Zuwa na gasar Euro bai yi amfani ba - Mbappe

Kylian Mbappe

Asalin hoton, PA

Kyaftin ɗin tawagar Faransa Kylian Mbappe ya bayyana rashin jin daɗinsa kan gaza cimma burinsa na zama zakaran Turai bayan wasan daf da na ƙarshe a gasar EURO 2024 da Sifaniya ta doke su da ci 2-1.

An sa ran cewa Mbappe, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a 2018 zai jagoranci Faransa ta yi nasara a gasar da ake gudanarwa a Jamus, amma lamarin ya faskara inda wasu magoya bayan tawagar Faransa suka zarge shi da rashin ƙoƙari a gasar baki ɗaya.

Babu shakka raunin da Mbappe ya ji a wasan matakin rukuni na ƙarshe da suka kara da Austria ya yi matuƙar tasiri kan gasar Mbappe, wanda hakan ya tilasta masa amfani da takunkumi.

Mbappe ya fuskanci matsaloli da takunkumin, inda aka gan shi a lokuta da dama yana neman daidaita zaman takunkumin a fuskarsa.

Da aka tambaye shi ko raunin ya taimaka wurin rashin ƙokarinsa, Dan wasan mai shekara 25 cewa ya yi, 'Ai Komai ne'.

'Ba wani batu na tashin hankali ba ne, na yi ƙoƙari ko ban yi ba. Gaskiyar ita ce, ban yi ƙoƙari ba kuma za mu tafi gida. shi kenan.

Kocin tawagar Faransa Didier Deschamps ya amince a farkon gasar cewa Mbappe ya ɗan fuskanci ƙalubale da takunkumin amma bayan rashin nasarar da aka yi a daren ranar Talata ya ce laifin ba na wani ɗan wasa ɗaya ba ne.

Ya kara da cewa 'Ba zan ɗaurawa wani ɗan wasa alhakin da ya fi na wani ba.'

"Idan kuka kai matakin wasan kusa da na ƙarshe kuma kuka da tawaga mai kyau irin ta Sifaniya, dole ne ku kasance masu matuƙar ƙoƙari, kuma ba mu kasance hakan ba."

Yanzu dai bayan ya lashe kofin Ligue 1 sau bakwai a Faransa tare da Monaco da Paris St-Germain, Mbappe zai karkata akalarsa wurin neman lashe gasar Champions League a kakar wasa mai zuwa inda zai koma Real Madrid, ya kuma haɗe da zaratan ƴan wasa kamar su Jude Bellingham da Vinicius Jr da kuma Rodrygo.