gefen babban birnin Kampala, shi ne kaɗai cibiyar lafiyar jama'a a ƙasar da ke ba da irin wannan kulawar. Marasa lafiya kusan 200 ne ke zuwa asibiti a kai-a kai da yawansu kuma sai sun yi doguwar tafiya. Sai dai, kason na wakiltar wani rukuni ƙalilan ne na mutanen da ke fama da larurar ciwon ƙoda a faɗin ƙasar waɗanda kuma ke bukatar kulawar ƙwararru. "Suna barin iyalansu da sana'o'insu a can, su tafi su zauna kusa da asibitin. Wannan wani al'amari ne da ba a saba gani ba," kamar yadda Dr Daniel Kiggundu guda ɗaya tilo da ke aiki a sashe, ya faɗa wa BBC.

Sashen, wata matattarar injina ce, yayin da ma'aikatan jinya ke kai komo a tsakanin tashoshin wankin ƙodar don kula da marasa lafiya. Wasu da ke samun kulawa, za ku gan su jikin ya yi matuƙar rauni, barci yana ɗibansu, suna farkawa, yayin da wasu ke zaune suna tattaunawa da ma'aikatan jinya. Asibitin yana da tsarin ma'aikata da ke karbar aiki sau biyu a kullum, kowanne rukuni yana kula da marasa lafiya kimanin 30. Yana aiki cikin hatsarin gab da ƙure ƙarfinsa kuma akwai ƙarancin lokacin da ake shirya maras lafiya kafin ba shi kulawa. Duk lokacin da Annita Twongyeirwe za ta je ganin likita, tana kwana a asibitin ne don ta shirya a tsanake. A 2018 ne, Annita ta fara gane cewa ba ta da lafiya, lokacin da ta ga duk jikinta ya fara kumbura, kuma ta shafe tsawon shekara ɗaya da rabi tana zuwa daga wannan asibiti zuwa wani kafin ta samu a gano daidan abin da ke damunta. Rayuwarta duk ta hargitse. Sai da ta bar jami'a inda take karantar aikin lauya har ma ta rasa aikinta. Ta bar gidansu da ke yammacin Uganda zuwa babban birnin Kampala kusa da asibiti. A gida, matar mai sanyin murya takan yi wanke-wanke da irin ƙarfin halin jin cewa, in ban da filastar da ke hannunta, da ƙyar za a iya cewa ta dawo ne daga wankin ƙoda. 'Ina jin wani irin gingiringim' "Lokacin da na komo daga asibiti nakan huta saboda duk jikina ya yi la'asar. Babu daɗewa kuma zan tashi na yi 'yan aikace-aikacen gida don na ji kuzari," a cewarta. Ta ce tana tara gudunmawar kuɗin da take buƙata kowanne mako daga 'yan'uwa da abokan arziki. "Nakan ji tamkar na zama ƙarin nauyi ga mutanen da ke taimaka min don biyan kuɗin wankin ƙoda. A duk lokacin da mutum ya ga kiran wayarki, ya san kuɗi kike nema daga gare shi." Annita ta kuma je ga dangi tana neman ko wani zai so ya ba ta gudunmawar ƙoda. Ta ce wani kawunta ya nuna muradin taimakawa amma daga bisani ya canza shawara. Ko akwai wannan alƙawari har yanzu, sai Annita ta tara gudunmawar ƙarin kudi, kuma ta samu izinin hukumomin lafiya kafin ta iya tafiya kasashen waje don a yi mata aiki.
Sai dai idan aka zartar da wannan ƙudurin doka, to ɗaya daga cikin abubuwan da suka zame mata shamaki, ya kau.

Uganda za ta shiga jerin ƙasashen Afirka ƙalilan ciki har da Afirka ta Kudu da Tunisiya da Kenya da ke da tsare-tsare da kayan aikin likitancin yin dashen ƙoda. A yanzu haka ƙasashen Indiya da Turkiyya ne masu cutar ƙoda daga Uganda suka fi zuwa. Dangin maras lafiya ne kawai aka bai wa damar ba da gudunmawa da kuma yin tafiya ƙetare, kuma sai Hukumar kula da Lafiya ta Uganda ta amince da hakan don hana fataucin sassan jikin mutane ko kuma a tursasa wa mutum ba da wani sashen jikinsa. Sai dai idan majalisar dokokin ƙasar ta amince da sabbin matakan da ake son ɓullowa da su, tsarin zai fi zama kai tsaye kuma kuɗin tiyata da na kula da farfadowar maras lafiya na iya raguwa zuwa kimanin $8,000 (N5,760,000) Masu goyon bayan ƙudurin dokar na cewa Uganda na buƙatar wata doka ta musamman don samar da wani amintaccen tsari a ƙarkashin tsauraran ƙa'idoji da za su tabbatar cewa ba a tozarta harkar ba. Kudurin dokar ya ƙunshi samar da wani kundin sunayen masu neman gudunmawar sashen jiki na ƙasa da kuma kafa wasu cibiyoyin ƙwararrun dashe a faɗin ƙasar. Tuni aka buɗe wani ɗakin tiyata a babban asibitin ƙasa da ke Mulago na birnin Kampala. Za a tanadi cibiyoyin adana sassan jikin mutum ga waɗanda ke son ba da gudunmawa - ba kawai na ƙoda ba. "Muna [kuma] tunanin yin dashen zinariyar ido [da kuma] cibiyoyin dashen fata ga mutanen da suka ƙone," Dr Fualal Jane Odubu cewar, shugabar Hukumar kula da harkokin Lafiya ta Uganda.

Duk da fatan da hakan zai kawo, akwai kuma buƙatar jerin mutanen da za su yi zaman jira da kuma buƙatar tara gudunmawar kudi. Annita Twongyeirwe ta ce tunanin yanke ƙauna har yanzu bai yi nisa ba. "Sauran marasa lafiya da muka zama kamar dangi ɗaya. Ranaku mafi wahala su ne duk lokacin da kuka zo asibiti, kuka ji wani ya mutu. Kwanan nan, muka yi rashin wani ƙaramin yaro kuma irin wannan halin dugunzuma na da wuyar sha'ani," ta faɗa tana ƙoƙarin share hawaye. Duk da haka, a gare ta, sabuwar dokar na iya zama wani juyin-juya-hali. "Za ta taimaka wa marasa lafiya kamar mu, wajen samun aikin dashe. Samun gudunmawar ƙoda, tamkar bai wa mutum wata damar rayuwa ce.







