Me gwamnatin Najeriya ke yi da kuɗaɗen tallafi da take cirewa?

Man fetur

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja

A jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar kama mulki, ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye "tallafin mai".

Shugaban ya ce matakin cire tallafin man fetur ɗin ya zama dole.

Mahukunta a ƙasar na kukan cewa tallafin man da gwamnati ke biya yana janye ɗumbin dukiyar da ya kamata a yi amfani da ita wajen samar da muhimman ababen more rayuwa.

Tun daga wannan furuci da ya yi aka shiga ruɗu, aka yi ta samun dogon layukan motoci a gidajen mai, kuɗin sufuri ya tashi, inda gidajen mai ɗin suka koma sayar da litar mai kan naira 700.

Bayan haka ne kuma, ƙungiyar kwadago a ƙasar ta tsunduma yajin aikin gargaɗi domin nuna adawa da matakin da gwamnatin ta ɗauka na cire tallafin.

Ƙungiyar ta ce babu abin da cire tallafin ya yi illa ƙarin wahalhalu ga ƴan Najeriya.

Ba ya ga tallafin man fetur, akwai kuma batun cire tallafin lantarki, inda tun a tsakiyar watan Fabrairu ne, ministan lantarki na Najeria, Adebayo Adelabu ya sanar da cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a kan wutar lantarki ba saboda tarin basukan da kamfanonin samar da lantarki ke bin gwamnati.

Sanarwar ta Adelabu ta janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta kasancewar ba a fita cikin kuncin da cire tallafin mai ya yi ba, sai ga na wutar lantarki.

'Cire tallafi ya sa ana biyan albashi yadda ya kamata'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnatin shugaba Bola Tinubu dai ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen tallafin da ta cire wajen yi wa ƴan ƙasar ayyukan more rayuwa kamar hanyoyi da sauransu.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Abdul'aziz Abdul'aziz ya faɗa wa BBC cewa ba wai gwamnati ta ware kuɗin ne tana ajiye su a wani asusu ba kamar yadda wasu ke bayyanawa.

"Kuɗin tallafi ba kuɗi ne na daban da aka ware su ba. Dalilin cire tallafi shi ne saboda an samu ƙarin kuɗin shiga wanda ya sa yanzu ana biyan albashi. Idan da ba a cire shi ba da jihohi ba za su samu damar biyan albashi ba," in ji shi.

Ya ce yanzu jihohi na samun damar biyan albashi yadda ya kamata saboda cire tallafi, ana kuma yin ayyuka duka a matakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Kakakin shugaban Najeriyar ya ce cikin abubuwan da ake yi bayan cire tallafi shi ne fara rabon kuɗaɗen taimako da na bashi da ya kai kusan naira biliyan 200.

"Akwai kuma manyan ayyuka na titi da jirgin ƙasa waɗanda ake yi sakamakon ƙarin kuɗaɗen. Duk gwamnoni da ke aiki a jihohinsu suna yi saboda samun ƙarin kuɗin cire tallafi," in ji shi.

Ya ce a baya ana yawan samun ƙorafi kan rashin biyan albashi a jihohi da kuma ƙananan hukumomi, amma yanzu babu duka wannan.

Abdul'aziz ya kuma musanta rahotanni da ke cewa gwamnati na biyan kuɗin tallafi fiye da a baya, inda ya ce da akwai haka da batun ba zai ɓuya ba.

"Ba za a ɗauki kuɗi kuma ana samun ƙarin kuɗin shiga, sannan a ce ana biyan tallafin mai ba," a cewar kakakin shugaban Najeriyar.

'Babu abin da cire tallafi ya yi illa dagula tattalin arzikin Najeriya'

Tun bayan cire tallafin mai da kuma na lantarki dai, masana harkar tattalin arziki a Najeriya ke ta bayyana ra'ayoyinsu kan batun.

Farfesa Kabiru Isa Dandago, Malami a Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce cire tallafin ya ƙara dagula tattalin arzikin Najeriya.

"Cire wannan tallafi ya sa farashin kayayyaki da ake amfani da su a yau da kullum ya ƙaru, kuma saukarsu zai yi matukar wahala. Waɗanda suka ƙara farashin su ma suna sayen kayayyaki da tsada ko ma a cikin gida ko a waje.

"Darajar abin da masu karɓar albashi ke karɓa ya narke gaba-ɗaya bayan janye tallafin mai. Abin da ya rage ba ya taimaka musu wajen ciyar da kansu, biyan kuɗin haya da kuma abubuwa da ke buƙatar kuɗi na kyautata rayuwarsu," in ji Farfesa Dandago.

Ya ce babu wani tasiri da cire tallafin ya yi na inganta rayuwar jama'a, sai ma daɗa jefa al'umma cikin tashin hankali.

Farfesan ya ce da ma tallafi abu ne da duk ƙasashe a faɗin duniya ke bayar da shi musamman a ɓangaren wutar lantarki, ruwa, ko aikin gona balle man fetur wanda a Najeriya shi ne jigon tattalin arzikin ƙasar, inda ya ce cire shi ya nuna ba a soa cike tazara da ke tsakanin waɗanda ke da abu da marasa shi.

'Ba shi da alfanu ko kaɗan'

Farfesa Kabiru Dandago ya ce cire tallafin da gwamnati ta yi ba shi da alfanu ko kaɗan musamman ma ga talaka.

"Duk abin da zai zo ya faɗaɗa tazara da ke tsakanin talakawa da masu hali ba shi da amfani ga al'umma.

"Duk ƙasashen da suka ci gaba ai da haka suke cike tazarar da ke tsakanin masu shi da marasa shi ta hanyar ba da tallafi, ko tallafi na ruwa, man fetur, amfanin gona da sauransu," in ji masanin.

Ya ce yayin da aka cire tallafi ana so ne kawai a jefa talakawa har ma masu kuɗi cikin wahala.

"Duk lokacin da aka ce talakawa ba sa barci suna cikin yunwa da fatara, su ma masu kuɗi ba za su iya barci ba," in ji shi.

Me ya kamata gwamnati ta yi?

Masanin kan harkar tattalin arziki ya ce ya kamata gwamnati ta dauki mataki na canza tsarinta na cire tallafin man fetur, a kuma ga darajar man fetur ya yi ƙasa daga 700 zuwa lita ɗaya kan naira 200 ko 300.

"Idan an yi haka farashin kayayyaki zai sauka," in ji shi.

Ya ce ya kamata gwamnati ta inganta tallafin aikin gona yanda za a samu yin noma yadda ya kamata, a kuma fito da taki da iri a farashi mai rahusa har ma da kayakin noma.

Ya ƙara da cewa in aka ba da tallafi sosai a ɓangaren aikin gona, manoman ƙasar za su iya yin noma har su fitar da amfani zuwa ƙasashen waje.

"Kuɗaɗen da ake kashe wa a ɓangaren tsaro ninƙi ne na kuɗaɗen da ya kamata a ce ana batar wa a kan harkar gona, ruwa, man fetur da kuma wutar lantarki.