Wace illa amfani da na'urorin sadarwar zamani ke yi wa ƙananan yara?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Idris
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Duba da yadda wasu iyaye a yanzu suke barin yaransu suna ɗaukar tsawon lokaci suna amfani da na'urorin sadarwar zamani ta hanyar kallon shirye-shirye ko fina-finai ko gyam da makamantansu a talbijin ko wayar hannu ko kamfuta tun suna jarirai.
Mafi yawan yaran kan taso da shakuwar waɗannan abubuwa tare da yawan kasancewa tare da su ta yanda mafi yawan lokuta suke yi wa kansu illa.
Akan samu wasu yaran ma da in shaƙuwar ta yi tsanani sai a ga cikin baccinsu suna kwatanta kamar suna amfani da su.
Wasu yaran kuma ko makaranta suka fara zuwa hankalinsu gaba ɗaya na gida, ba sa iya mai da hankali kan me ake koyarwa a makarantar, balle su koyi darussan da ake koya musu, kawai ko da yaushe suna cikin zaƙuwa a tashi su koma gida su ɗora daga inda suka tsaya wala'alla kallo ne ko kuma wani gyam.
Mafi yawan lokuta na'urorin (talbijin/waya da sauransu) kan ɗaukewa yara hankali daga abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ace sun koya a shekarun da suke, tare da cinye musu lokaci.
Wani sa'ilin ma akan yi rashin sa'a wannan dabi'a ta taba lafiyar yara ko kuma basirarsu.
- Shin wace illa yawan kallon talbijin ko wayar salula ko kamputa na hannu ke da shi ga yara?
- Kuma ta waɗanne hanyoyi za a iya taƙaitawa yaran yawan amfani da su?
- Sannan waɗanne ayyuka ne zasu iya maye gurbin na'urorin a rayuwar yara?
Domin samun amsoshin tambayoyin ne BBC ta tattauna da Dakta Asma’u Garko, likitar ƙwaƙwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano da Nusaibah ƙofar-Naisa, wata uwa da yaranta ke makaranta tare da ita a gida da kuma Khaulat Zubair Jibril, malamar yara inda suka mana ƙarin haske kan batun.
A cewar Dakta Asma'u, wani bincike ya nuna cewa duk yaron da aka saba wa amfani da waya ko talbijin da makamantansu zai iya kamuwa da lalurar sabo da su, abin da bature ke cewa ''addictive behavior''.
Wasu lokuta in iyaye na son yaro kar ya dame su in suna wani abu, ko yana koke-koke sai kawai su ba shi waya ko ace a kunna masa talabijin yayi kallo.
A tunanin iyayen sun yi wa yaron wayo amma kuma ƙwaƙwalwarsa kullum tana sabawa da wannan lokacin da ya ke yi da waɗannan na'urori.
To a hankali akwai wani abu da ake kira dopamine, kamar sinadarai ne da ƙwaƙwalwa take saki duk lokacin da ta ji daɗi, to duk lokacin da aka ba wa yaro waya ko aka kunna masa talbijin sai yaji daɗi sosai dalilin haka, wani lokacin wannan dopamine ɗin na ɓaɓɓakowa fiye da yadda ake tunani.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta haka ne kuma sai sauran abubuwa da a baya suke sa yaron nishadi har dopamine din ya ɓaɓɓako misali in ya ga wanda yake so ko ya ga abinci da ke masa daɗi, to sai ya zamana sun daina ba shi nishaɗin.
Tunda wannan sabon da yayi da kallon ya ɗauke masa hankalinsa ta yadda tunanin yaron da zaɓinsa da komai nasa ya ta'allaƙa kan lokacin misali wannan kallon kaɗai.
Dakta Asma'u ta kuma bayyana cewa waɗannan na'urori kan iya zama mai amfani wajen karawa yara kokari ta bangaren exposure wato wayewa da wasu abubuwa da dama amma kuma illar da ke tattare da su tafi yawa. Daga cikin illolin akwai;
- Rashin mayar da hankali kan karatu
- Rashin nutsuwar yin abubuwa da suka kamata a lokacinsu.
- Matsalar bacci
- Buɗewa yara ido ga wasu ɗabi'u ko halaye marasa kyau da kuma abubuwan da basu dace da hankalin yaran ko tunaninsu ba.
Likitar ta bawa iyaye shawarar cewa ya kamata su gane abu me amfani da kuma mara amfani tunda waɗannan abubuwa wato waya ko talbijin da makamantansu zamani ne ya kawo, amma kuma shi kanshi wanda ya kirkire su yana cewa a taƙaita lokacin da yara zasu yi amfani da su.
Kowanne abu a bashi lokacinsa. Wato ya zamana akwai lokacin bacci da lokacin wasa da lokacin makaranta da lokacin zaman hira da iyaye da sauransu. Ya zamana dai yaron ya san cewa komai akwai lokacin sa ba wai ko yaushe yaro yana kan talbijin ko waya ba.

Asalin hoton, Getty Images
Mun kuma tattauna da wata mahaifiya mai suna Nusaiba Ƙofar Na’isa wadda ta shahara a shafin sada zumunta na instagram, inda take nuna yadda take bai wa yaranta ilimi a gida, ba tare da zuwa makaranta ba.
A cewarta duk abin da mutum ya fi ba wa lokaci, shi ne zai yi tasiri a ɗabi’unsa, haka ma lamarin yake a wajen yara.
Idan yaro yana kewaye da rukunin wasu mutane ko yaushe, to waɗannan mutanen ne za su yi tasiri a kan abin da zai zama a rayuwa.
Ta ce “haka ma a ganina abin yake ga lokacin da ake kwashewa a gaban kwamfuta ko talbijin. Wasu yaran kan shafe tsawon sa’o’i ko awanni kullum a gaban talbijin inda ƙwaƙwalwarsu take jajiɓo wasu saƙonni ba tare ma da sun sani ba.
Ta cigaba da cewa fina-finan da suke kallo nawa ne ke nuna rikice-rikice da koyar da fitsara da hamayya tsakanin ƴan’uwa da tsokane-tsokane? Jajiɓo irin waɗannan abubuwa a kullum na da tasiri a tunaninsu, kuma suna shafar ɗabi’un yara.
Yara za su iya koyon abubuwa masu yawa ta hanyar amfani da lokutansu a kan wasu abubuwa daban waɗanda ba kallon talbijin ba, da aka tsara musamman don saita ɗabi’un yaro.
Abubuwan da yara zasu iya yi daban da yawan kallonsu talbijin ko waya ko gyam ɗin bidiyo
Malama Nusaibah ta shawarci a dinga barin yara suna yawan fita farfajiyar gida suna wasanni saboda hakan na da kyau wajen bunƙasa kaifin ƙwaƙwalwarsu.
Ta kuma ba da shawarar a riƙa ƙarfafa musu gwiwar;
- karanta litattafai
- Wasannin ɗaurin gwarmai
- Wasannin gargajiya na yara kamar langa da ƴar ɓuya
- Zane
- Ƙere-ƙeren hannu
- Zaman hira tsawon lokaci tare da iyaye
- A dinga barin yara suna samun kansu cikin gundura. Gundura tana bijiro da dabarun neman mafita da ƙirƙira. In ji ta, bai kamata komai na rayuwarsu ya kasance tsararre ba.
Ta ƙara da cewa "Babbar shawarar da zan bai wa iyaye shi ne su kasance masu manufa game da kowanne al’amari na tarbiyyar yaransu. Kuma kada su ji tsoron yin abin da ya sha bamban da saura.
Iyaye su yi tsokaci a rayuwar gaba lokacin da yaransu za su girma su zama cikakkun mutane. Su yi tunani, shin waɗanne irin mutane suke burin ganin ƴaƴansu sun zama?
Waɗanne irin halaye suke son gani a tare da su? Waɗanne irin wakilan jama’a suke son ganin sun zama?
Su amsa waɗannan tambayoyi cikin gaskiya da abokan zamansu, sai su waiwaya su gani, shin me suke buƙatar yi a yanzu don samar da irin wannan mutum a nan gaba.
Su fara daga yanzu, su tsarkake niyya, su yi ƙoƙari bakin iyawarsu, sauran al’amari kuma su bari a hannun Allah."

Asalin hoton, Getty Images
Muhimmanci koya wa yara ayyukan hannu tun ƙuriciya
BBC ta kuma tattaunawa da malamar yara ta makaranta, Khaulat Zubair Jibril inda ta bayyana muhimmancin koyon ayyukan hannu daka iya zame musu sana’a a rayuwarsu ta gaba maimakon yawan kashe lokaci akan waya ko talbijin.
Acewar Malama Khaulat za’a iya koyawa yara ayyukan da zasu iya ɗauke hankalinsu daga bata lokutansu kan talbijin ko waya ko gyam din bidiyo da makamantansu, ko da yake hakan ya danganta da abinda yaro ya nuna yana son koya ko aka fahimci yana da fiƙirar yi misali yaron da ke kwakkwance abubuwa a gida irin rediyo haka , sai a nuna masa hanyar da zai kwance ya kuma maida ba wai a dake shi ba ko a hantare shi kan wannan abun da yayi.
Wasu daga cikin ayyukan sun haɗa da;
- Saƙa
- Ɗinkin kayan sawa
- Ɗinkin takalmi da jaka
- Haɗa abun hannu ko saƙa da duwatsu
- Aikin kafinta
- Gyaran na'urori irinsu waya ko mota da makamantansu
- Girki
- Rini
Ta cigaba da cewa wasu yaran tun kan su gama sakandire ma sun iya wani daga cikin waɗannan abubuwan, wasu ma tun suna firamare iyayensu ke sa su koya suna cake kudadensu ma.
Ta kuma bayyana cewa yanzu makarantu sun farga inda suke koyawa yara abubuwan hannu inda kafin su gama sakandare ma sun koyi wani abu.
A ƙarshe tayi ƙarin haske kan yadda ake kukan babu aikin yi yaro ya gama jami’a ya na zaune a gida, inda da ace ya iya wani abu, zai samu hanyar samun na kashewa yayin da yake jiran aikin gwamnati, in kuma aikin ya samu zai iya cigaba da sana’arsa tare da aikin gwamnatin.










