Inter Milan na zawarcin Guehi, Everton ta sanya ido kan Jackson

Marc Guehi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Inter Milan na sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, idan kwantiraginsa da Crystal Palace ya ƙare a bazara mai zuwa, amma ta na fuskantar hamayya daga Barcelona da ​​Bayern Munich da Real Madrid da kuma Liverpool. (Gazzetta dello Sport)

Everton na sa ido kan ɗan wasan gaba na Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, yayin da Bayern Munich ke jan ƙafa wurin biyan fam miliyan 70 don siyan ɗan wasan gaban na Chelsea. (Football Insider).

Manchester United na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Chelsea ɗan ƙasar Brazil Andrey Santos, mai shekara 21, a ƙoƙarinta na ƙarfafa ɓangaren ƴanwasan tsakiyarta a watan Janairu. (Football Insider).

Kocin Manchester United Ruben Amorim na sa ran wasu daga cikin ƴan wasansa na za su nemi barin ƙungiyar a watan Janairu. (Times)

Manchester United na nazarin ɗaukar ɗan wasan Lille ɗan ƙasar Faransa Ayyoub Bouaddi, mai shekara 18. (Caught Offside).

Arsenal da Liverpool su ma suna zawarcin matashin mai hazaƙa, Bouaddi. (TBR Football)

Ɗan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, ya ce ya na sane da hasashen da ake yi kan makomarsa, amma ya yi farin ciki da ya ci gaba da zama tare da Cherries a bazarar da ta gabata. (Sky Sports)

Ismael Saibari na PSV Eindhoven na jan hankalin ƙungiyoyi da dama na gasar Premier, inda aka samu labarin cewa Aston Villa da Leeds na cikin waɗanda ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Morocco mai shekara 24. (TBR Football)

Real Madrid ta bi sahun Manchester United da Chelsea wajen zawarcin ɗan wasan Red Bull Salzburg ɗan ƙasar Bosnia-Herzegovina Kerim Alajbegovic, mai shekara 18. (Defensa Central).