Hanyoyi shida na kauce wa yin ɗari-ɗari da samun ƙwarin gwiwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alicia Hernández
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
“Ban san dalilin da ya sa har yanzu ba su kore ni ba. Za su ga ban dace da wannan aikin ba. Ina nan ne kawai saboda sa'a. Ni mayaudari ne.”
Wataƙila kun gaya wa kanku wani abu makamancin haka - sau da yawa ko kaɗan - a wani lokaci a rayuwar ku ta aiki.
Ba kai kaɗai ba ne: ƙila kana jin rashin kwarin gwiwa ko kuma ɗari-ɗari a cikin mutane, kuma tunanin haka ba sabon abu ba ne.
Dolors Liria wata likitar halayyar ɗan'Adam ta ce "Rashin kwarin gwiwa ko kuma ɗari-ɗari a cikin mutane shi ne wahalar da wasu mutane ke fama da ita wajen gane cancantarsu da kuma fargabar cewa ba za su iya bayar da abin da ake so ba ko kuma su yi tunanin su mayaudara ne.
Martínez Ricart, kwararriya a fannin sanin halayyar ɗan'Adam, ta ce wannan matsala tana faruwa ne a lokacin da “ainihin asalinka da ainihin abin da ka gano a cikin kai ba su daidaita ba, kuma kana jin cewa ba za ka yi wani kataɓus ba.
Wannan yana haifar da "yanayin rashin gane me za mu iya cimmawa, ko jin rashin cancantar cimma abin da muke da shi," in ji Isabel Aranda, wadda ke da digiri na uku a fannin ilimin halayyar ɗan'adam kuma mamba a ƙungiyar kwararru kan halayyar ɗan'adam a birnin Madrid.
Domin samun ramawa, mutanen da ke fama da wannan matsalar sukan yi aiki fiye da kima ko amfani da wasu hanyoyi waɗanda za su iya yin illa ga lafiyarsu, kamar cutar damuwa.
Masana halayyar ɗan'Adam Pauline Rose Clance da Suzanne Imes ne suka fara ba da suna ga wannan matsalar a 1978.
Ba cuta ba ce kuma ba yanayin tunani ba ne, amma ɗabi'a da aka koya tun yarinta don haka yana sauyawa, in ji masanan da muka tuntuɓa.

Asalin hoton, Getty Images
Kowane mutum zai iya fuskantar wannan matsala, sai dai ta fi yawa tsakanin mata.
Masana sun yi nuni da cewa rashin abin koyi da mata, da nunawa mata bambanci a wuraren aiki, da kuma tsarin ilimi, wurare da aka yi sa ran cewa mata ba za su taɓuka wani abu ba, na cikin abubuwan da ke janyo matsalar.
"MatsalarThe impostor syndrome" ya ce "Muna ƙoƙari sosai don nuna cewa za mu iya aikin, domin alamu sun nuna za mu fara daga farko maimakon daga matakin da muke kai na ainihi,"in ji Ricart wanda ya kiriro da wata cibiyar bayar da shawara.
Masana halayyar ɗan'adam ɗin guda uku sun ba da shawarar cewa idan muka ji ba za mu iya jurewa yanayin ba, ya kamata mu nemi taimakon kwararru. Suna ba mu shawarwari kan yadda za mu kawo ƙarshen wannan matsala ta rashin kwarin gwiwa kuma yadda za mu samu kwarin gwiwa.
1. Gano matsalar
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da duk wani batu na motsin rai shi ne cewa ba mu ɗauki lokaci don gano kanmu ba, don mu san abin da yake faruwa da mu kuma mu ɗauki lokaci don tunani game da shi.
Abin da muke gaya wa kanmu da kuma yadda muke yin hakan yana da mahimmanci: "Dole ne ku gane cewa ba ku daraja kanku ba, ba ku san yadda za ku ce 'da kyau' ba ko kuma ku taya kanku murna kuma ba ku ganin kun cancanci wannan nasarar,” in ji Aranda.
Ricart ya nanata cewa wannan murya mai mahimmanci, mai tsananin buƙatu da ke gaya mana "ba ku isa ba", ta bayyana a wani lokaci a rayuwarmu "a matsayin muryar da ta taimake mu don tsira a cikin muhallinmu". Wataƙila ya taimaka mana mu gyara a wasu wurare, amma muna buƙatar mayar da hankali idan hakan ya hana mu ci gaba.
"Ƙoƙarin neman tushen wannan zai iya taimaka mana mu fuskanci matsalar don ganin tana ta'azzara," in ji Dolors Liria.
2. Ka tunawa kanka irin nasarar da ka samu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan hangen nesa na iya taimaka mana lokacin da muke cikin tsananin damuwa. Zai iya taimakawa wajen kawar da waɗannan matsalolin da kuma kimanta kanmu daga mahanga mai kyau.
Dolors Liria ta bayar da shawarar yin bitar abin da ya faru da mu a wasu lokuta lokacin da irin waɗannan ƙalubale suka bayyana. "Wataƙila mun ji haka, amma yawan lokuta muna samun damar shawo kan lamarin."
Dolors Liria ta ba da shawarar yin bitar abin da ya faru da mu a wasu lokatai lokacin da irin waɗannan ƙalubale suka bayyana. "Wataƙila mun ji haka, amma yawancin lokaci mun sami damar shawo kan lamarin."
Kuna iya sake tunani idan kuka fara jin rashin kwarin gwiwa ko kuma kuna iya rubuta da hannu ko kuma a intanet irin dukkannasarorin da kuka samu.
"Wani nau'i ne na ci gaban mutum, tare da abubuwan da za ku yi da kanku," in ji Aranda.
Mar Ricart ya kira shi da "itacen nasara" kuma ya bayyana cewa yana da amfani ta yadda idan muka manta abubuwan da muka yi, za mu iya sake duba nasarorinmu waɗanda suka riga suka zama jigo gare mu.

Asalin hoton, Getty Images
3. Ka yi farin ciki da kowane irin nasara
"Da zarar ka samu damar kammala wani abu, ka zarce zuwa abu na gaba ba tare da ka bai wa kanka lokaci na yin farin ciki da hakan ba, ko jnjinawa ƙoƙarin da ka yi wajen samun nasarar," in ji Ricart.
Wannan shi ne dalilin da ya sa yana da mahimmanci a yi murna, ka more wa kowane nasara, babba ko karami, a cewar ƙwararren.
"Saboda a bayansa akwai ƙoƙari da kuka yi. Kuma dole ne ku ba wa kanku sarari don ɗanɗana shi, da kuma yin godiya. Idan ba haka ba, kamar bai taɓa kasancewa ba.
A wannan yanayin, "batu ne na nasara tare da gamsuwa da kai da kuma cewa, 'Na yi shi, na yi farin ciki sosai, na cancanci hakan'".
Ƙari ga haka, Ricart ta nanata muhimmancin yin aiki a kan cancanta, ko da kuwa aikinmu. "Ka jaddada cewa muna da ƙima ga gaskiyar kasancewa da wanzuwa. Dole ne ku tunatar da kanku cewa ku mutum ne mai cancanta, komai aikin da kuke yi."
4. Yadda mutane ke kallonka
Ɗaya daga cikin abubuwan da ke nuna wannan girman matsalar shi ne yadda kake kallon kanka da kuma yadda mutane suka ɗauke ka.
Shi ya sa zai iya zama abu mai kyau ka kalli kanka ta fuskar wasu wato yadda suka ɗauke ka," in ji Aranda.
Ba ya ga yin tambayoyi ga wasu mutane, Aranda ta ba da shawarar cewa a riƙa ajiye jerin abubuwa da wasu ke faɗa a kanka. "Ka rubuta lokacin da ake yabonka, kada ka manta da abin da mutane ke cewa game da aikinka."
Bugu da ƙari, idan akwai wata shakka a wurin aiki game da yadda kake yin ƙoƙari, Dolors Liria ya bayar da shawara mai sauƙi: nemi ji daga wajen mutane.
"Kada mu jira mutane su gaya mana yadda muke, idan kuna da shakku, maimakon jira, ku tambayi manajoji su ba ku bayani idan ba ku da tabbacin kuna aikin da kyau ko kuma idan kuna buƙatar wanda ya tabbatar da shi."

Asalin hoton, Getty Images
5. Ka rage tsammani
A kowane irin alaƙa akwai tsammani daga dukkan ɓangarori. Wannan ya kunshi alaƙa ta aiki: dukkan ɓangarori na tsammanin wani abu.
Amma idan aka zo ga batun rashin kwarin gwiwa, abin da kake tsammani ba shi kake sa rai a wajen aiki ba, illa abin da kake tsammani daga kanka.
Kuma ya kamata hakan ya daidaita.
"Me ake nufi idan aka ce ba za ka iya cike wani gurbi ko aiki ba? Ya ya kake kallon kanka? Wane mataki ka ajiye kanka?"
Aranda, kwararriyar a fannin halayyar ɗan'adam, ta bayar da shawarar cewa mu yi gwaji don gane ko mun kai wani matsayi, ko yin tsammani. Alal misali: ba daidai bane ka yi tsammanin cewa za ka iya gudun tsere na watanni huɗu bayan da yanzu kake fara yin horo.
Dangane da haka, ya rage wa mutumin ya ba mu sharuɗa kan abin da ake sa rai a aiki "domin rage tsammani da ake yi".
6. Kula da kanka
Wannan - ya danganci yadda muke jin kanmu - kula da kai, wadda masana suka ce yana da muhimmanci mu san abin da ke faruwa da mu, kuma mu koyi yadda za mu rage hakan.
Wasanni za su taimaka. "Wasannin motsa jiki suna da matukar muhimmanci ga jikinmu. Sai dai ba sai mun je wuraren motsa jiki ba, zai iya zama kowane irin abu da ya danganci tafiya daga nan zuwa can: tafiya ko kuma yin rawa," in ji Liria.
A karshe, muna yin wannan ne duka domin neman abin da zai taimake mu, abin da zai kwantar mana da hankali, in ji ta.
"Waɗanne abubuwa ne ke taimakawa wajen kwantar mana da abin da muke ji. Kuma, bayan haka, ka yi ƙoƙarin ganin abubuwa ta hanya daban. Zai iya zama wasanni, waka, rawa, magana ko kuma wani da ka yarda da shi."

Asalin hoton, Getty Images
Mu saka a cikin ranmu cewa akwai muhimmancin barin aiki da kuma mayar da hankali kan wasu abubuwa, kamar iyalai da abokai. "Samun mutane na kusa masu goyon baya na ƙara kwarin gwiwa."
Liria ta kuma ba da shawarar cewa a samu abubuwa masu saka farin ciki na yau da kullum. "Rayuwa tana da wuya, aiki na da matukar wahala, amma suna da daɗi, abubuwa ƙanana za su saka ka farin ciki a lokacin da kake cikin damuwa ko gajiya.
A lokaci guda, abu guda a nan shi ne barin muryar da ta tsaya mana kuma ta hana mu samun kwarin gwiwa ta tafi, saboda kwarin gwiwa ta zo mana, za mu iya aiki cikin nishaɗi da walwala, a cewar Mar Martínez Ricart.











