Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Reus zai bar Borussia Dortmund
Dan kwallon Borussia Dortmund, Marco Reus zai bar kulob din a karshen kakar wasan bana idan kwangilarsa ta kare.
Dan Jamus din ya zura kwallo 168 a wasa 424 da ya buga wa kulob din tun bayan da ya bar Borussia Monchengladbach a shekara ta 2012.
Dan shekaru 34, ya shafe shekaru tara a kulob kuma yarjejeniyarsa za ta kare a watan Yuli.
"Na shafe fiye da rabin rayuwa ta a wannan kulob din kuma ina jin dadin haka a kullum," in ji Reus.
"Akwai matukar wuya in yi ban kwana da wannan kulob din."
Reus ya lashe kyautar DFB-Pokal sau biyu a tsawon lokacin da ya shafe yana murza leda a kulob din.
Yana cikin tawagar Dortmund da ta sha kashi a wasan karshe na gasar zakarun Turai tsakaninta da Bayern Munich a shekara ta 2013.