Ghana za ta sake naɗa Otto Addo a matsayin kocin Black Stars

Asalin hoton, Reuters
Ghana za ta sake naɗa Otto Addo a matsayin kocin Black Stars a karo na biyu.
Dan shekaru 48, zai bar kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus a karshen kakar wasa ta bana.
Addo ya taba rike mukamin kocin Ghana a shekara ta 2022, inda ya hada aikin da horas da matasan Dortmund.
Ya jagoranci Ghana ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a 2022 amma sai yayi murabus bayan an fitar da Black Stars a matakin rukuni a Qatar.
Hukumar kwallon Ghana - GFA ta rubuta a Facebook cewa za a bai wa Addo "kwangilar wata 34" da kuma damar karin shekara biyu.
"Ba karamin abu ba ne dana yanke shawara irin wannan. Ina godiya da mahukunta Borussia Dortmund da suka ɗauki wannan matakin," Addo ya bayyana a cikin wata wasika da aka wallafa a shafin intanet na Dortmund.







